Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 11 of 25

Page1⃣1⃣

Dedicated dis page to *Maradin Zazzau's Family..Alh Haruna Muh'd Jumare* Allah Yaja kwana UncleπŸ‘πŸ»

Cikin Ikon Allah tasamu ta shiga Hall din, tana Shiga lecturan ya shigo. Saida Tagama Sannan Ta fito Tai Kicibus da Aminiyarta Hadeeza Yar Maradin Zazzau. Parveen ta Qarasa ta Rungume Deeza, Deeza ta hade rai ta Rungume Hannu
"Lallai Parveen Kikai Tafiyanki, Saidai na kira naji kina Gombe"
Dan Murmushi Tai Ta Marairaice Fuska
"Am Sorry Bae! Wallahi Tafiyan neh Yazo min cikin Gagawa, Sai ana gobe Zan Tafi nasani. Buh ai nabaki Haquri"
Tabe Baki Deeza tai Tareda Murmusawa
"Na Haqurah Anma nima zan Rama"
Parveen ta shafa Cikinta Tareda Yatsine Fuska
"Muje Musamu Wani abu Yunwa nakeji"
Ok muje. Motan Parveen suka Shiga Suka Fita daga cikin Schl din, Wani hadaden Eatry Suka nufa, Abinci mai Raida Lapia Parveen tai musu odering, Sunci Sunsha Deeza ta Kalli Agogon Hannunta
"12 Dai Munada Lectures knsani"
Itama Agogon Hannunta ta duba, Ai Yanzu 11:31am neh munada Sauran 30mint koh??"
Kai Kawa Deeza ta daga Tana daddana Wayanta. Chan ta kalli Parveen
"Ahan Bae Wai dan Allah dagaske kike abinda kika Fadamin Rannan??"

Parveen ta dago Tana Kallanta
"Nameh fah??"
Maganarki da Yarima mana
Tabe Baki Parveen Tai
"Qwarai kuwa"
Idonta ya Ciko da Kwalla ta Kalli Deeza
"Tunda Nake a Duniyan nan Ba'a Taba Cimin Mutumci irin Ranan Bah, Yanzu dawani ido zan Kalli Mutanen Gombe??"
Hawayen dake Maqale a idonta suka Gangaro
"I Hate Him Deeza, I Hate Him! Tunda Nake Ban Taba Tsanan wani bah Kamar Yarima. Na Tsaneshi! Na Tsaneshi!!"
Kukane Ya Kufce Mata, Deeza ta Dawo Kusada Ita ta zauna tana Lallashinta
"Kiyi Haquri Pls, Ai kema kin Guma Masa. Nasan Wannan Abinda kikamai bazai Taba Mantawa dakebah Har Qarshen Rayuwarsa"

Dagowa tai Idanunta Chabe Chabe da Hawaye tadan Mata Murmushi
"Deeza Mazinaciya fah ya kirani"
Ta Qara Rushewa da wani Sabon kukan
Haba Bae! Kar wannan Ya daga miki Hankali, Ni Shaida ce akan Halinki. Karki Bari Maganganun Yarima Suyi Tasiri a zuciyarki Pls, Karki Damu Allah zai Saka miki kinji??"
Kae Kawai Parveen ta gyada, Dakyar Deeza tasamu ta Lallasheta Sannan suka Bar Wajan Suka Koma Makaranta..
Yanma Lis Parveen ta Dawo Gida, Direct Side din Ummanta ta nufa, Dakinta tq shiga ta fada Jikinta Tana Yar Shagwaba. Umma Ta Kalleta baki Bude
"Lallai Parveen sodai kike ki Qarasani ki Huta koh??"
Turo Baki Tai Tana gungunai
"Kinga Fah Fulani Tana Yarda Nahau Jikinta Har Barci nakeyi"
"Iyeh! Tho ai Fulani kikace, Nikam bazan iya bah"
Qara Turo baki tai Ta Mike
"Ni Natafi tunda Bakyaso ina Hawa Jikinki, Kuma Ana qarayin Hutu zan koma Wajan Fulani nabarki"
Bata jira mai Umman Zatace Bah tabar Dakin tana gungunai
Murmushi Umman tai
"Parveen! Parveen!! Allah ya Shirya"

