Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 25

Page2⃣2⃣

Dedicated dis Page to *Umma Yahaya Musa (Sisin Mama)* Thnks For Ur lav n support..

Dan Murmushi Tai ta Koma Daki Tadauko Biro. Juya Papern Tayi ta Fara Rubutu kamar haka:
_Bandamu da Ko nazama Gyne dr ko Karnazama Bah Yanzu, Saboda Jidani Abinda Ka Karanta Knan. Alhamdulillahi Tunda nasamu wanda Yafi Mahimmanci, Bandamu da saina Rami na nasara Bah. Kaga ko A Nan Nafika, tunda Ni Bah Wanda Ya Taba Ganina Da Wani namiji mun Riqe Hannu Ma Balle Har Yakaiga Abinda kai Kakeyi...Kae qoqari ka koma koda Islamiyan Zaure ne Kasan Banbancin Duhu da Haske Dan Har Yanzu a Cikin Duhu tsundum Kake_
Shiru Parveen Tai tana Nazarin Mai Zata Qaramai Wanda zai Kara Baqantamai Zuciya. Ganin Tana neman Yin Latti Yasa Daga Qasa Ta Rubuta "Princess Parveen Khaleed".

Papern Ta ajiye a inda Ya aje Mata Littafin, Tai dan Murnushi Tabar Wajan. Tea Ta Hada Tasha a gurguje ta Fada Toilet Tai Wanka Ta Fito, tana Shiryawa Ta Fito ta nufi Wajan Motoci, A nan Taga Sallau, Sam Batama Ganeshi bah Saida Taji Yana Mata Godiya. Kallanshi Tai Cikeda Tausayawa
"Karka damu Mallan, Yiwa Kaine"
Hannu tasa Cikin jaka ta ciro bandir din Yan Naira Hamsin ta miqa Mai
"Kayi Haquri da wannan Bah Yawa"
Godiya ya Shiga mata, Tai saurin Dagamai Hannu ta Shiga motan suka bar gidan.
Duk abinda ke Faruwa a wajan Fulani na daga Chan Wajan Side dinta tana Hangosu, Murmushi Tai Tareda Girgiza Kai..

Shiru Fulani Tai tana Tunani
Watan Auren Yarima da Parveen Daya knan, Ta Qara Gane Halayan Parveen Nason Kyautatama na Qasa da Ita, Da Sauransu. Ta Lura Akwai Wanni qulaliya Tsakanin Yarima Da Parveen tun Bayan Auren da Kwana Biyu, Kallansu Kawai Take...

Yauma Qarfe Biyu Suka Fito daga Lectures, Kiran Dan Ladi Driver tai Yazo Ya dauketa. Yasmeen Daketa Kallanta Tace
"Parveen Tun Sanda Mukasan Juna Kullum Nake Ganinki da Damuwa, Gani nai Kamar ni Wacce Zaki Fadama Damuwanki neh dan Nabaki Shawara Nakuma Tayaki da Addua"
Kallanta Parveen Take Tana Murmushi
"Babu komai Yasmeen, Anma Idan ma Kika Tayani da Adduan Bakiyi Laifi bah"
Shiru Yasmeen Tai Tana Nazari, Chan Saiga Drivern Gidansu Yasneem Ya Qaraso, Sukai Sallama Ta shiga Ta Tafi. Shiru Shiru dan Ladi Bai Zo Bah, Kiranshi Ta Qarayi Ya bata Haquri tareda Fada mata Motarce Ta Lalace Masa A Hanya..

Shiru Tai Tace
"Shiknan Idan An Gyara ka Wuce gda Kawai ni narin nemi Taxi"
Tho Yace Treda Kashe Wayan...

Tunda Yarima Yaje Office Tunanin Yanda Zamansh da Parveen Yake A Cikin Gidan Kawai Yace, Yanzu Yarinyan nan Tafara Bashi Mamaki, Yanda Batada Tsoro Take Taranshi Ido da Ido Ta Zazzaga Mai Rashin Mutumci Tai Gaba. Tsaki Yayi tuna Akwai Ayuka Gabanshi, Files din Daka Gabanshi na Patients Ya Fara dubawa. Dafe Goshinshi Yayi da Hannu Daya
"Oh Shit! Tunanin Stupid Girl din nan na Nema Ya Taba Aikina, yanzu gashi na Manta da Files din nan a gida"

Mikewa Yayi Yadau Car key dinshi Yabar Office Din, Haraban Asibitin Yake ketawa Cikin Taku Na Qasaita, Hannun Daya Cikin Aljinunshi, Matan dake Wajan Sai binshi Suke da Kallo har ya Shiga Motarshi Ya Tada Yabar Asibitin. Yana Isa Gida Direct Side dinsu Ya nufa, Dakinshi ya Shiga Yadau Files din Ya Fito. Har Ya Wuce Dinning Din Ya dawo Yaga Ko Tadau Littafin, Ganin Papern Shi kadai Yasa Ya Qarasa Wayan Yadau Papern Yana Dubawa...

