Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 17 of 25

Page1⃣7⃣

Kamar dazu amarya mota daya suka Koma Gida da fulani. Shiko Gogan Motrda Ta daukoshi ita ta Maidashi Gida...
Washe Gari da Safe Mutanen Zaria Yan Rakiyan Amarya Suka Fara Shiri, Parveen na Ganin Deeza zata tafi ta Fara Wani Sabon Kukan. Bah Irin Lallashinda Ba'ai mata bah Anma ta Tubure, Hakanan duk mutanen Suka Tafi Suka Barta Ita Kadai Kwal a Cikin Gidan Kamar Mayya...

Mai Martaba neh Zaune Da Fulani a Gefenshi Sai Yarima dake Kan Carpet kanshi a Kasa. Mai martaba ya Kalleshi Sannan Ya Fara Dacewa
"Yarima Yanzu Ka Zama Babban Mutum, Duk darajan da Akeba Mutum baikai idan Yayi aureba. Ina Maka Nasiha Akan ka Kula da Matarda, Kamar Yanda Kasani Yanzu Ci da Sha, Tufatarwa Da Wajan Kwanciya da Sauransu duk Yana Wiyanka. Banaso Naji daidai da Rana daya ka sabama yarinyan nan, Ku Zauna lapia Allah ya muku Albarka"
Yarima Da Fulani Suka Amsa da "Ameen"
"Insha Allahu zanyi Kokarin Kiyayewa"
Fulani Tai Murmushi
"Ni Kuma Maganan dazanyi, Kaga Yanzu Kai Aure. Maganan Shashancinka daka Saba Babu Shi Yanzu, Banda Fita Yawon Dare Dan Allah Yarima. Kaga Dai Ita Kadaice A Gidan Kuma bah dadi mutum Ya zauna shi kadai a Gida"
Hade Rai Yayi kanshi na Qasa
"Tho Fulani Zan kiyaye"
Ta Qara Murmushi Tace
"Allah ya maka Albarka"
Ameen Yace Ya mike Yabar Falon...

Side Dinshi ya nufa, Direct Bedroom Ya Wuce, Dakin Yagani Wayam bah Kaya Sai Funitures din dakin kawai. Qarasawa Yayi ya bude walldrop Yaga Wayan, ranshi ne Ya baci Ya Nufi Side din mai martaba. A Hanya Yaci karo da Fulani tana qoqarin Zuwa nata bangaren, Ta kalleshi da Mamaki
"Ina zuwa??"
"Fulani ina aka kaimin Kayana?? Na Duba basa Side dina"
Hararanshi Tai Cikin Sigan Wasa
"Ina Kuwa Za'a Kai maka in bah Sabon Side Dinka Bah"
Bata Rai Yayi Baice Komai Bah ya juya Zaibar Wajan, Fulani Ta kira Sunanshi. Juyawa Yayi ya Kalleta Tace
"Ina Kuma Zaka??koh ka manta Amarya Nachan Tana jiranka neh"
Ranshi Bace Ya Juya ya nufi Gidan Amarya...

Parveen Taci Kuka Ta Qoshi, Ganin Kukan bazai Pisheta bah Yasa Ta mike Ta Shiga Toilet, Wanka Tai Ta Dauro Alwala ta Gabatar da Sallan Magriba da Isha Sannan Ta Sauya Kayanta Zuwa na Barci Ta Kwanta. Barci ne Yayi Qaura a idonta, Tunani ta Soma Yi Kala kala, Yanzu ya zamansu Zai Kasance Da Yarima?? Tsaki Taja A Fili Tace
"Saidai Wallahi Mu Goga, Bazan Zauna Ka Raina min Hankali Bah"
Murmushi Tai Ta Gyara Kwanciya A Hankali Barci mai nauyi ya dauketa Cikeda Mafarkai Kala Kala...

Koda Yarima Ya Shigo Side din Parveen Ta Dade dayin Barci. Dakuna Yagani Guda Biyu, Shiru Yayi Yana Tunani, Chan Ya bude na Hannun Damanshi Ya Shiga, Hadadden dakine, Wanda Yafi Wanda ya Baro, komai Akwai a Dakin, A Hankali ya Qarasa Ciki, Turarukanshi Da Lotions dinshi Ya hango Kan Mirrow Din Dakin. Riqe Kugu Yayi
"So Nan Fulani Tasa a Kawomin Kayana, Umm Not Bad!"
Toilet Ya nufa Ya Watsa Ruwa Ya Fito Daure da Towel, Wayanshi Ya dauka Ya Soma neman Wani Layi, Yana Fara Ringing Aka dauka, Banji meh akace achan Bangaren bah. Dan Murmushi Yayi Yace
"Am Waiting For You"
Sannan Ya Kashe Kiran, Baifi Awa Daya da Wani abu bah Akai Knocking Kofa, Dsauri Yarima Ya mike Ya Fita Ya bude, wata Kyakyawar Yarinya Ce Fara Ta Shigo Ta Rungumeshi Tana Dariya. Shima Dariyan Yayi Tace
"Ka Manta Dani Prince, Ai naji kayi Aure"

Gefen Fuskanta Ya Shafa Yana Kallan Kwayan idonta
"I Dnt Hv time For All dis Conversations, Am in need"
Daukanta Yayi Chak Tana Dariya ya Nufi Dakinshi da Ita..
Kiran Sallah neh Ya Tashi Parveen, Addua tai Ta Mike Ta zauna Sannan Ta mike Ta Nufi Toilet, Wanka Tai Ta dauro Alwala Ta Dawo Dakin, Kayan Jikinta ta Sauya Tasa Hijabi Ta Shimfida Sallaya Ta Tada Sallah, Tana Idarwa Tai Adduointa. Shiru Ta zauna Jugum Tana Tunani. Chan Ta Mike Tuna Jiya Deeza Ta bude kit taga Qur'ani, Budewa Tai Ta dauko Qur'anin Ta dawo Kan Sallayan Ta Zauna, Suratul Maryam Ta bude Ta Shiga Karantawa a Hankali Cikin zazzaqan Muryanta, bata Tashi bah Saida Taga Garin yayi Haske a Hankali Tace
"Sadaqallahul Azim"
Ta Rufe Qur'anin Ta maida Cikin Kit din...

Knocking Aka soma Yi a Qofan Falo, Ta Fita Ta Bude, Kuyangi neh dauke da Kulolin abinci kala kala, hanya ta basu suka wuce, kan dinning Suka Aje Sannan Suka Zube dan Kwasan Gaisuwa, amsawa tai suka fita. Shafa Cikinta Tai ta yamutse Fuska, Waige Waige Ta Soma Yi, wani qofa Ta Hango Ta qarasa ta bude a Hankali. Kitchen Ta gani, komai na Buqata Akwai a Ciki, Sosai Kitchen din ya burgeta. Dube dube ta Soma Yi, chan Ta Hango Wani set din plates, kwalin ta bude ta dauko daya ta Wanke, da Dauki chokali Shima Ta Wanke Ta Fito. Tana Zama Kan Dinning din Taji An Bude wani qofa daga Gefenta, Kai Ta daga Cikeda Tsoro...

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
🏀🏀🏀 πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.