A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 21 of 25
Page2β£1β£
"Shiknan Sai Anjima, Ki Aikomin da Assignment din"
Tho Parveen Tace tabar dakin.
Parveen na Fita Ya kalli fulani
"Wai Fulani meh namiki neh?? Yanzu bakya Sona"
Dan Murmushi Fulani Tai Tana Kallan Yarima
"Meh ka gani Kace Haka??"
Turo Baki Yayi baice Komai Bah
Dan Dariya Fulanin Tai
"Yau Yarima Shagwaban Neh Ya Motsa?? Kai Kayi Matarka Tayi"
Hade Rai Yayi
"Fulani Tunda Nai Aure kika Daina Sona meh nai miki??"
Kan Fulanin Tai Magana Sukaji Sallaman Atika, Amsawa Tai Tareda Bata Umarnin Ta Shigo..
Rusunawa Tai Ta Kwashi Gaisuwa Sannan Ta mikama Fulanin Takardan da Parveen Ta Aiko Mata, Amsa tai Atikan Ta mike Tabar Dakin Dasauri. Yarima Fulani ta miqamawa Tana Kallanshi
"Gashi Kaima Parveen Assignment din, Dan Naga Kaman Kunyan Baka Take"
Hade Rai Yayi Ya Amsa Ya aje Gefenshi.
Dan Allah Kai Qoqari ka Mata Wai Jibi Zasuyi Submitting"
Tho Kawai Yace Ya miqe Ya dau Littafin Yamata Sallama Yabar Dakin...
Shinkafa Da Miyan Kaji Parveen Tai, Sai Farfesun Kayan Ciki, Tana Gamawa ta Zuba Na Mai Martaba Taba Atika Takai. Daki Ta koma Tai Sallan Magriba Ta Fito, Abincin Ta zuba Taci Sannan Ta Kofa Falo Ta Zauna Tana Kallo.
Yarima Bai Shigo Gidan bah Sai Bayan Isha, Kan Dinning Ya Zauna Yana Danna Wayanshi. Yi tai Kaman Bata Ganshi Bah Ta Miqe Ta Koma Dakinta. Saida Tai Karatu Sannan Ta Kwanta..
Yarima Koh Barci neh Ya Qauracema Idonshi, Safa Da Marwa Ya Dingayi a Falo, Tunanin Yanda Zai Bulloma Shawaranda Mahdi Ya Bashi Yake, Har wuraren Qarfe Biyu na Dare Yana Kishingide akan Kujera. Qishi neh Ya Tashi Parveen Ta Mike Zaune Tareda Hanma, Tsaki Tai Ta Sauka daga Kan Gadon Ta Fito, Wutan Falon a Kashe, Wutan Kicin ke Dan Hasko Falon, kicin din Ta nufa Tana Miqa Tareda Turo Baki, Fridge ta bude Ta dauko Goran Ruwa guda Daya ta Rufe Fridge din Ta Fito, Wutan kicin din Ta Kashe Ta Fito dan Komawa daki..
Jitai Tayi Karo da Abu, Shafawa Ta soma Yi taji Menene, Alamun Mutum Taji a Tsaye Kam, Aiko Ta koma da Baya dasauri Tareda Kwalla Ihu. Saurin Riqota Yarima Yayi ya Toshe Mata Baki, Bakinshi Yakai Saitin Kunenta
"Keh Nine"
Jin Muryan Yarima Yasa Ta Soma Kici Kicin Kwace Kanta, Qara Qanqameta Yayi a Jikinshi, Tureshi Ta Cigaba dayi da Iya Karfinta Anma Kaman Bata Tureshi.
Lalubanta Ya somayi yana Qoqarin Daga Shimin Dake Jikinta. Wani Qarfi neh Yazo mata Ta Tureshi Da Qarfi Har Saida Yayi Qoqarin Faduwa ta Falla Dagudu Daki, Ita Kanta Batasan Wani Daki Ta Shiga Bah, Key Tasa Ta Koma Dabaya dasauri...
Ganin bah Dakinta Baneh Yasa Taja Tsaki Tana Kallan Kofan
"Allah Ya Isa, Mugu Kawai"
Tsayuwa Tai a Bakin Kofan Na kusan Minti Goma, Barci neh Sosai a Idonta. Har takai bakin Gadon, Taja Tsaki Tana Yamutse Fuska
"Allah Ya kiyaye Nahau Gadon da Aze Zina, Mtcw"
Bakin Kofan Ta Koma tayi kwanciyanta Duk ta Takure Waje Daya..
Yarima Koh Tana Shiga Dakin, Ya Biyota Kamin Yakai har ta Kulle qofan, Naushin Tafin Hannunshi na Hagu Yayi
"Damn It!"
Falon Ya koma Yayi kwanciyarshi, Dakyar Barci Ya Daukeshi..
Kiran Sallah Ya Tayar da Parveen, Ta Mike Dakyar duk Jikinta Ciwo Yake, Rashin Saboda Kwanciyan Qasa. Har Takai Bakin Toilet din Ta Fasa Ta dawo ta Tsaya bakin Kofan, Jin Motsin Yarima Tai ya Bude qofan Falo Alaman Ya tafi Masallaci, Ta Bude Dakin Dasauri Ta fita ta koma Nata dakin ta rufe da Key. Toilet ta Shiga ta dauro Alwala Ta fito, Tana Idarwa Tahau Gado Dan Batasamu Barcin Kirki bah Da Daddare, BaTa Farka Bah Sai Karfe Tara, Dasauri Ta duro daga Kan Gadon Allah Yaso Karfe Goma Yau Takeda Lectures, Falo ta Fito Don Yin Breakfast, Har Tayi Hanyan Kicin Ta Hango Littafinta Databada Akaima Fulani Jiya...
A hankali Ta Qarasa Tadau Littafin Ta bude, Wata Yar Paper Tagani a Ciki Da Rubutu Kai, Kujeran Dinning din Taja Ta Zauna Ta Dau Paper ta Fara Karantawa Kamar Haka:
_Zama Gyne doctor Sai Mai Kwakwalwa Da Hazaqa, Mai Juriya Mara Tsoro. In Banda Rashin Azanci irin naki Ina Keh Ina Zama Gyne Doctor da Wannan Qwaqwalwan naki na Kifi. Kada Ki Taba Tunanin Zaki iya Kamoni Dan Nagaba Yayi Gaba Na Baya Sai Labari. Sannan Karki Taba Tunanin Abinda kikamin jiya da Safe Kinci Bulus, Ina nan Tafe da Nawa Sabon Rashin Mutumcin_
Chan Kasan Papern Aka Rubuta "Dr Fardeen Kabeer"
Dan Murmushi Tai Ta koma Daki Tadauko Biro, Juya Papern Tayi Ta Fara Rubutu...
Don Jin Meh Parveen Zata Rubuta Sai ku Kasance Dani Ummy Abduol Gobe da Safe Insha Allah..
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
*A WANI MASARAUTA*
π€π€π€ π
By *Ummy Abduol*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.