A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 23 of 25
Page2β£3β£
A falo suka tarar da yarima kan 1seater fuskan nan yayi jawur, yayi crossibg kafa yanata kad'a na saman Alamar ita yake jira. Atika ta kalla taimata nuni data tafi, bah musu tabar falon. Kauda kai Parveen tai ta nufi dakinta batareda ta kalleshi bah. Tsawa ya daka mata cikin daga murya
"Baki kai bah kinyi kadan, kamar ni yarima fardeen kisa fulani ta kusa Marina. Tashi tsaye Yayi ya qaraso inda take yana kallanta, who du uh tynk uh are?? Answeer mie!"
Kallanshi tai ba Alamr tsoro a idonta
"Ni bah kowa bace, kamar yanda kake ba kowa bah. Ni almajira ce kamar yanda kake almajiri, Haka zalika ni Talakace kamar yanda..."
Saurin katseta yayi cikin daga murya
"Ashe ilimin addinin naki na banza neh tunda baki san Yanda zaki daraja mijinki bah, Duk da kince ni jahili neh a dan a Cikin jahilcin nawa nasan Aljannar nace na qarqashin kafar mijinta, sai ya daga zata shiga"
Dariya Parveen tai sosai tana kallanshi
"Dan Allah idan kaine kesawa a shiga Aljannan idan nazo ka rufe kace ban shiga"
mugun Kallo Yarima yabita dashi
"Banida ikon na hanaki shiga Aljanna idan har Allah ya rubuta hakan, Ya nunata da dan Yatsa. Anma kisani tun daga ranar da aka daura mana aure kike cikin tsinuwar mala'iku, Knan ilimin naki da kike tinqaho dashi na banza neh tunda baki aiki dashi"
Dogon Tsaki Parveen taja ta harareshi tabar falon dsauri zuwa dakinta..
Kwafa Yarima yayi shima ya nufi dakinshi a Fusace. Kwana Parveen tai tana browsing assignment dinta, sai gab da asuba ta gama ta kwanta. Gogan ko Yana dakinshi, juyi yake tayi ya kasa barci, Gashi duk yayi fada da yanmatan nashi. Kuma shi a tsarinshi baya bah Mace haquri saidai ya nemi wata, dakyar Ya samu barci ya daukeshi cikeda Tunanin Rigimarsu da Parveen...
Ana kiran sallah ta tashi ta fada toilet, dan yau karfe bakwai takeda lectures. Wanka tai tareda dauro Alwala ta fito, tana idarwa ko hijabin bata cireba ta fito ta shiga Kicin ta fara Kiciniyar daura Breakfast. Arish ta fere ta Soya, Sannan ta soya kwai. Tana gamawa ta daura ruwan Zafi ta Dama kunnun gyada dan Yau shi take Sha'awan Sha, Tana Gamawa ta jeresu kan dinning ta koma daki ta shirya ta fito. Zama tayi tai breakfast dinta ta gama Sannan tadau jakanta da litatafanta, Har Takai Kofan fita daga falon tajiyo muryan Yarima ta bayanta
"Were du uh think ur Going"
Ba tareda ta kalleshi bah
"School"
Dan murmushin Mugunta Yayi Ya jingina da Bango Yayi folding Hannuwanshi
"Da Izinin Wah??"
Ganin yana neman Bata Mata Lokaci Yasa Ya juyo tana kallanshi
"Da Izinin Mai Martaba"
Daga Gira Yayi Yana Kallanta
"Oh Mai Martaba ke aurenki koh Ni"
Agogon Hannunta ta duba, 6:45am. guntun Tsaki taja
"Mallan ur Wasting my Time, Inada Lectures karfe bakwai"
Dinning ya nufa ya nemi guri ya zauna
"Stop wasting ur time, bah inda zaki Yau. Come and Serve me pls"
Idonta neh Ya Ciko da Kwalla, ta Dake Ta qi koh Motsi. Wayan dake Hannunshi Ya soma Dannawa, Sundau Kusan Minti Biyar a Haka. Chan Ya nisa Yace
"Idan kuma kisano kije ga Hanya nan, Sai kiyi anfani da Ilimin da kikace Kinadashi ki Gani menene hukuncin Macenda Ta fita bada Yardar mijinta bah".
Tsaki Taja Ta nufi dakinta a Fusace
Murmushin Mugunta Yarima Ya Saki Ya fara Serving kanshi...
Kuka Parveen ta Fashe Dashi, Wai mai Yarima ke Qoqarin Maidata neh. Agogo Ta duba Taga karfe bakwai Daidai, Wayan Yasmeen Ta soma Kira Cikin Sa'a kuwa ta Dauka
"Parveen ban Ganki bah, Yanzu na shiga class. Kin yanzu lecturan nan zai shigo"
Jim parveen tai
"Bazan samu zuwa bah yasmeen banda lapia."
"Assignment din fah?? Ko shine kizo kiyi submitting inyaso sai ki koma"
Ajiyan zuciya Parveen tai
"Bazan samu zuwa bah yasmeen, zandai bah drivern dake kawoni sai ku hadu a nan inda yake daukana ki amsa ki tayani submitting pls"
"Bah damuwa. kodai dan babane ke wahalar dake"
Dogon tsaki Parveeb tai, "Allah ya shiryeki Yasmeen"
Bata jira me zatace ba ta kashe kiran.
Wayan danladi driver ta fara nema ta fadamai sakon anma tace ya bari sai kaman karfe takwas yazo. Amsawa yayi ya kashe kiran...
Bakwai da rabi Yarima ya gama shirinshi ya fito dan Zuwa Asibiti. Dakin Parveen ya kalla ya saki Lallausan murmushi tareda Kwafa, Yadau Jakan Laptop dinshi Ya Fita. Dogarinshi Ya gani bakin kofa yana jiransh, dasauri ya rusunna yana kwassan kaisuwa. Kyada kai kawai yarima yayi, dogarin yayi saurin amsar jakanshi ya soma binshi a baya...
Yini Yarima yayi Cikeda tunanin anya Abinda yama Parveen ya dace??
Guntun tsaki yaja a Fili yace
"Wai meyasa nake Yawan tunanin Yarinyan nan??"
Wata Zuciyar Tace
"Santa ka Fara"
Dogon Tsaki Yaja, Daqarfi Ya furta
"God forbid Allah kiyaye. Nadaisan ina Sha'awarta"
Iska ya furzar
Tunanin yanda zai bulloma Parveen ya shiga yi, Yadau kusan minti sha biyar yana abu daya. A hankali ya sauke wani lallausan murmushi ya mike yadau Wasu Files ya fita...
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
*A WANI MASARAUTA*
π€π€π€π
By *Ummy Abduol*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.