Trending Hausa Novels

Sanadin Caca Book 1 Complete Hausa Novels By Sadi Sakhna

Reading file: SANADIN CACA.txt

Chapter 32 of 40

Da yamma kuwa kaman yanda shugaban makarantar yafaɗa,ya aikomin kayana uniform da kuma jaka ɗauke da litattafai,na rubutu da kuma na karatu,harda ƙur'ani izu sittin aciki..
Nikamma dan daÉ—i narasa bakin magana,ko Æ´aÆ´an gata albarka,babu abinda yarage sai karatu kawai..

__***__

"Deejah ki É—auki ruwannan kiyi wanka kizo ki tafi makaranta,kinsan fah abinda yayanku ya faÉ—a"
"Bazan jeba,nace bazanje É—in ba,ki faÉ—amasa idan yazo yaga banje ba ya kasheni nace ya kasheni,littafinma......"
Bata ƙarisa maganar ba ta rabashi gidan biyu fiyattt.
Kallonta ammi take da takaici,komai yasa Musbahu yakeson bata kuÉ—insa akan wannan halittar oho,a zatonsa wai hankali zatayi irin na sauran mutane idan ya kaita makaranta?
"Deejah kika yaga littafin makarantar?"
"Ehh É—in na yaga kuma......."
Bata ƙarisa maganar ba sukayi ido huɗu da Musbahu,wanda yake tsaye a bakin shiga ƙofar tasu,ya saƙala hannunsa a kirjinsa yana kallonta,fuskarsa cikeda bacin rai.
"Ya mukayi dake,me kika cemin jiyah"
"Ehh ni cewa nace zanje makarantar inna je kuma zanyi karatu,idan na ƙiyi a dakani"
"To me yasa daga zuwanki É—aya jiya kikace bazaki sake zuwa,wato irin duk abinda zanyi nayi harda yaga littafin koh,ana kije kiyi wanka kina cewa bazakiyi ba"
"Ahah ni bance baxanyi wanka ba,sannann kuma littafin bani na yagaba fatalwar tunkiyar rammah ce"
"Ohh bayan kin soke tunkiyar ma kaman wata raƙuma bai isheki ba saikin bita kinyi mata sharri,ki dai faɗi gaskiya abinda yahanaki komawa makarantar,kin fasawa malami goshi ai dole kice bazaki jeba"
"Ke rammah dagaske ta rotse kan malami,a ina kikaji?"
Ammi ta tambaya tana riƙe haba.
Wata harara Deejah ta watsawa rammah tareda cewa.
"Nasan wadda ta faÉ—amiki,wato duk da gargaÉ—in danayi mata bataji ba koh,hmmmm"
Bulala Musbahu ya zara zaiyi kan Deejah,amma kururuwar da uwaisu yakeyi ta tsayar dashi.
Daga É—akinsa yafito yana kururuwa,banda ambaton kuÉ—insa babu abinda yakeyi.
Kowa tsayawa yayi yana kallonsa a wajen.
"KuÉ—ina wanene ya É—ebemin kuÉ—ina,wayyo shikenan kun lahantani wane shegenne ya bankaÉ—emin ajiya yamin sata waye?"
HaÉ—a ido sukayi da Deejah wacce take tsaye a bakin banÉ—aki,saboda gudun da tayi daga wajen Musbahu.
Gwaliyo tayiwa uwaisu tareda kashe ido,aikuwa nan ya gane mai take nufi.
"Zo shegiyar yarinya zo nan, tunda kika kasheni ai sai ki bar gidannan,ki faÉ—amin inda kika kaimin kuÉ—ina"
Kowa yanxu kallo wajen Deejah ya koma,wacce take kallon mutanen wajen idonta a tsatstsaye kaman nono maza..
"Niba kuÉ—i na É—auka ba takardu na É—auka,jiya fah aka tambayeka a gida za'ayi abinci kace bakada kuÉ—i,to ni taya zanga kuÉ—i a É—akinka bayan kace bakada kuÉ—i,takardu na É—auka,kuma nayi makamashi dasu"
TafaÉ—a hankalinta kwance kaman batasan mai ta aikata ba,bayan kuma tana sane rashin mutuncine kawai. Dan yanzu ta daina wannan gurnanin,tsiya take shukawa a gidan cikin hankalinta.
