Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 1 of 25

πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
🏀🏀🏀 πŸ‘‘

By Ummy Abduol

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Da Sunan Allah mai rahama maijin kai

TSOKACI
Ina rokon Allah yasa yanda nafara littafin nan nagama Lapia Allahumma Ameen....
Banyi littafin nan Dan cin zarafin wani ko wata Bah. Nayi neh Dan nishadi dakuma fadakarwa...ngd..

Page1⃣

*MASARAUTAR GOMBE*

Motoci neh wajan guda biyar suka shigo cikin Airport din dai dai inda jirgin ya sauka sukai parking, fadawa neh suka dinga fitowa daga motocin, biyu daga cikinsu suka shimfida wani hadadden red carpet a daidai step din jirgin, niko ummy na gyara tsayuwa dan naga wanene zai sauko daga jirgin yanda naga fadawan sai Rawar jiki suke. Andau mintina kamar sha biyar Sannan wani hadadden saurayi fari tas ya leko tareda yatsine fuska, Ahankali ya soma saukowa daga step din jirgin, motar dake tsakiya wani bafade ya bude, wani dan dattijo ya fito cikin kayan sarauta, Tsantsar kamar da suke da saurayin neh yasa na tabbatar da mahaifinshi neh..
Dan Murmushi saurayin yayi daidai sanda ya iso inda mahaifinshi yake tsaye, dasauri ya qarasa tareda rungumeshi, cikeda kasaita mai martaba ya dan bubuga bayanshi tareda cewa "barka da dawowa my son", dan murmushi yayi sannan yace "Am vry happy to see uh dad" murmushi mai Martaba yayi aka bude musu kofar motan suka shiga..

Basu tsaya koina bah sai katafaren gidan sarauta, horn motar farko tai aka wangale gate din Gidan, dagudu motocin suka shiga cikin gidan zuwa inda yakamata su tsaya, tsakar gidan bayi neh burjik kowanne yana aikinda aka sashi, Sanin dawowan Yarima Fardeen dakuma halinsa yasa duk ma'aikatan suka aje aikinsu don zuwa kwasan gaisuwa, mai martaba da yarima na fitowa sukai cikin gidan, tareda rakiyan fadawan dake take musu baya, ganin haka yasa kowa yakoma bakin aikinshi....

Kishingide suka samu fulani a babban falonta wata baiwa tana mata tausa, da sallama mai martaba ya shigo hannunshi cikin na danshi, baiwar na ganin sun shigo ta rusuna ta gaidasu sannan tabar wajan dasauri, mikewa zaune fulani tai tana murmushi tana kallan dan nata, cikin sanyanyan murya tace "barka da zuwa dana" murmushi kwance akan fuskarshi yace "lapia lau mum nasameku lapia?" fulani daketa kallan dan nata cikeda farin ciki tace "lapia lau, ya Karatu ina fata ansamu abinda akaje nema" kai ya gyada, mikewa mai martaba yayi tareda cewa " umm ni kunga tafiyata tunda ni ba'a gani bah, mutane na jirana" dan dariya fardeen da fulani sukai ya fice daga falon yana cewa " nima lokacina na nan zuwa", mikewa fulani tai tace "zakaci abincine Yanzu ko sai kayi wanka??" Dan jim yayi sannan Yace "bari nai wankan tukun", side dinshi ya nufa, ko ina a gyare tsaf ya shiga bedroom ya chanza zuwa towel sannan ya fada toilet...

*MASARAUTAR ZARIA*

Zaune take kan wani hadaden carpet bayi zagaye da ita ko wacce qoqari take dan taga ta farantawa uwar gijiyarta rai, wata da kayan itatuwa a gabanta tana barewa, wata kuma farce take gyara mata, wata kuma gashin kanta take taje mata tareda sa sinadarai masu sa gashi laushi da kanshi akai, wacce take kusada ita koh labarai take bata na ban dariya ita kuwa sai dariya take gwanin ban sha'awa, suna cikin nishadinsu jakadiya ta iso wajan dasauri tareda rusunawa Sannan tace " Allah ya taimakeki, uwar gijiyata nasan ganinki" bata rai tai Sannan ta kalli jakadiyan cikin bacin Rai tace "jakadiya mai yasa koda yaushe kikesan batamin rai??" na fada miki ki daina durkusa min kinqi, banaso naga babba kamarki ko wanda bai kaiki tsufaba yana durkusa min, cikeda ladabi tace "Tuba nake ranki shi dade insha Allah daga yanzu na daina" Mikewa tai Altine baiwarta itama ta miqe, jakadiya na gaba tana biye da ita har side din mahaifiyar nata...

A bakin kofa jakadiya ta tsaya ita da Altine suka karasa, da Sallama suka shiga dakin zaune suka sameta hannunta riqe ta Apple tanaci, dasauri Altine ta tsugunna tareda kwasan gaisuwa, Apple dinda ke hannunta ta aje sannan ta amsa gaisuwan tace "Altine dan bamu guri", dasauri tabar dakin, ta Kalli yar nata Tace " Parveen dama bah wani abu baneh, Aisha ce ta kirani ta roqi Alfarman Tanaso kije kiyi mata hutu koda na sati daya neh" shiru Parveen tai kanta na Qasa, Ummanta ta kalleta Sannan Tace " banji Amsarki bah??" dan dagowa tai Tace " umma ban ganeh wa kike nufi bah??" umma tadanyi Murmushi Tace "Aminiyata Aisha Matar sarkin Gombe" Damm! Gaban Parveen ya fadi idonta cikeda kwalla tace "Umma kinfa san halin Yarima nidai Banaso naje"...

Haquri Umma ta soma bata dakyar ta shawo kanta ta amince badan Ranta yaso bah. Da daddare mai martaba Ya kirata dan Tambayanta Shawaranda ta yanke, Batareda bata lokaci bah Ta amsa mai, cikeda murna yace "ki shirya Gobe in Allah ya kaimu sai mu tafi nida kaina zan kaiki dan inaso dama nakai ziyara masarautar gombe"..

Tho fah! Ya zaman Parveen zai kasance da Fardeen?? Sai kun biyoni dan jin yanda zata kaya..

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
A WANI MASARAUTA
🏀🏀🏀 πŸ‘‘

By Ummy Abduol

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.