A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 4 of 25
Page4β£
A hankali yake binsu Har yaga sun nufu wani Hadadden Wajan shaqatawa, A Hankali ya saki Lallausan murmushi Har saida Fararen Haqoranshi suka baiyana, Parking sukai Drivern Ya fito dasauri ya zagaya ya budemata kofan, qafan damanta ta sako a qasa Sannan ta Sauko na Hagu ta fito a hankali tafara takunta Maijan Hankali Altine na take mata baya riqe da wayoyinta da jaka, wani dan Qaramin Canopy suka Samu, Parveen ta zauna Sannan Taima Altine alaman itama ta zauna. Samarine da Yanmata a wajan dukansu cikeda farinciki, kowanne canopy ka juya zakaga masoyane zaune suna Hira cikeda nishadi, Dan Murmushi Parveen ta saki daidai nan service din wajan ya iso, Cikeda ladai ya kalli Parveen Yace "Ranki ya dade meh kikeso??" Altine tai Saurin tareda da Fadin "Ruwa zaka kawo sai fayrouz da meat pie" Amsawa yayi harya juya parveen tace Cikin lallausan muryanta batareda ta kalleshi bah "Make it 3 pls" Amsawa yayi yabar wajan dasauri..
Daidai nan Fardeen ya qaraso wajan tareda neman kujera ya zauna, Altine ta mike dasauri, Murmushin mugunta Yayi yana Kallan Parveen data hade rai Yace "No! Bah sai kin tashi bah yanzu zan bar wajan" juyawa Yayi yaga mutane burjik a wajan kowa na Harkan gabanshi, Yawanji Masoyane. Ya kara Sakin Murmushi Sannan Yace Cikin Zazzakar muryanshi kamar namai jin barci "Paveen Or What ever uh r Cal, Har keh kin isah kizo gizanmu ki gayamin Magana??. Ni Nafi Qarin a Wulaqantani, indai Jahilci neh zan nuna miki koh Hali irin na jahilai" Tabe Baki Tai Tareda Kauda kai. Bata Ankara bah Taga ya Buga Tabur din tareda mikewa, Hakan yasa kowa dake Wajan Hankalinshi ya dawo kansu, cikin Kakausan Murya Ya nunata da dan yatsa Yace "Kinyi Kadan, Bakeba kaf danginku. Soyaiya ceh nace banyi dole neh?? Meh zanyi dake Har dazaki dinga bibiyata, Oh! Dan nace bana sanki Shine Zaki rinka bibiyana Akan na Kusanceki??, Mutanen dake wajan suka zazzaro ido suna kallan juna Yace "meh kike dashi??, inaso naja miki kunni kar ki qara kiran wayana ko kice zakizo nemana Akan daqiqin qudirinki na fada miki, Banza Mazinaciya", yana Gama fadi yabar wajan dasauri tareda jan tsaki, Har Yabar wajan Mamaki neh Qarara a fuskarta, Hawayen dake Maqale a idonta ya qarasa zubowa, Mutanen Dake Wajan sai Kallanta suke Tareda Allah wadai da Halinta..
Kallan Altine tai idanunta chabe Chabe da hawaye Tace "Altine mu tafi" Altine ta kwashi Wayoyinta da jakanta, kuka sosai Parveen take a mota har Suka iso gda, Dakinta ta nufa tama Altine alama na karta biyota, Ta fada kan Gado ta fashe dawani matsanancin kuka. Fulani taji Dawowansu tanata sa ido taga Parveen anma Shiru har wajan Minti talatin, dakanta ta nufi dakin Tareda Sallama, Parveen najinta ta mike daga kwancen datake ta gogoge Hawayen Fuskanta, Fulani ta qaraso dakin Tace "Lapia Parveen naji dawowanku inata sa ido naganki yau nayi kewanki baki nan balle muyi hira" qago Murmushi tai Tace "Lapia lau fulani, Nagaji neh shiyasa dama Yanzu nake shirin zu..." Saurin Katseta Fulani tai da Fadin "Ya naga idonki yayi ja?? Parveen fadamin Gskiya meke damunki??" duqar dakai tai tace "Bkmai Fulani wani abune Ya fadamin ido" Dan Murmushin rashin Yarda fulani tai ta riqe Hannunta ta miqar da ita tsaye Tace "Muje kiga Wani abu" Tare suka fito Haraban gidan, Kamar ance ta dago suka Hada ido da Fardeen Dake chan nesa dasu Cikin Yar runfa suna Hira Shida Abokinshi, Wani Malalacin Murmushi ya Sakar Mata ta kauda kai dasauri Fulani na rike da Hannunta, Garden din Gidan Suka nufa, Sakin Baki Parveen tai Tana Kallan Garden din, A hankali ta Saki Hannun Fulani ta Qarasa Cikin Garden din, Saita nemi Bakin Cikin dake damunta ta Rasa, Ado Akaima Garden din, Fulawas neh burjik gwanin ban sha'awa, Daga gefe Guda hotunanta neh kala kala, Sai dan wanni kyalle da Aka Rubuta "Welcome to Badras Kingdom Princess parveen" Dariya tai Ta juya tana Kallan Fulani, Dagudu ta Qarasa tareda Rungumeta tana Dariyan Farinciki, Cikeda jin dadin yabawan datai Fulani Tace "Mai Martabane Yasa Akai Wannan" Sakin Fulani tai Ta karasa kan Wani hadadden Carpet dah aka zube Gifts Kala Kala, Ta zauna Tana Budewa Cikeda Farinciki...
Fardeen dake Zaune sanda su Fulani suka Wuce Hankalinshi Yaqi kwanciya Ya Kalli Mahdi Yace "Au b ryt back pls" bai jira mai zaice bah ya nufi Garden din, mutuwan Tsaye yayi yana Kallan Garden din, Ranshi neh Ya baci dan Yasan bah Wanda zaisa ai Wannan Sai mai martaba. Ranshi a bace Yabar Wajan a Ranshi Yana cewa "Banason Zuwan Yarinyan nan I hate her, duk sanda tazo banasamun kulawan Mai martaba balle Fulani" da Wannan Tunanin ya nufi side dinshi kota kan Mahdi bebi bah ya wuce...
Tho Fah mudaije Zuwa...
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
A WANI MASARAUTA
π€π€π€ π
By Ummy Abduol
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.