A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 25
Page1β£3β£
Shidai Sarki Kabeer bai Qara cewa Komai bah Akan Maganan, haka suka Cigaba da hirarsu..Kwanansu uku Suka Koma, Ranan da Suka koma fulani ta iske Mai Martaba a side dinshi, Newspapern dake Hannunshi Ya Aje Yana Kallanta, Ta zauna Kan kujera tana Kallanshi, Dogaran dake gefenshi Yama nuni Suka Bar Falon Dasauri...
Ya Kalleta Cikeda Tsokana
"Uwargida Sarautar Mata, Yana Ganki neh Yau wani iri??"
Fuskanta bah Fara'a Ta kalleshi
"Ranka Ya Dade bai Kamata Kai Irin Furucin nan Akan danka bah"
Ya Dago
"Kamar Yha??"
"Muna Magana Akan Yarima da Parveen kuma naji ka Sako wani Maganan"
Murmusawa Yayi yana Kallanta
"Rabiatu knan! Keh Kanki kinsan Hali irin na Yarima. Bah saina Fada Miki bah, Tho Fisabilillahi Jibi abinda Yayi Rannan Har Saida Ya Kwana Magarqama"
Saurin Katseshi tai da Cewa
"Wannan Ya wuce, Rayuwar dana nake Tunani, Yace bazai iya Rayuwa bah parveen bah. Ni kuma banason rasa shi"
Dariya Mai Martaba Yayi qasa, Qasa yana Kallanta
"Maida Wuqar Uwargida, Na gama Shirya Komai. Sati mai kamawa Insha Allahu za'aje nema mai Aurenta"
Murmushi Fulani tai ta Harareshi da Sigar Wasa
"Mai Makon ka fadamin tunda na Shigo ka barni inata Asarar kalamaina"
Dariya Sosai Mai Martaba Yayi Suka Cigaba da Hirarshu Cikin Nishadi...
Yau Monday Tushan Aiki, Tunda Asubah da Yarima Yayi Sallah bai Koma bah, abubuwan da Duk yake Buqata Yasa dogaranshi Suka Hada Mai a Wata Yar Jaka, Wanka Yayi Ya Shirya Cikin Yellow Suit da Black Shirt, Sai black tie. Qafafuwanshi Cikin Wata Hadadiyar Black cover. Ga Gashin.nan Yasha Gyara Kamar Na india.
Kayan sun Matuqar Amsarshi, abinda da Farin Fata, Ni Kaina Ummy Abduol Saida Ya Burgeni. Yana Tafe Dogaranshi na Takemai baya Rike da Breifcase dinshi.da kuma Wata Yar Jaka, Dakin Fulani Ya Shiga Ya gaidata
Ta Kalleshi Tana Yar Fara'a
"Yau Za'a Fara zuwa asibiti??"
Kai Kawai ya Gyada Yana Danna Wayarshi
"Tho Allah ya Tsare Ya kiyaye Hanya, A Kula Dan Allah da Haqqin mutane. Sannan Ka Tuna Ran dan Adam Kake Aiki akai Banda Sakaci"
Mikewa yayi Yana duba Agogon Hannunshi.
"Insha Allah Fulani"
Fatan Alheri tamai ya fito Ya nufi side din mai Martaba dan Safiya neh bai Isa ace Yaje Fada lokacin bah
Zaune Ya Sameshi Yana Lazumi, Saida Ya Iddar Sannan Ya Amsa
Yamai Addua Sosai Tareda fatan Alheri, Ya Fito Ya Shiga Motarda Aka Tanadar Mai Dan Zuwa Aiki, Dogaranshi Suka Shiga Dayan Sai "Fardeen Specialist Hospital"
***********
Parveen Na Cigaba da Karatunta Cikin Kwanciyar Hankali da Annasuwa, Koda Su Umma Suka dawo basu Mata Magana Akan Yarima bah, Jira suke Sai Sanda Akazo neman Auren Sannan ta Sani, dukda ita Lokaci Zuwa Lokaci Takan Tuna Yarima Sannan Taji Gabanta Ya Fadi. Addua Take Sosai dan neman Tsari daga Sharrin Yarima. Tana Yawan Fadama Aminiyarta Deeza Halin datake ciki, Kwantar Mata da Hankali koda Yaushe takanyi Tareda Jadada mata Dagewa da Addua...
