Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 25

Page1⃣0⃣

Labarin Zuwanta Yahau bah mahdi har zuwa sanda Tamai Abin nan Mamaki Qarara a Fuskan Mahdi...
"Ka Tsaya Kana Kallona Kaman Tv, Mafita nake nema. Jibi zata tafi, Inaso nai mata Wani Abu wanda Harta mutu bazata Mantani bah
Dan Dariya Mahdi yayi yace
"Indai wannan neh tazo gidan sauqi"
Da Mamaki Yarima ya Kalleshi
"Kamar Yha Meh kake nufi??"
Dan murmusawa Mahdi yayi Sannan Ya kalleshi
"Haba Yarima Sai kace baka waye bah??. Har kamar yarinyan nan zataima Wannan Rashin Mutumcin ka Kasa daukan mataki?"
Tsaki Yarima Yaja
"Kawai ka fadamin meh za'ayi Ynxu"
Qara murmushi Yayi
"A Nawa tunanin Kawai ka Aureta, Ka Maida Ita Sex Machine dnka Kawai Sannan a Gefe Kaita Gana mata Azaba. Kaga dai bah Halin...
Saurin Katseshi Yarima Yayi ta hanyar Dagamai Hannu

Kaifa Banza neh Mahdi, Kai Kanka Kasan Banida Ra'ayin Aure Ynzu. Idan ma Inadash bah Wannan Stupid Gurl din bah, Naushin Hannun kujeran dayake kai Yayi
"I Hateeee Her Wallahi"
Mahdi yadan dara Sannan Yace
"A nawa Tunanin Wannan neh kawai mafita, Buh ka tsaya kai tunani Akai. Kaga Idan kai Kama daina Neman Matan nan dakake"
Yarima baice komai bah, Yadan Zame daga Zaunen dayake Tareda Lumshe ido
Mahdi Ya Mike tareda Farin
" Ni Natafi, Inada Uzuri Yanzu"
Kai Kawai Yarima Ya gyada mai Ya Fita...

Yini Yayi yana Saqawa da kwancewa, Anya Zai iya Auren Parveen?? Lokaci Lokaci Yakanja Tsaki
"Ni Ban Shirya Aure bah, Am just 26 fah"
Idan kuma Ya tuna da Dalilin auren saiyaji Zuciyarsh Ta aminta da Hakan.
Haka Ya Cinye kwanaki Biyun nan Cikin Tunanin Mafita..

Fulani da Mai Martaba Sun Wayi Gari Yau ransu bah Dadi, Kasancewar Parveen zata Koma, Ita Kanta Sai Taji Batasan komawan. Anma bah yanda Zatai saboda Makaranta. Altine che Ta shirya mata Kayanta Tareda Sawa amota, sun Fito don Tafiya, mai Martaba Harda Fulani suka Fito don rakasu, Kallan Fulani tai Wanda duk Ranta bah dadi, Ta juya Ta kalli Mai Martaba, Kawai Saita Fashe da Kuka...

Fulani ta Qarasa ta Rungumeta Tana Lallashinta, Magana take Mata a kunni wanda ni kaina bansan meh take ceh mata bah, Saidai naga Ta daina kukan tana dan Murmushi, Fulani ta Share Mata Hawaye Sannan Suka Dunguma Zuwa Airport. Kyauta Sosai Mai Martaba Yama Parveen har Tana Mamaki Saboda Yawanshi, Sallama Tai Musu Suka Hau Jirgi tana dagama Mai Martaba da Fulani hannu, Suma Hannun Suke daga Mata. Hawayene ya Gangaro mata, Tasa Hannunta na Hagu ta share Ta Shige Cikin Jirgin don inta Tsaya Kallansu Zata iya Fashewa da Kuka...

Cikin Awan da bai wuce daya bah suka iso masarautar zaria, Already dogarai tareda bayin umma suna jiransu, Jirginsu na sauka suka Fito tareda shiga motan da aka tanadar musu zuwa gida. Sai Taji dama bata dawoba, ranta bah dadi har suka Qarasa Gda..

Umma Daketa Hidima dan Jiran Yar nata taji Shigowan motoci, Mikewa Tai Dasauri Umma Ta nufi wajan cikeda Farinciki, Kuyanginta neh Suke Take mata baya, Har sun kai Bakin Qofan Fita side din Umma, Sukai Kicibus da Parveen dake Qoqarin Shigowa Side din. Parveenta qarasa dasauri ta rungume umman nata tana dan dariya, Umma Cikeda farinciki Tai mata Sannu Suka qarasa cikin side din. Sun baje Anata Hira, Sunci Sunsha, Parveen ta nunama Umma kyaututukan da Mai Martaba Yamata, Godiya sosai Umma tai Tareda Farinciki...

Saida ta huta Sannan Ta nufi Side din Mai Martaba bayan tasa Jakadiya tai mata Iso. Mai Martaba na ganinta ya Mike Cireda Fara'a Tareda bude Hannu, Dasauri ta qarasa ta rungume mahaifinta, Kanta ya shafa Yana mata Sannu da Dawowa. Dan dagowa tai ta Kalleshi
"I Missed uh dad"
Murmushi Yayi Shima yana Kallanta
"I Missed uh My Princess"
Dariya tasaki Ta zame jikinta daga nashi ta nemi guri kan Carpet ta zauna
Hira suke Sosai Ya Tambayeta Fulani da Mai Martaba, Kyautan da mai Martaba Ya mata Ta fadama Mhaifinta. Yayi Murmushi
"Ai sarki Kabeer Akwai Mutumci da datako"
Itama murmushin Tai tanata bah shi Labarin Yanda Mai Martaba da Fulani ke Santa, Batabar Side din mai martaba bah saida aka kira Sallan Magriba Sannan..

*Bayan Sati Biyu*
An Kammala Ginin Asibitin Yarima Budewa kawai Ya Rage, Sam Ran Yarima Baiso Hakan Bah, Anma bah Yanda zeyi dole Yayima Mahaifinshi biyaiya...Harynzu ya kasa Haqura Akan Abinda parveen Tamai, Dole Yadau Mataki. Dole Ya Rama, Saiya nuna mata Shi yarima fardeen neh kuma ya haifu, Sun Zauna shida Mahdi Abokinshi, Qara nusar Dashi Lalillin Hakan Mahdi Yayi yar Ya Yarda. Sun Yanke Shawaran duk Yanda Za'ayi, Yarima Ya Saki Lallausan Murmushi Sannan ya Kalli Mahdi
"Kwanyanka naja Frnd"
Shima Mahdin Dariyan yayi...

Hadadden Motarda Mai martaba Ya siyan mata Qirar Dodge Ta nufa Dasauri Hannunta rataye da jakan Laptop, Sai Keyn motanta, Motan Ta Shiga Ta Fita Daga Gidan Dasauri. Gudu Take dan Takusa Yin Latti, Ahmadu bello University naga ta nufa dasaurinta, Horn taketa ma Student din Demostration da Sukai Cincirindo a gate sun shiga. Tsaki taja ta Qara danna Horn, Agogon Hannunta ta duba taga 7:56am Gashi 8:00am Takeda Lectures kuma Tasan Lecturan baida mutumci. Dakyar tasamu Ta wuce ta nufi depertment dinsu, Cikin ikon Allah tasamu ta shiga hall din, tana shiga lecturan ya shigo. Saida Tagama Sannan ta fito Tai Kicibus da Aminiyanta...

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
*A WANI MASARAUTA*
🏀🏀🏀 πŸ‘‘

By *Ummy Abduol*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.