A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 20 of 25
Page2β£0β£
Ai Dake da Bayin Gidan nan Babu Maraba a Wajena, Duj Daya Kuke. Dan Haka Ina Jiran Breakfast Nan da 1hour idan bah Haka bah..kwafa Yayi Yabar Dakin Tareda Bugo qofan"
Bin Kofan Parveen tai da Kallo, Murmushin Takaici Tayi Tareda Girgiza Kai. Saida Ta Gama Karatunta Sannan Ta Mike ta Nufi Kicin din. Cikin Mintinan da Basu Wuce Sha Biyar bah ta Fito dauke da Food Flask guda Biyu akan Tray. Kan Dinning ta Aje Ta koma Dakinta..
Wanka Tai Ta Shirya Ta dau Jakanta da Kyalle Ta Fito, Kicin ta Koma Ta Hado tea Ta dawo Palour Tasha Ta Maida Cup din Sannan Tadau Trayn ta dosh Hanyar Dakin Yarima. Knocking Tai Ta Shiga Da Sallama, Budurwar Ta Samu Zaune Tana Daddana Waya, Yarima Kuma Ya Fito knan Daga Toilet Daure da Towel daga Gani wanka Ya fito. Kallanshi Tai Tace
"Ranka Ya Dade ga Breakfast din An Gama"
Mamaki neh ya Kama Yarima Anma Ya basar, Kan Bedside Ya Nunama Alamar ta Aje, Bah Musu ta Qarasa Ta aje. Ta Kalleshi Tana wani washe baki kamar Doluwa
"Ranka Ya dade Akwai kuma Abinda kake buqata??"
Girgiza Mata kai Yayi. Ta Kalli Yarinyan dake Zaune Tace
"A Fito Lapia Yan Mata"
Dakin Tabari Dasauri Ta bar Side din Gaba Daya, Saida Taje ta Gaidasu Fulani da Mai Martaba Sannan Ta Shiga Mota Driver Yajata Zuwa School. A Hanya Neh Danladi Driver ke Fadamata Koranda Yarima Yama Sallau bayan Bulalan dayasa Amai.
Bah Qaramin Baci Ran Parveen Yayi Bah, Tace
"Dan Ladi Kasan Gidansh?"
Kwarai Rank ya dade ai baida Nisa da Gidan Sarki"
Nisawa Tai Cikeda Damuwa
"Inaso idan Ka kaini Ka Wuce Gidan Kace Injini Nace Gobe Ya koma Aikinsa"
Washe Baki Dan Ladi Yayi Dan Shi kanshi baiji Dadin Koranda Yarima Yama Abokin nashi bah.
Godiya Ya soma Mata, Batace komai bah Har Suka Qaraso makarantan Ya ajeta Ya Wuce..
Saida yarima Ya Shirya Sannan Ya Xauna Bakin Gadon, Budurwar Ya Kalla Yana Murmushi. Serve Us please, Murmushi Tamai ta miqe Ta Dauko Trayn. Gabanshi Ta aje Ta dauki Plate Dake Cikin Trayn Ta Aje Sannan Ta Bude Food Flaske Din, Danyen Plantain suka gani a Ciki, An Yanyanka Ko Bare Bawon Ba'ai Bah, Dagowa Tai Ta Kalleshi suka Hada ido, Dayan Kulan ta Bude nan ma Danyan Kwai Suka Gani Guda Goma a Ciki...
Ba Qaramin Baci Ran Yarima Yayi bah, Dashi Yayi Yana Huci Ya fita Zuwa Dakin Parveen, Banko Qafan Yayi ya Shiga, Bai Ganta Bah Yasa Ya Qarasa Toilet din, Nan ma Wayam, Duk inda Yake Tunanin Ganinta Ya Duba Batanan. Sai A Nan Ya tuna Jiya Sallau Yace Mai Tana Zuwa Makaranta. Bah Qaramin Kunya Yaji bah Wajan Budurwarshi, Hakanan Ya Bata Haquri Suka Fita Ya Saya Mata Breakfast Sannan Ya Ajeta Gida Ya Wuce Office..
Zama Yayi a Office Yana Tunanin Yanda Zai Bulloma Parveen, lallai Yarinyan Nan Ta Raina Min Wayo Zanko Yi Maganinta Kwanan nan. Mahdi neh Yayi knocking Ya Shigo Office din, Zama Yayi Yana Kallan Yarima
"Yaya Akaine Yariman Duk duniya"
Dan Yaqe Yarima Yayi
"Lapia Anma Fah bah Lau bah"
Tho Fah Lapia ? Meya Faru??
Furzar da Iska Yarima Yayi yana Kallan Mahdi
"Am Sick and Tired of That Stupid Girl, Wallahi Wani Lokacin Har mamaki take bani Yarinyan nan. Duk hanyarda Zatai disgracing dina Yarinyan nan Tasani"
Dan Murmushi Mahdi Yayi
"Yariman Duk duniya. Har Yanzu kaqi bin shawaran dana Baka, Shawaran Dana Bakan neh Fah Dalilin Aurenta"
Shiru Yarima yayi yana Kallan Mahdi, chan Ya nisa Yace
"Kasan Banasan Raini, N Na Lura Yarinyan Tashen Rashin Kunya Take. Buh Are you Sure it wil work??"
Gyada Kai Mahdi Yayi
Yarima Ya daga Kafada
"Shiknan Zan Gwada"
Hira Suka Shiga Yi Har Lokacin Wardround Yayi Yarima Ya tashi suka Fita Daga Office din...
Yau Da Wuri Parveen Ta Tashi, Waya Tama Danladi Driver Yazo Ya Dauketa. Tana Zuwa Gida Ta Fada Wanka, Ta Sauya Kaya xuwa Abaya Baki, Indomie ta dafa Taci Sannan Ta Wuce Side din Fulani. Hiransu Suketayi Kamar Yanda Suka Saba Har Wuraren La'asar. Parveen kwance Kan Cinyan Fulani Tana Shagwaba.
Dariya Fulani Tai Tace
"Niko Wannan shagwaba Naki Parveen naso inga Idan kinada Ciki Zaki Haihu"
Hannu Parveen Tasa ta Rufe Fuska tana Dariya
itama Fulanin Dariyan tai
Parveen Ta turo baki Tace
"Wallahi Fulani wani Gugun Lecture neh Ya bamu Assignment gashi da Wahala Wai Muyi Submitting Jibi, ni narasa Ta yanda Zanyi Assignment din"
Fulani ta Shafa Kanta Har Ta bude baki zatai Magana Sukaji Sallaman Yarima, Fulani ce Ta Amsa ya samu Guri ya Zauna Fuskan nan a Murtuke..
Fulani Tace
"Ai Shiknan mah Ga Yarima Kinsan shima Abinda Ya karanta knan"
Nan da Nan Parveen Ta hade Rai, A Ranta Tace
"Wallahi danasani daban Zami Wannan Course din bah."
Mikewa Tai Tsaye Tace
"Fulani Barinje Nai Girki"
Fulani Tace
"Shiknan Sai Anjima, Ki aikomin da Assignment din"
Tho Parveen Tace Tabar Dakin...
_kuyi manage da Wannan Bah Yawa_
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
*A WANI MASARAUTA*
π€π€π€ π
By *Ummy Abduol*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.