*Masarautar Gombe*
Yau Mai martaba bai shiga Fadaba Yana Side dinshi Tareda Manyan baki da sukazo Ganinshi daga Kasa Kasa, Kowanne Yazo neh Dan Tallata hajarshi na Kayan Aiki na Asibiti, Wasu kuwa neman Aiki sukazo, Saida Ya Sallami Kowa Sannan Yasa Amai kiran Yarima. Ba'adau lokcibah sai Gashi, da Sallama ya shigo ya samu guri qasan carpet Ya zauna tareda Gaisuw, mai Martaba ya Amsa Fuska a Sake. Kallan Yariman Yayi
"Ina Fata ka gama dukkan Wani Shirye Shiryenka dan sati mai zuwa insha Allah za'a bude Asibitin"
Kanshi a duqe ya Girgiza kai
"Na Gama ranka ya dade, Allah kuma Ya kaimu"
Ameen Inji Mai Martaba Ya Qara kallanshi
"Inaso na Hada Qayataccen Biki dan bude Wannan Asibiti, Kana iya Gaiyatan Abokanka na kusa dana qetare Duka dan Zuwa tayaka Murna"
Qara dukar dakai Yarima Yayi Yanadan Murmushi
"Godiya Nake Ranka ya Dade"
Yarima Inaso Kazamo mai Gaskiya da Ruqon Amana Akan Aikinka, kazamo mai Juriya da Tawakalli. Karka zamo Cikin Ma'aikata Masu Wulakanci da Talakawa da Rashin Zuwa duba Marasa lapia dawuri. Dan Allah kai Qoqarin kiyayewa, Sannan Kazamo Maiba Na Qasa dakai Hakinsu daidai Kwargwado banda Cuta da muzgunawa."
"Insha Allahu Mai Martaba Bazaka Sameni da Duk Wadannan bah, zanyi qoqarin kiyayewa."
Murmushi Mai Martaba yayi
"Allah ya maka Albarka"
Ameen Ya Amsa
Tashi Kaje
Ya mike Yamai Sallama Yabar Side Din...

Side din Fulani Ya nufa dan Fada Mata Qudurinshi, Kishingide ya sameta A Falo tana cin Yayan Itatuwa, Wata Kuyanga Tana Matsa Mata Qafa, Ya Zube Kan 2Seater Yana Kallan Fulanin, Fulani Ta Kalli Kuyangar, Tashi Kije. Ta Amsa Tareda Mikewa Dasauri ta Fita.
Kallan dan nata tai
"Yadai Lapia??"
Yadan Dago
"Bakomai Dama Akwai Maganan danakeso nafada miki neh"
Ta Mike Ta Zauna Sannan tace
"Ina Sauraranka"
Dan Murmushi Yayi
"Fulani na Dade inasan Parveen Anma narasa Ta Yanda zanyi na Fada miki, Pls ki Fadama mai Martaba Aje a Nema min Aurenta dan Allah"
Da Mamaki Fulani keh Kallanshi
"Yarima Kasan meh kake fada kuwa??"
Kai ya gyada Yana Kallanta
"Nasani Fulani, Idan ban Aureta bah..Ya taba Kirjinshi, Zan Shiga Cikin Wani hali pls ki Taimaka min"
Kusan d'a da Mahaifi
Tausayinshi Taji ya kamata Ta Kalleshi Cikeda Kulawa
"Karka Damu Insha Allahu Parveen Matarka Ce, Kuma Nasan Bazata qika bah"
Wani Qayataccen Murmushi Ya Saki
"Thank Uh Fulani Shiyasa Nake Qara Sanki"
Itama Murmushin Tai, Ya mike Yabar Falon Yana dariyar Mugunta...

Tho Fah... _Shin Fans kun. Yarda yarima Ya auri Parveen??_

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
🏀🏀🏀 πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.