A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 9 of 25
Page9β£
"Wallahi Ranka ya dade bah...bah lefina bneh. Ni...Nima sani akai
Ido Ya zaro waya saki??
Dukar dakai tai sannan tace
"Hadimar Gimbiya Parveen ce"
Damamaki ya Kalleta
"Wato za'a Iya hada baki dake a kasheni a cikin gidan nan koh"
Girgiza kai take tana kuka sosai
Ta window ya leka tareda kiran dogarawanshi dake qofar Falon
Dsauri suka shigo ya umarcesu dasu dauki baiwar su kaita Magarqama..
Suka Amsa ciki na rawa suka dauketa suka fita.
Kan kujera ya Fada Mamaki fal a ranshi, Lallai dan haqin daka raina shike tsole maka ido. Anma yarinyan nan Ta Cuceshi Wallahi
Mikewa Yayi ya nufi side din fulani, Duk yanda yake tunani abin ya wuce haka.
Dakyar ya Samu ya lallabata ta Haqura..
Washe Gari dasafe ya shirya Cikin Kaya na Alfarma ya nufi fada, Yayi Sa'a mai Martaba na nan, Ya shiga da Sallama Tareda Duqawa, Mutanen Gurin Ya gaida sannan Ya soma bah Mai Martaba Haquri, Bah Irin Magiyan da Yarima beyi bah anma sarki kememe Yaqi saima Cewa Yayi ya tashi yabashi waje. Jiki Sabule Ya mike Tabar Fadan. Yana Qoqarin Komawa Side dinsh Yayi kicibus da Parveen dake qoqarin Shiga mota, Mummunan Kallo ya bita dashi ta Dan Dara Sannan Ta shiga mota Drivern yabar Gidan a Guje...
Bilal dayaga duk abinda ya Faru Ya Karaso inda Yarima ke Tsaye
"Wai meye Tsakaninka da Yarinyan nan??, Naga Tana Kallanka tana Dariya"
Wani qayatacen Murmushi Yarima Ya Saki Tareda Shafa Suman kamshi
"Bah Komai"
Cikin Isa Ya fara taku hannunshi daya cikin Aljihunshi Ya Qarasa Side dinshi. Bedroom dinshi ya nufa Ya chanza kayan jikinshi Ya Fito Yana Kallan bilal
"Tashi Ka Rakani muje naga wajanda mai Martaba yace Ana Ginawa"
Kallan Mamaki Bilal Yamai
"Yau kuma??"
Bansan iskanci idan Zaka Rakani kazo ka Rakani.
Bah musu Ya mike Suka Bar Falon..
Yauma Kamar Rannan, Chan bayan Gidan Mai Martaba Sukaje Shida Parveen, Hira Suke Sosai Cikeda Nishadi. Labararaku kala kala Yake bata Tanata Dariya Harda Kyakyatawa. Mai Martaba najin dadin Zama Tareda Parveen Saboda yarinyace Mai Saurin Shiga Rai, Mai Hankali da natsuwa. Shigowan Yarima Knan daga Yawonshi, Fada Ya nufa koh Allah zaisa Yau Mai martaba ya haqura, Dogaran dake wajan suka sanar dashi yana chan bakin ruwa..
Chan ya nufa wit full confidence, tun daga nes ya hango waja zaune duk daukanshi Fulani ce, Ya qarasa wajan da Sallama, Mai Martaba ya daga kai ya kalleshi, Ganin Parveen a wajan Yasa ya tsuke fuska yaji dama baizo bah, gefen qafan mai martaba ya zauna ya gaidashi, Amsawa yayi a takaice, yarima yadan sunnan dakai Ya fara rokan mai martaba, Parveen koh wayanta ta zaro tahau chatn.
Mai martaba rai bace Ya kalleshi
"Tashi kabarmin nan"
Magiya yahau yi, Dakamai tsawa yayi dole ya mike yabar wajan jiki a sabule
Parveen neh ta kalli mai martaba cikeda ladabi
"Dan Allah Ranka ya dade kamai Afuwa, Idan Har ya sake sai kadau hukuncin da duk ya dace"
Dan Murmushi yayi
"Shiknan Parveen"
Dogarin dake gefensu mai martaba yasa ya kiramai Yarima wanda har yayi nisa ya kusa barin wajan
Chan sai gashi ya dawo ya zauna, Mai martaba Ya kalleshi dakyau da kauda kai
"Kaci darajan Parveen ta Roka na yafemaka anma idan bah haka bah, bah Yanda za'ai na sauko yanzu"
Godiya yama mai martaban Ya mike Suka hada ido da Parveen, Harara ta sakar mishi Yaja guntun Tsaki mara sauti Yabar Wajan Fuuu..
Side din Fulani ya nufa, Baiko sa amai iso bah ya shiga kai Tsaye, Zaune take kan Darduma tana lazimi, ya Qarasa ciki tareda neman wajan zama. Saida ta Gama Sannan Ta kalleshi
"lapia?? Meh kuma kakeso??"
Furzar da iska yayi rai bace
"Fulani I hate dat girl pls ta koma Garinsu, Banasanta! Banasanta!! I hate her!"
Dam! Gaban fulani ya fadi, ta dake Tana kallanshi
"Saboda meh??"
Wai yanzu fisabilillahi fulani inata Rokan mai martaba akan yamin afuwa anma yaqi, wai saida wannan wawiyar Yarinyan tace Sannan"
Dan Murmushi fulani tai tana Kallanshi
"Duk Abinda ya faru ai kai Kaja, bakaji masu iya magana nacewa wani lokaci da dan uwa gwara bare bah. Ai duk abinda kagani yanxu kai ka saya da kudinka. Sannan kasha kurumin kah indai Parveen ceh nanda kwana biyu zata bar gidan, Zata Koma garinsu"
Mikewa Yayi yace "Dayafi Mata"
Barin dakin Yayi yadau waya ya kira Mahdi, Bugu daya ya dauka, Yarima yadanyi jim har saida Yace "Yarima kanajina"
"Kazo gida inasan Ganinka Pls"
Tho Mahdi Yace tareda kashe wajan. Ba'adau lokaci mai tsawo bah saiga shi. Direct Side din ya nufa, Falon ya shiga ya tarar da Yarima zaune yayi crossing leg sai jijiga nasaman yake.
Mahdi ysamu guri ya zauna, Shiru ne ya ratsa Falon, Chan Yarima Ya dago Tana Kallanshi
"I Hope kasan Wata yarinya yar Gidan Sarki Khaleed na Kasar Zaria koh"
Shiru Mahdi yayi nadan sakanni Sannan Ya dago
"Yes! Gimbiya Parveen koh??. Wata Kyakyawa, Kamar Rannan danazo gidan nan naganta. Kai Babyn ta hadu bah karya kaga m....
Saurin Katseshi Yarima yayi da Tsawa.
"Shut Up dallah"
Labarin Zuwanta yahau bah Mahdi har zuwa sanda Tamai Abin nan
Mamaki qarara a fuskan Mahdi..
"Ka Tsaya Kana Kallona kaman tv, Mafita nake nema, jibi zata tafi, Inaso nai mata wani abu wanda harta mutu bazata mantani bah
Dan dariya Mahdi yayi yace
"Indai wannan neh tazo gidan sauqi"
Muje zuwa..
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
*A WANI MASARAUTA*
π€π€π€ π
By *Ummy Abduol*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.