A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 14 of 25
Page1β£4β£
Dedicated dis page to *My Facebook Fans* Allah Ya barmu Tare..
"Parveen a Matsayinmu nida Mahaifiyarki, Munada Daman Da zamu Zaba Miki miji Wanda Mukaga Ya Dace da Tsarin Rayuwarki, Mai Hankali da Tarbiya dan Gidan Dattaku.
Gabanta neh ya Fadi ta dake Tana Cigaba da Sauraranshi
"Dan Haka A Matsayina na Mahaifinki na Zaba Miki Miji wanda Nasan Zakiyi Alfahari dashi ko bayan bah Raina"
Kanta na Qasa Batace Komai Bah
"Ina Fatan zayi Na'am da Wannan Auren, Anma Inaso ki Fadamin idan da Wanda Kikeso. Duk da Nasan Its Too late Saboda Har an Kawo Sadaki an kuma Sa Rana Nanda Wata Daya"
Hawaye ne Ya fara Zarya a fuskanta, Qoqarin boyewa Tai Kar Ya gani..
Dan Murmushi Yayi yana Kallanta.
Bakicemin Komai bah Parveen
Kanta Na Qasa Muryanta na Rawa Tace
"Ranka Ya Dade banida Tacewa. Na Amince, Zabinka shine nawa kuma ina godiya"
Murmushi Mai Martaba Yayi
"Allah ya Miki Albarka, Tashi kije"
Ameen Tace Tareda Mikewa Tabar Falon..
Tana Fitowa Ta Fashe da wani Matsanancin kuka, Ita bah Kukan Auren da Mai Martaba Zeyi mata bneh Aa, kukan Karatunta Take. Haka Ta Qarasa Side din Umma Tana kuka Sosai, Jikinta ta xube Tace
"Umma Meh Yasa mai Martaba bazai bari na Qarasa makarantana Bah Sannan Ya Auramin duk wanda nakeso??"
Shafa Kanta Umma tai
"Kiyi Haquri Parveen, Da nan da Gidan Aurenki duk daya neh. Kamar Yanda za'a kula dake anan Haka a Chan, karki damu kanki kinji??. Maganar Makaranta kuma Za'a miki Transfer Zuwa Chan Garin Sai ki Cigaba da Abinki"
Batace Komai bah Ta mike Tana Kuka Sosai Tabar Dakin..
Kwana Tai Kuka, Kota Kan wanda Za'a Aura mata batabi Bah. Washe Gari da Safe Tanada Test Dakyar Ta Tashi ko breakfast batai bah tai Wanka Ta Tafi, Idanunta Luhu luhu. Saida Aka Gama Test din Sannan Suka Hadu da Deexa. Kallanta Tai Da Mamaki
"Meya Sameki?? Daga Ganin idanunki kinyi kuka??"
Kamar Jira Parveen take Ta Fashe Da Kuka Tana Kallan Deeza.
Hannunta Ta Deeza ta kama suka Shiga Motanta, Kuka Parveen Take Sosai Dakyar Deeza Ta lallasheta Ta danyi Shiru
"Pls Bae Banasan Ganinki cikin Wannan Halin Fadamin menene?? Ko Yariman neh kuma"
Girgiza Kai Parveen tai Hawaye na Cigaba da Zuba
"Mai Martaba neh Yakeso Yamin Aure"
Dafe Kirji deexa Tai
"Aure!? Y??"
Girgiza Kai Tai
"Nima bansani bah Deeza, Niba Auren da zaimin ke damuna bah, Karatuna. Ke kanki kinsan Yanda Naci buri akan Karatun nan, Inaso na Zama Gynecologist. Inaso na Taimaka ma Yan uwana Mata.
Dafata Deeza tai
"Wannan Bah Abin damuwa bneh Bae, Ko kina gidanki Zaki Iya Yin Karatunki indai Mijinki zai Yarda"
"Ta Yaya Deeza??, Yanda Fa Umma Kemin Bayani Ba Inan Garin Zan Zauna Bah?? Tho ya makomar Karatuna??"
Shiru Deeza Tai Tana Nazari
"Karki Damu Pls, Allah Yana Tare Dake. Ki Cigaba da Addua Kinji??"
Kae kawai Parveen ta Gyada batareda tace komae bah
Haka Tai Yinin Ranar Hankalinta ba Akwance Yake bah..
Kwanaki Sun ja, Anata Shirye Shiryen Biki daga Duka bangaren Biyu. Har Yau Parveen batasan Wanda Zata Auraba kuma Bata Tambaya bah. Iyayen neh Kawai ke Shirye Shiryensu, Yarima ko da Parveen bah abinda Suke Shiryawa Bama Kaman Parveen da Tunda Akai mata Maganan Auren Batada Aiki sai kuka Sai tunani, Makarantan ma Ta daina Zuwa, Kullum idan Deeza ta tashi makaranta Sai Tazo ta Lallasheta...
Sarki Kabeer Yasa Anata Gyaran Inda Yarima Zai Zauna da Amaryanshi, Cikin Gidan neh anma Da Tazara Sosai Tsakaninsu Da Fada Sides din fulani da Martaba. Shiko Yarima Sam Baisa Maganar auren Akaba Aikinshi Yake bah Ruwanshi. Bilal ne Kawai keta Fadi tashi akan Bikin, Duk Wanda Yakama Ya sanar Mawa duk Ya Sanar...
Ana Saura Sati Biyu aka Kawo Lefe. Lefene Nagani na fada Ko lefe Zahra buhari albarka lol, Anata Yaba Kayan Lefen Itako Parveen na daki qudundune cikin Barko sai kuka take. Ganin Batada niyar Yin wani abu lokacin Bikin Yasa Umma ta nemi Deeza, Katin Gayyata Taba Deeza Tace Ta rabama Qawayenta, Tareda Ankon da umma Tasa Akai Oder dan Rabama Yan uwa da abokan Arziki, Deeza Ce Taita Zarya na Rabo Itako Gimbiyar Tana Gida Kullum Cikin Kuka...
Fulani Tasa an Hada dinner Wanda Za'ai Washe Garin Biki Haka Umma Itama ta Shirya Events Kala Kala Tareda Taimakon Deexa.
Ana Saura Sati Daya Hajiya Shuwa daga Maiduguri Tazo dan shirya Amarya, Ansha Daga da Parveen Saida Umma Tai mata Jan Ido Sannan Ta Yarda Aka Fara Gyarata Tana Kuka Sosai. Kullum Sai an Mata Gyara Cikin kwana Hutu Ta Qara Kyau kamar ba Itaba. Ana Jibi Daurin Aure aka Fara Events Wanda Aka Fara Da Arabian Night. Da Taimakon Hajiya Shuwa ta Shirya cikin Hadadden Arabian Gown Baki, Kwalliya Hajiya Shuwa tai mata Ta Fito Sak Kamar Balarabiya, deeza Ta Shigo dakin itama Cikin shiri, ta Rike mata Hannu Suka Fito Zuwa Hall din Cikin Gidan. Suna Shiga Wajan Yadau Tafi, Sai a Sannan Parveen ta Dago, Mamaki Ne Kwance kan Fuskanta Ganin Kawayenta na nesa dana Kusa, Wasu mah Tunda Suka gama Secondry schl bata Qara Ganinsu bah, A Hankali ta Rintse ido Tareda Duqar dakai Wasu zafafan Hawaye Suka gangaro mata...
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
*A WANI MASARAUTA*
π€π€π€ π
By *Ummy Abduol*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.