Kama ƙirjin uwaisu yayi numfashinsa yana yin sama sama,kafin Musbahu ya tafi da sauri ya taroshi har yakai ƙasa..
Ihu da kururuwa mutane gidan suka saka,aka nufi asibiti dashi.
Banda Deejah waccce ta shiga wanka zata tafi makarantar da tace bazata ba.
Ammi ce ta kalleta wacce tazo É—aukar mayafi zasu tafi asibitin.
"Amma wannan yarinyar bakya cikin mutane inaga,yanzu kiga abinda kika aikata masa amma bai dameki ba?."
"Ahh to ubana ne dazan damu,kuke wani kukan munafurci naga kuma ba damuwar kukayi dashi ba,shima kuma ba damuwa daku yayi ba,yanada kuÉ—in jiya ya kawo ayi tuwo yace wani bashida kuÉ—i,kuma yanzu yafito yana faÉ—uwa wai an É—auke masa kuÉ—i,harda za'aji haushina ma ai na banza ne,kuÉ—i suna amsa sunansu kuÉ—i idan za'a kashe ,inku aka ajiyesu da bunu ne.
Nina tafi makaranta naga yanda zamu ƙare da wancan shima wani uwaisun hmmm,aishima in bai kiyayeni ba saina figewa wannan ƴar tasa mai suffar agwagi ƙafafu"
Surutun take tana tafiyha harta bar gidan,ita kuma ammi ta tari acaba zuwa asibitin.
Lokacin da ammi ta isa asibitin har an saka masa ruwa yana kwance,yayi shuru da alama bacci yakeyi.
Musbahu ne a jingine a jikin bangon É—akin,sai rammah a gefensa a zaune,magana yafarayi kaman zautacce..
"Kuɗina kuɗina dana tara,da ƙonamin kuɗina mai kuma ya sauramin tunda na kuɗina"
"Baban ubadu dan Allah kabar zancennan,wai yau kafara rasa kuÉ—inka ne,naga kusan ko yaushe kaje caca sai ka rasa kuÉ—innaka,har Æ´ar ka ka rasa abin bai dameka ba,amma yanzu akan kuÉ—i kana ta tadawa mutane hankali"
Ammi ce tafaÉ—a cikeda takaici,dan itama kaman Deejah abinda kuma yafara bata haushi..
"Dallah rufemin baki,kinsan kuwa kuÉ—innan na menene,duk sanda nayi caca tayi kyau zuwa nake na tara su,hatta kuÉ—in gonata ma ta hayi tana siyar suna ciki,kuÉ—innan su nake gani nakejin daÉ—i,saboda yanda sukeda muhimmanci a wajena,kuÉ—in sadakin Sumaimah ma suna ciki,harda kuÉ—aÉ—enku da in ansiyar dabbobi nake cewa sun faÉ—i......"
"Kambuuuu kace har kuÉ—in tunkiyata ma data kasa narasa su suna wajenka kenan"
"Ke dallah dana É—auka ma ai ba cinyewa nayi ba ajiyewa nayi,bare kice nayi miki sata"
FaÉ—a ne ya kaure tsakanin uwaisu da matannasa,kowa tana faÉ—in albarkacin bakinsa..
Musbahu bayan ya kallesu na É—an lokaci É—auke idonsa yayi yana jijjiga kai,shikamma inaga barin gidannan zayyi yayi nesa dashi kozai hutah,ace kullum sai wani abu ya bullo a gidan. A irin wannan rigimar tasa yake ya É—akko wata hatsabibiyar yarinya,tausayin halinda take ciki da kuma ganin nauyinta yana kan ubansa shiyasa ya fara kulada lamuranta,domin ko kaÉ—an bayaso a kuma yarinya wacce zata maimaita rayuwa irin ta Sumaimah a gidan,amma kash ba'a ma farashi ba wata ta bullo. Dan da alama kuÉ—aÉ—ensu da abubuwansu da uwaisu ya É—ebe ya ajiye na tsawon lokaci sun faÉ—a,wanda hakan yana shirin mayar da shi suru suru.
