Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 25

Page2⃣

Haka Parveen tabar dakin mahaifinta jiki bah kwari, koda ta isa dakinta hana kowacce baiwa ta shigo mata tai. Dakanta ta hada kayanta da duk wani abu datake buqata duk da tasan chan kamar a gida take, dakyar barci barawo ya kwasheta a daran..
Washe gari wuraren karfe Shadaya jirginsu ya tashi zuwa garin gombe, Koda suka isa sun samu mutanen mai martaba na jiransu, dan haka jirginsu na sauka suka shiga motoccinda aka tanadan musu tareda yan rakiyansu zuwa gidan Sarkin Gombe..

Fulani sai shige da fice take kamar bah matar sarki bah, cikin mintina kadan aka gyara mah Parveen dakinda zata zauna Tareda haka kalolin Abinci iri iri, yau Fulani cike take da Farinciki yarta zatazo, tana daki zaune Fardeen yayi Sallama ya shigo, amsawa tai tareda dagowa ta kalleshi, yadanyi murmushi Yace "Fulani wai sarki Salman na Qasar Saudi Arabia neh zaizo ko ko Obama??" naga Sai rawar Jiki Ma'aikatan gidan nan keyi, naga Mai Martaba Sai Fara'a yake, gashi kema nazo nasameki. Murmushi tai Sannan Tace "Yarima knan, Sarki Khaleed neh Tareda Yarshi ke Tafe inaga ma yanzu suna Cikin Garin nan Qarasowa kawai ya Rage, Yadan Yatsine Fuska Sannan Yace "badai Wannan Yarinyan Tashi bah Mara kunya n I hope Bah zama Tazoyi bah" Hade rai Fulani Tai zatai Magana sukaji Horn din motoci, Dasauri Ta mike Tafito daga dakin, Bayinta dake take mata baya suka rusuna suka gaisheta Sannan suka Soma binta a baya...

Futowan Fulani daidai da Fitowan Parveen daga mota, dagudu ta Qarasa tareda Rungumeta, cikeda Farinciki Fulani Tace "Barka da zuwa Yata" Bayin dake Wajan suka zube dan diban Gaisuwa, Parveen ta Yatsine Fuska tace "Ni Fulani banaso bayi na duqamin pls kice su daina" Dan Dariya Fulanin Tai Sannan Tace "Har yanzu dai kina nan da Halinki, Wannan Shine Ikon ai" Hannunta ta Kama sukai side dinta Cikeda Farinciki..

Sarki Khaleed ya Shiga fada Cikeda Farinciki, dasauri Mai Martaba Ya mike sukai Musabaha tareda Rungume juna, Sarki Alameen Yayi Matukar Farinciki da Ganin Abokin nashi, sun Zauna a Fada, Dakatai, Masu Anguwanni, da Sauran Masu Muqamai na Sarauta nata Kawo Gaisuwa, Sai Bayan Sallan La'asar Sannan Suka Samu kebewa a Side din Mai Martaba. Suna Cikin Hiran Bayan Rabo Yarima Fardeen Yayi Sallama Ya Shigo tareda Rakiyan Abokinshi Adnan da fadawanshi, Zama Sukai Kan Carpet din Falon Sannan Suka Soma Gaida Sarki, Sarki Khaleed Ya kalli Yarima Cikeda Kulawa Yace "Yarima an Girma Ya Karatu??? Ka Kammala neh?" kai Ya gyada Sannan Yace "Angama Ranka ya Dade", Sarki Khaleed Yashafa Kanshi Yace "Allah yamaka Albarka" Yarima Ya amsa da Ameen Sannan Suka Mike Suka Bar Falon...

Side din Yarima Suka nufa shida Abokinshi, har sunkai Bakin Kofan Ya Daga Hannu Batare daya Juyoba Fadawan dake Take musu baya suka Bar wajan Dasauri, Adnan Ya bude kofan Suka Shiga. Kan Three seater Ya Fada Tareda Sakin Wani dogon Tsaki, Adnan Yakalleshi Cikeda Mamaki Yace "Deen Yadai Whts Wrong?" tsakin Yakuma Ja Sannan Yace "Wallahi Mai Martaba neh Waishi dole sai nayi aiki a Nigeria nikuma Sam Banasan Zaman Kasan nan" adnan Yadan nisa Sannan Yace "Buh Yarima Yan Kasan nan nabuqatanka matuqa, Suna neman kwararun Likitoci Kamarka, Shiyasa Zakaga Mutane na fita Qasashen Qetare Ganin likita. Kuma Bawai dan Fararen sun Fimu baneh Aa! Zakaga Yawanci mah Baqaqen Fatan neh Anan tho.... Saurin Katseshi yayi ta hanyar dagamai Hannu, Dasauri Yayi Shiru, ya Mike Sannan Yace "pls katashi kaban waje I need privacy" Mikewa Adnan Yayi dasauri dan Yasan Halin Abokin nashi Yamai Sallama Ya bar Side din...

A Dakin Fulani Suka Yada Zango itada Yar nata, Hadimai Sai Hidima suke da Parveen kamar zasu hadiyeta, Hira Suke Sosai Cikeda Farinciki, Sunci sunsha Sannan Jakadiya ta nunama Parveen Dakinta Sannan ta Nunama Altine Nata dakin..Kwanan Sarki Khaleed biyu Ya Koma..

*Bayan Kwana Biyu*

Cikin Sauri Yarima Yafito fadawanshi na takemai baya, hannunshi Riqe da Agogo yana qoqarin Daurawa, Daidai Nan Parveen Tafito daga dakinta Cikeda Farinciki Tana Waya da Ummanta, Hankalinta Sam baikai kanshibah, Shima haka. Jitai Tayi karo da mutum Ta dago Zara xaran idanunta dasauri suka hada ido, Hade Rai Tai, Hadiye Yawu tai dakyar Da Qarfin hali Tace "Haba Mallan baka Gani neh" da Mamaki Yarima Ya Kalleta Yace....

Ummy Abduol✍🏻
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ‘‘
A WANI MASARAUTA
🏀🏀🏀 πŸ‘‘

By Ummy Abduol

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.