Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 24 of 25

Page2⃣4⃣

A Hankali ya sauke wani lallaudan murmushi ya mike yadau wasu files ya fita.
Yarima na fita parveen taima danladi waya yazo ya amsa sakon ya yafi. Kwanciya tai barci ya dauketa dan dama da daddare batasamu barcin kirki bah. Bata tashi ba sai wuraren karfe daya da kusan rabi, Tashi tayi ta fada toilet tai alwala ta Fito. Tana idar da Sallah ta jiyo knocking a kofar Falo, Ta tashi ta fito ta bude. Ihu parveen ta saki Cikeda murna.
dasauri Deeza ta qarso tareda rungume parveen
"Deeza Wannan Suprise??"
Dariya deeza tai Tana Kallan Parveen
Hannunta ta kama suka shiga Ciki, Kan kujera suka baje Parveen na cigaba da mamakin Ziyaran bazatan da Deeza ta kawo mata..

"Bae na dauka zanzo na sameki Kina Amai ai"
Dukan wasa Parveen ta kaimata
"Allah ya kiyaye, keh kina tunanin zan haihu da Yarima neh??"
Girgiza mata kai deeza tai
"Bai kamata kina irin furucin nan ba bae, komin lalacewarshi mijinki neh. Yakamata ki rinka furuci masu kyau akanshi"
Dogon tsaki Parveen tai ta yamutse fuska tareda kauda kai
"Deexa knan, koh kinsan Yarima har neman mata ya..."
Saurin rufe mata baki deeza tai tana Girgiza mata kai
"Sirrinki neh parveen bai kamata kina gayama kowa bah. Nifa laifinki nake gani bae"
Kallanta tai da mamaki
"Kamar ya??"
Gyada kai tayi tana cigaba da kallanta
"Kwarai kuwa, haba bae sai kace ba mace bah. Keh zaki sa ya daina neman mata, look lemme tl uh zaki iya juyashi yanda kikeso kece dai in baki so bah"
Murmushin takaici Parveen tai tadau jakan deeza tana cewa
"I hope wata zakimin"
Bude baki tai da mamaki
"Wata?? Haba dai sai kace mara hankali. Jibi ran sunday insha Allah zan koma"
Tsuke fuska parveen tai
"Haba wasa kike yarinya. Tashi mu shiga Ciki"
Sun dade suna hira har akai Sallan la'asar sannan suka shiga kicin dan daura girki. Suna girkin take bah deeza labarin hanata zuwa schl dinda yarima yayi...

Dariya kawai deeza tai batace komai bah, har abin yaso bah Parveen haushi.
Bayan magrib Yarima ya shigo gidan, Lokacin sun zaune kan dinning suna cin abinci, Jin hayaniya yasa ya qaraso wajan dinning din da sallam, Deeza ce ta amsa tareda gaidashi. Da fara'a ya amsa tareda tambayanta tazo lapia, Ta amsa da lapia lau. Dakinshi ya wuce kai Tsaye. Deeza ta kalleta
"Ya dawo baki kai mai abinci bah"
Tsaki parveen tai ta cigaba dacin Abincinta
"Keh fa matsalata dake knan bae, Bai kamata bah abinda kikeyi. Kada ki biye halinshi ko kin manta maganan da mukai dazu"
Mikewa deezan tai ta shiga kicin ta hado abinci a tray ta ajema parveen a gabanta
"Pls tashi ki kai mai"
Turo baki tayi
"Nifa indai abinda ya kawoki knan gwara gobe da sassafe ki kom gida. Nifa da kika gani bana shiga dakinshi, yanzu idan nakaimai saiya raina ni"
Kafadanta ta dafa
"Bah wani raini bae, Kiyi qoqari ki gyarashi zaki samu lada, ina miki kwadayin ladan da zaki samu nan gaba neh"..

Turo baki parveen tai ta mike tareda daukan Trayn har ta doshi dakin deeza tace
"Ki Tambayeshi akan maganan zuwa gaida fulanin"
Batace komai bah ta qarasa dakin, Bata tsaya knocking ba ta tura qofan ta shiga kai Tsaye. Har ya zame towel dinda ke Jikinshi yana qoqarin sa Kaya ta shigo, Ihu ta Saki Tareda rufe idonta, ta saki trayn ta fita dsauri. Dariya Sosai ta bashi, Kayan Ya qarasa sawa Ya zauna bakin Gadon Yana cigaba da dariya..

Qanqame Deeza tai idonta a rude tana ihu, rufe mata bakin tai Tana jijigata
"What?? Menene??"
Sakin ta tayi ta ruga daki dagudu. Girgiza kai Kawai tayi ta zauna tacigaba dacin abincinta. Gado parveen ta fada tana maida numfashi, Ganin Surar Yarima tayi cikin idonta. Dasauri ta qara rufe ido tana Turo baki. A Hankali ta furta
"Allah ya isa ban yafe bah"
Kwanciyanta tayi tana chating har deeza ta shigo.
"Wai wane irin abu wannan parveen??"
Tashi tayi ta zauna tareda hade rai

"Allah ya isa deeza, kin cuceni Wallahi. Gashi kinsa naje..kasa qarasawa tai ta ja tsaki"
"Nidai yanzu kin tambayeshi maganan Zuwa gaida Fulanin"
"Nifah karki dameni deeza, bazan koma dakin nan bah" cewar Parveen
Tsaki deeza taja ta mike
"Natafi Kallan Players a bollywood"
Wup Parveen ta tashi tana washe baki
"dan Allah dagaske??"
Batace mata komai bah ta bar dakin, itama binta tayi zuwa Falon.

Zama sukai suka soma kallo bah wanda ya qara cewa kowa komai, chan sukaji bude kofar dakinshi, ya fito ya qaraso falon. Parveen ya kalla Fuskan nan a daure
"Hu wil clean up dah mess"
Tsaki taja ta mike dan tasan zai iya dizgata a gaban deeza.
Dakin ta shiga ta soma tattara wajan, tana gamawa ta dawo ta tarar dashi zaune a falon sunata hira da deeza kamar dama sunsan juna.
Guntun tsaki taja tana kallan deeza
"Ni natafi na kwanta"
juyowa tai tana kallanta
"Bazaki tsaya ki qarasa kallan bah??"
Girgiza kai tayi alamar Aa
Harta juya taji muryan Yarima yana cewa
"Tashi to kuzo muje ki gaida fulanin sai naraka ki koh"
Parveen ta qarasa daki ta zauna bakin gado, deeza ta shigo tana kallanta

"Tashi muje pls ya rakamu, kinga ma dare ya soma"
Dakyar ta lallaba parveen ta mike tasa hijabi suka fito. A hanya Deeza da Yarima sai hiransu suke parveen ko ta hade rai tana bayansu suna gaba.. Tare suka shiga side din da yarima, deeza da parveen suka zauna kan Carpet tareda gaida Fulani, Parveen ke fadama Fulani wacece Deeza a wajanta. Ta Taresu dakyau sun dade suna yarima ya fito falo ya zauna yana kallan news, Sai wuraren sha daya suka baro Side din, Kamar dazu hiransu sukaitayi suka barta a baya, Haushi abin ya bata sosai. Koda suka qarasa side din ko inda deeza take bata kalla bah ta wuce daki fuuu..

Tho fah kodai Parveen kishi takeπŸ€”??

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.