Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 25

Page1⃣2⃣

Wani Qayataccen Murmushi ya Saki
"Thank uh Fulani Shiyasa Nake Qara Sanki"
Itama Murmushin Tai, Ya mike Yabar Falon Yana Dariyar Mugunta...

Hidimar Bude Asibiti ne Ya kankama, Gaiyata Sosai Mai martaba Yayi, daga Ciki akwai Gwamnoni, Sarakun, Yan Majilisu, Ya uwa da abokan Arziki, Haka Itama Fulani Tayi Gaiyata Sosai dan a Tayata Murnar Bude Asibitin Dan Nata...

Umma nazaune Katin Gaiyata ta Sameta. Dukda Dama sunyi waya da fulani ta fada mata, Katin parveen Musamman Aka Kawo Mata daga Mai Martaba. Lokacinma Tana Schl, sai dt dawo tagani. Dan Tsaki Tai Ahankali Ta aje Katin
Umma dake kallanta Sun Sanda Ta Dau katin Tace
"Naga Kin Bata Fuska neh, jibi neh dai Kuma Tare zamu Tafi"
Tsuke Fuska Tai Tana Kara Kallan Katin
"Nifa Umma Inada Lectures Ranan"
"Haba Parveen, Dan kinyi missing Lectures na kwana Biyu zuwa uku Shine meh?? Kinga Fah Wannan Gaiyatar daga Sarki Kabeer Take. Shi Yace Abaki, kinga bai kamata ki Watsa mai Qasa a ido bah"

Gyada Kai Kawai Tai
"Shiknan Allah Ya kaimu"
Umma Tace "Ameen"
Barin Wajan Tai Tana gungunai, Ita bawai Batasan Zuwa bneh, Kawai Saboda Maqiyinta neh Yasa batasn zuwan, Tsaki Taja Ta qarasa dakinta Tana nazarin Yanda zata Subulbule zuwan. Da Daddare Mai Martaba Yayi Kiranka, Ta Je Side dinshi Ta Gaidashi Tareda Neman Wajan Zama.
"Gobe in Allah Ya nufemu da kaiwa zamu Tafi Masarautar Gombe dan Kinsan Akwai Taro na bude Asibitin Yarima Fardeen, Dan Haka Ki Zamana cikin Shiri"
Bata Fuska Tai Tadan dago ta Kalli Mahaifin nata
"Gobe fah inada Test harda Jibi, nima sai dazu ake Fadamin kuma idan banyi bah Zai Shafi result dina"
Shiru Mai Martaba Yayi Nadan Seconds Sannan ya klleta
"Shiknan Allah Ya bada Sa'a"
Ameen Tace Tana Yar Murmushi
Tashi Kije Abinki"
Duqawa Tai Kanta Qasa
"A Tashi Lapia"
Sannan Ta mike Tabar Falon Cikeda Farinciki..

Haka kuwa akai Parveen batabi Su Umma bah, Umma Dai Sam Bata Yarda da test dinda parveen tace Suna dashi bah. Abin bah qaramin daure mata kai Yayi bah, tho mai yasa Parveen batasan Zuwa Gombe?? Da Wannan tunanin Suka Kai Masarautar Gombe. Gidan Cike Yake da Baki Yan nesa, an Karamasu Tareda Basu Masauki, Umma Kam tana Chan Wajan Aminiyarta Fulani. Washe Gari Aka Hau Biki A Chan Haraban Asibitin Mai Suna "Fardeen Specialist Hospital"
Taro Yayi Taro, Kowa Daka gani Yana Cikin Farinciki, Bama Kaman Mai Martaba Da Bakinshi Yaqi Rufuwa...

Yarima Nachan Zaune Cikin Abokanan Shi Sai Hira Suke, Wanda Yawanci Wayanda Sukai Karatu neh Tare, Anan Yake Fada Musu Ya kusa Aure. Niko Nace "Wah Yce Ya Bashi?? Yaushe Akai Maganan Balle" Yawancinsu Mamaki Suke Saboda Sunsan Yarima Baisan Kalmar Aure, Sanin halinshi Yasa kowa Yaja bakinshi Yayi Shiru, Saidai Fatan Alheri dasuka mai...

Anci ansha, Sannan Aka Bude Asibiti, Mutane Suka Shishiga Aka Zagaya Ko Ina Na cikin Asibitin, Niko Ummy Abduol Sakin Baki nai Ina Kallan Asibitin, Kayan Aikin ban Taba Ganin Irinsu anan nigeria bah. Mutanen dake Wajan Sai Santin Asibitin suke Saboda Tsaruwanshi da kuma Kayan Aikin dake ciki. Addua Sosai Akai Sannan Kowa Ya Watse Cikeda Nishadi bayan An Raba Kyaututuka Kala kala. Su Mai martaba Gda Suka koma, Haka su Fulani da Ummah. Saida Aka Natsa Da Daddare Lokacin Duk baki Sun koma, Fulani da Umma Sai Sarki Kabeer da Sarki Khaleed Zaune a Side din Mai Martaba Sunata Hira, Kayan Itatuwane a Gabansu, Da Abinci kala kala.

Fulani ce Ta Kallesu Tace
"Damako Akwai Wani Abu danakesan Fadama Mai Martaba, Anma Tunda Ga sarki Khaleed Saina Fada Duka"
Sarki Kabeer Ya Kalleta
"Maganan Meh Fah?"
Fulani Ta gyara Zama
"Last Week ina Zaune Yarima Yazo ya Sameni akan Maganan Parveen, Yace Gaskiya Yana santa kuma Aurenta Yakeson Yi"
Murmushi Sarki Khaleed Yayi Yace
"Indai Wannan neh Bah Matsala ni nabashi"
Itama Umma Murmushin Tai
"Wannan Ai bah Abin Damuwa baneh. Allah Ya shige Mana Gaba Ya Sanya Alheri"
Sarki Kabeer koh Tsuke Fuska Yayi
"Niko Sam Ban Amince bah"
Dukkansu Suka Juyo Suka Kalleshi da Mamaki
Ya Gyada Kai Sannan Yace
"Yarinya Mai Hankali kamar Parveen za'a dauka aba Fardeen??, Aa Bazai Yuwu bah. Salan Yaje Yayita Cutanta"

Dan Murmushi Sarki Khaleed Yayi
"Na Yarda da Tarbiyan Yarima, Nasan Bazaiyi Abinda Kake tunani bah"
Girgiza Kai Kawai Sarki kabeer Yayi yana Murmushin Qarfin hali
Umma Tace
"Bah Damuwa Ranka Ya dade, Yarima Mutum neh Na Qwarai bashida Matsala"
Shidai sarki Kabeer bai Qara cewa komai bah Akan magana, Haka suka Cigaba da Hiransu...

_Shin Fans Kodai Sarki Kabeer naciki neh??_

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
🏀🏀🏀 πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.