Abinda Ta Rubuta Yaci Karo dashi, Gyara Tsayuwa Yayi ya Karance Shi Tsaf, Ransh ne Ya Baci. Lalai Yarinyan nan na Qorarin qureshi. Wurgi Yayi da Takardan Ya Bar Falon A Fusace... Bai Dawo Gidan Bah Sai Bayan Isha'ai, Yana Shigowa Gidan Yayi Parking Motarshi Ya Fito. Sallau ne Ya Tareshi Yana Mai Sannu da Zuwa, Da Mamaki Yarima Ya Kalleshi
"Meh ka Qara dawowa yi gidan nan??"
Nan da Nan Jikin Sallau yadau Rawa dan Yasan Halin Yarima, Daidai Nan Parveen Itada Atika Sunzo wucewa Zuwa Side Din Fulani, Dan An Aiko Mata Batajin Dadi. Jin Abinda Yariman Ke Cewa Yasa Ta Qarasa Wajan Dasauri
"Ni Nasa Ya Dawo Saboda banga Dalilin Koransh Bah"
Juyawa Yarima Yayi Yana Kallanta Ido Cikin Ido
"Akan Wani Dalili?? Har ni na Kori Wani Banza Talaka Ki Dawo Dashi. Koh Nan Masarautar Ubanki neh"
Ranta Neh Yayi Mugun Baci, Ta kalli sallau Tace
"Jeka Abinka"
Rusunawa Yayi Ya Mata Godiya Yabar Wajan
Atika Na Ganin Yabar Wajan Itama Tai Saurin Barin Wajan..

Kallan Yarima Parveen Tai Ranta Bace, Nan Bah Masarautan Ubana Baneh kamar Yanda Ka Fada, Anma Ka Sani, A Namu Masarautar Ansan Mutumci da Darajan Dan Adam. Kuma Dawowa Ya Dawo Knan, Kai Baka Isa Ka Koreshi Bah. Nunashi Tai da Dan Yatsa, Zan Zauna a Masarautarku Nakuma Fika Iko da Masarautar. Hannu Ya daga Zai Kai Mata Mari Sukaji Muryan Fulani, Qarasowa Wajan Tai Dasauri Tana Kallan Yarima Rai Bace
"Karka Kuskura Hannunka Yakai Kan Kuncinta, idan Kuwa Yakai Ni dakaina Zan Rama Mata. Dama Yarima Dalilin Auren Nata kenan Kaci Mata Mutumci?? Duk Abinda Ke Faruwa a Gidan nan Atika Na Kawomin Labari Sharewa Kawai Nake"

Nagode Sosai Ka Kyauta. Hannun Parveen Taja Suka Bar Wajan. Mutuwan Tsaye Yayi Ya Bisu da Kallo Har Suka Bar Wajan. Dukan Motan Yayi Rai Bace Yabar Wajan, Suna Shiga Side din, Fulani Ta Kalleta
"Ki Cigaba da Hakuri Parveen, Nidai Bazan Rabaku Bah. Nasan Watarana Sai Labari kinji"
Dan Murmushi Parveen Tai Kanta Na Qasa
"Bakomai Fulani, Dama Nazo neh Naga Jikinku. Dazu Atika Take Fadamin Bakida Lapia"
"Naji Sauki, Dama Dan Ciwon Qafa neh Kuma Yayi Sauki"
"Allah Ya Qara Sauki"
Fulani ta Amsa da "Ameen"

Shawarwari Fulani Ta Dinga Bah Parveen Akan Yanda Zatai Hakuri Ta Zauna Da Mijinta, Sun Dade Tana Mata Nasiha Sosai sannan Tai Mata Sallama Tabar Side Din itada Atika. A Falo Suka Tarar da Yarima Kan 1seater Fuskan nan Yayi Jawur, Yayi Crossing Kafa Yanata Kad'a Na Saman, Alamar Ita Yake Jira...

*Kuyi Manage da Wannan Banida Chargi neh dts Y"

Ummy Abduol✍🏻
Ο€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.