Juyar da kansa yayi bakin ƙofah suka haɗa ido da Sumaimah,sanye take da kayan uniform na Albayan,yaushe tashiga makaranta..
Hijabinta ya kusa zuwa ƙasa,da sandal da safa a ƙafarta,sai babbar jakar makarantar data rataya,tayi fari tai kyau kaman ba itah ba..
Shuru kakejin su rammah sunyi,dan suma a tare sukaga Sumaimah tashigo É—in,babu wanda zai kalleta yace Itace yarinyar da aka kai gidan miji watanni uku da suka wuce.
Tayi kyau haskenta yasake fitowa,tunda ta tafi kowa ya manta da babinta saboda sabon abinda ya kunno musu kai.
A hankali take tafiyah harta isa inda uwaisun yake kwance.
"Baba mai yafaru haka,yanzunnan nadawo daga makaranta na shiga ta gida,anan suke cewa wai kuna asibiti"
Tausayinta ne yakama Musbahu,inaga bazayyi ƙarya ba idan yace kaff cikin ƴaƴan gidan babu wanda yakaita tausayin ubannasu,koda yake ita matsayinsa take bashi cikeda ilimi da kuma sanin darajarsa a wajenta,sabanin sauran yaran gidan da suke masa kallon ba komai ba,irin yanda iyayensu suka nuna musu. Ƙasa yayi dakai yarasa ma mai zai ce mata,da alama kunyarta ne yakamashi.
"Uhm uhm bakomai Sumaimah,yakk a gidan naki dai?"
ÆŠan murmushi tayi tareda cewa.
"Bakomai baba muna zaune lafiyah,yanda ake zatonsa ma ashe ba haka yakeba,kalli fah yasakani a makaranta,shine ya kaini makaranta ma yau dazai bi ta wajen,inna ma ta É—aukeni tamkar Æ´ar ta"
"Ahh to to abu yayi kyau Allah ya taimaka,kinga tashi maza ki tafi gidanki,inyaso wani lokacin sai kizo gidan koh"
"Amma baba mai yasameka aka kawoka asibiti"
"Ke fah dama kin faye magana,to tunda so koke kiji waccar hatsabibiyar yarijyar ce ta ƙonamin kuɗaɗena,kai wannan ƴa na rasa yanda zanyi da itah,ace ƴaƴan ka basu takura maka ba sai can wata bare?"
Sumaimah bata tambayi wa yake nufi ba,saboda tagano da Deejah yake.kuÉ—i ta ciro kaman dubu Biyar ta ajiye masa a gabansa.
"Gashi baba toh ka riƙe wannan,yace nayi siyayya ne to banyi ba saboda naji kuna asibiti,sai a siyamaka abinda zai gina jiki. Ammi da inna rammah ni barina wuce toh saina sake zuwa"
Babu kunya tunkafin ta gama bayanin uwaisu yasaka hannun ya fizge kuÉ—in tareda sakawa a cikin rigarsa,babu zancen siyan wani abu kenan.
Ammi ce kawai tayi mata a sauƙa lafiyah,rammah kam ɗauke kanta ma tayi.Fuskarta ƙarara bata boye baƙincikin da take ciki.
Tashi tayi zata tafi,a nan ta kulada Musbahu wanda yake tsaye,gabaÉ—aya ma inaga bata ganshi ba É—azu.
"Lahh yah Musbahu banganka ba,barka da rana ya mai jiki?"
"Yawwa sannu Sumaimah,akwai maganar danake so muyi dake,in lokacin yazo zan sanar dake,wata alfarma nakeso kiyimin kinji?"
"To shikenan yaya karka damu Allah ya kaimu lokacin"
Cikin farinciki da murna tabar asibitin zuwa gidanta,dukkan su kowa sai binta da kallon mamaki yakeyi,kaman ba ita. Wasu sunyi farincikin sauyawarta,wasu kuma babu yabo ba fallasa,yayinda wasu kuma zuciyarsu take tafarfasa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.