Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 25

Page7⃣

Tsalle Parveen tai Tace "Yauwa haka nakeso" Sai kuma mu jira Cika Aiki kawai, Itama Altine Murmushin tai, Parveen tace "Muje Wajan Umma" tana tafe Altine na take mata baya, Lokaci lokaci takan saki Murmushi har suka qarasa Side din, Sun baje Umma nata bata labarin yanda Tai kewanta Sanda Bata nan, Parveen koh saima Umma dariya take, lokaci lokaci Takan duba Agogo. Har Umma takaiga cewa "wai Parveen wannan duba Agogon Fah??" tai Murnushi Tace "Bkmai"..

Bilal idonshi nakan kallan dayake Coz ana Favorite hindi film dinshi "Mujshe dosti karoge", Yarima koh tunda ya zauna yake jinshi wani iri ya mike yana dan tangaji Yace "Bilal idan kagama ka tasheni, Zamu fita da mai martaba anjima Around 12, am Slipy" kai kawai Bilal yadaga batareda Ya Kalleshi bah, Daki ya Shga dakyar Ya fada kan Gado, Barci neh mai nauyi ya daukeshi, Sam Bilal ya manta Yana Gama Kallanshi Yabar Side din. Shiru shiru Mai Martaba Baiga Yarima bah dan Haka Yasa amai kiran Jakadiya, Ta karasa Fadan dasauri, Umartanta yayi ta kiramai Yarima, Amsawa tai ta nufi side din Yarima, Kai Tsaye Ta shiga Side din, Bah kowa a falon don Haka Tai knocking a kofar bedroom din, Nanma Shiru, Rakai Minti goma Tana Knocking jin shirun yayi yawa Yasa Ta murda ta shiga da Sallama..

Kwance ta Sameshi shame shame kamar Matacce Yanata Barci, Mamakine Qarara a fuskan Jakadiya, Ta shiga Tashinshi a Hankali tana Kiran sunanshi Yarima! Yarima!! Shiru, Dakyar tasamu ya Bude ido dakyar, Tace "Mai Martaba Nasan Ganinka ranka Ya dade" cikin Muryan Maye Yace "dallah Mallama Getout, Kije Kice Baza'azo bah" da Mamaki Jakadiya Ta Kalleshi Tace "Ranka Ya Dade Lapia?? Ban saba ganinka Cikin Wannan Halin bah" Mikewa Yayi Zaune yana wani lullumshe ido Yace "I Said get out!" alajabi ya hana jakadiya koh motsi. Tunda Take Bata Taba ganin Yarima cikin maye bah Sai Yau, Mikewa Yayi yana tangani Yace "keh wacce irin Tabbace, Fitar min daga Daaaki dallah. Kinbi kin ishhheni da Warrri" ta fita Dasauri ta Nufi fada harda dan gudunta...

Tsugunawa Tai Ta gaida mai Martaba Sannan Tace "Ranka Ya dade bansan Yanda Zaka dau Maganan nan bah Anma...waziri Yayi saurin Katseta da Cewa "Meya faru Jakadiya??" kuka ta Fashe dashi Tace "Yarima Ya jefa kanshi cikin hali irin na Yaran Zamani, Naje dubashi naganshi Cikin Maye yanata Sambatu" Mai martaba Yace "Jakadiya Kin Tabbatar da Abinda kike fada" ta Share kwallan idonta tace "kwarai Ranka Ya dade" Dogarawan Dake Wajan Mai Martaba Ya Kalla Yace "Kuje ku tahomin da Yarima" suka Amsa suka fita dasauri. Sunsha wuya kamin su daukoshi sai sambatu yake, Parveen ta Fito zata Shiga Garden taga an daukoshi Sai Sambatu da Buge buge Yake kamar Mahaukaci, Tai Murmushi Kawai suka hada ido da Altine. Garden din suka shiga Saida Tasamu wuri ta xauna sannan Ta fashe da dariya Harda Kwanciya, Saida Tai Mai Isarta sannan tajawo Wayanta ta Shiga Instagram Tanata Liking post din wayanda Take following cikeda nishadi...

Jakadiya dasauri ta qarasa Sashen Fulani tasanar da ita abinda ke faruwa. Hankali Tashe Itada Umma Sukai Fada, Zaune suka Samu Yarima Sai Sambatu Yake, Takaici Ya hana mai Martaba magana, Fulani ta qarasa kusada Yarima ta tsugunna kusadashi tana Girgiza Shi Tace "Yarima meyasa zakai haka, meh Yasa ka jefa kanka cikin wannan Halin??" kuka take sosai dakyar Umma Tajata Suka bar Wajan...

Mai Martaba Ranshi a bace Yacema dogarawa "ku kaishi ku dauremin shi" waziri yace "Ranka ya dade Aimai afuwa, Muna roqamai Sassauci" baice komai bah suka bar wajan riqe da Yarima, Parveen na xaune akazo aka wuce dashi, Dariya tasaki tareda yin kwafa...

Yarima baisan inda Kanshi Yake bah Sai washe Gari dasafe, Bude ido Yayi ahankali, Ganin Dakin duhu Yasa ya daga kai dakyar, haske ya hango ta Window, Dasauri ya tashi zaune tareda bin dakin da kallo. Mamakine Qarara a fuskarshi, Mai Yakeyi anan dakin?? Kamarshi yarima Fardeen dan Sarki kabeer ya kwana a Magarqama, Dasauri ya miqe ya fara Ihun kiran bayin dake gadin wajan, daya daga Cikinsu Yazi dasauri tareda Rusunnawa, Ya kalleshi da jajayen idonshi
"Meh nakeyi a nan?? Waya kawoni"
Ranka ya dade tun jiya kake nan kuma mai martabane Yasa a kawoka.
Mamaki qarara a fuskarshi, dafe kanshi Yayi dake saramai Sannan Ya dago ya kalli bawan
"Jeka kiramin Bilal"
Tho Ranka ya dade Ya tafi dasauri, Yana Fita daga wajan yayi kicibus da shi a hanya, Bilal ya Kalleshi
"Yariman ya Farka kuwa"
Kwarai ranka ya dade shine ma Yace nazo na kiramai kai.
Ai bai gama Maganan bah ya Nufi Magarqaman Dasauri, Yarima na ganinshi ya qaraso wajan Qarfen daya musu iyaka Yana Kallan Bilal da damuwa
"Bilal meke Faruwa?? What am I doing here"
Ai kai zan tambaya Yarima, Why! Why yarima?? Meyasa zaka jefa kanka cikin Wannan Halin??..

Da Mamaki Yarima Ya kalleshi "Meh kake nufi"
Yanzu Yarima Abin naka ya wuce neman mata Har Shaye Shaye ka fara Why?? Kakosan Yanda mai martaba Yayi Fushi dakai jiya?? Ranshi ya matuqar Baci musamman Sanda Aka kawoka Gabanshi kana maye
Zaro ido Yarima yayi tareda Fadin WHAT?? "What are you trying to tel me Bilal kai kanka Kasan banashan Komai"
Shiru Bilal Yayi Sannan Ya kalleshi
Ina Zuwa insha Allahu Everything wil b olryt. Yabar wajan dasauri. Dukan Qarfen da aka rufeshi dashi Yayi tareda Fadin Daim It!

Muje zuwa...

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
🏀🏀🏀 πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.