Cikin Satin Nan Yarima Yaba Aikinshi Mahinmanci Sosai, Kuma Yana Matuqar jin Dadin Asibitin, Kasancewarshi Gynecologist (Likitan Mata) hakan Yasa yawan Harka da Mata, Wasu daga Cikin patient Masu zuwa Asibitin Suna Zuwa neh Kawai dan Ganinshi Saboda Yanda Sukejin Labarin Haduwarshi, Hakan Yasa Neman Mata wajan Yarima Ya Qaru "Allah Ya Kyauta"...
Ranar Juma'a Da Safe Sarki Kabeer da Tawagarshi Suka nufi Kasar Gombe, Tun a Airport suka Hadu da Tawagar Sarki Khaleed da Sukazo tarbarsu. Suna Sauka Suka Shiga Mota Suka Nufi Gida, Saida Akai Sallan Juma'a Sannan Suka Samu Suka Qebe, Bayan sunci Sunsha, Umma Tazo Ta gaida Mai Martaba sun dan Taba Hira Sannan Tabar Falo, Sarki Kabeer sai Tambayan Parveen Yake, Mai Martaba Yace Tana Makaranta..
An Tsaida Maganan Aure, An Bada Sadaki Naira Dubu Dari. Sannan Ansa Ranar Biki Wata Daya, Sarki Kabeer bai Kwana bah Suka Juya Tareda Tawagarsa Cikeda Farin Ciki, Sun Koma Gida Lapia. Fulani Ta Iske Mai Martaba a Side dinshi, Bayani yamata duk Yanda Akai, Farin ciki Tai Sosai Ta mike Tana Cewa
"Yau Yarima Zaisha Albishir"
Dan Dariya Mai Martaba Yayi
Tadan Rusuna
"Ka Huta Lapia"
Ta fita daga Dakin Fara'a Kwance Kan Fuskanta...
Yarima na dawowa Fulani tasa A mata kiranshi, Ya qaraso Side din yana gungunai. Gefenta yasamu ya Zauna yana Turo baki. Ta kalleshi tana Murnushi
"Kasan Dalilin Kiranka??"
Kai Ya gyada Alamar Aa
Qara Murmushi tai Tana Kallanshi
"Mai Martaba Yaje Qasar gombe Yau Akan magananka da Parveen"
Gyara Zama Yayi Yace
"Tho ya Ake Ciki fulani??"
Sumar kanshi ta Shafa
"An Gama komai biki nanda Wata Daya"
Dariya Ya saki Ya Rungume Fulani
"Much Thanks Fulani, Shiyasa Nake Sanki"
Ya Mike
"Barinje Naima Mai Martaba Godiya"
Bai Jira mai Fulani zatace bah Ya fita Yana Fara'a Kamar dagaske..
Parveen Bata dawo gidan bah Sai Yanma, Saida Taci Abinci ta huta Sannan Jakadiya Ta Shigo, Rusunawa tai ta kwashi Gaisuwa Sannan Tace
"Ranki Ya dade Mai Martaba Nasan Ganinki"
"Tho Tace"
Jakadiya tabar dakin
Ko Minti daya bata Qaraba Ta mike ta Nufi Side din Mai Martaba da Sallama..
Ya Amsa Ta nemi guri ta zauna..
Shiru ne ya Biyo baya. Chan Ya Dago Ya kalleta Yace
"Parveen a Matsayinmu nida Mahaifiyarki, Munada Daman da Zamu zaba Miki Miji wanda mukaga ya Dace da Tsarin Rayuwanki, Mai Hankali mai Tarbiya dan Gidan dattako.
Gabanta neh ya fadi ta dake Tana Cigaba da Sauraranshi...
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
*A WANI MASARAUTA*
π€π€π€ π
By *Ummy Abduol*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.