A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 25
Page1β£8β£
Tana Zama kan Dinning din Taji An Bude Wani qofa Daga Gefenta, Kai Ta Daga Cikeda Tsoro dan A Tunaninta ita kadaice Ta kwana a gidan. Wata Kyakyawar Yarinya ta gani Ta Fito Sanye da Wani Matsatsen Wando da Riga, Kafanta Sanye da Dogon Takalmi, Kan nan Yasha Attachment. Ko inda Parveen Take Bata Kalla Bah Tai Hanyar Kofan Falon, Juyawa Parveen Tai Cikeda Mamaki, daidai Nan Yarima ya fito Sanye da Brown Jallabiya, Bai ko Kalli Parveen Bah Ya Riqema Yarinyan Hannu suka Fita Daga Falon..
Mamaki neh Kwance Kan Fuskan Parveen, Tunani ta Soma, dama Yarima Na neman mata meh?? Wata zuciyar Tace
"Ina Ruwanki da neman Matanshi"
Tsaki Taja Ta Soma Zuba abincinta, saida Taci Ta qoshi Sannan Tadauke Plate din Takai Kicin Ta koma Daki. Wanka Ta sake Ta Shirya Cikin Pink and Purple Atamfa, Simple Make up tayi tasa Mayafi Pink, Tadau Flat Shoe Shima Pink Tasa. Wayanta ta Dauka Ta Fito Falo, Tana Qofarin Bude qofan Falon Aka Bude. Yarima Neh, Yana Ganinta Ya Hade rai, Itama hade Ran Tai TaKauda kai, ta gefenta Yabi Ya Wuce ya Shige Dakinsa. Tsaki tai Ta Fita Ta nufi Side din Fulani..
Fulani na Ganinta ta Tareta da Murna, Har Kasa Ta Tsugunna Ta Gaida Fulani, Ta Amsa Fuska A Sake Tana Fara'a. Parveen Tsintan Kanta Tai da Jin Kunyan Fulani, Lura da Hakan Yasa Fulani Tace
"Amarya kinsha Kanshi"
Sadda kai Parveen tai tana dan Dariya
"Bai Kamata Ki Fara Fita Tun Yanzu bah, ki Bari idan kikai Sati daya Saiki Fita. Sannan Maganan Makaranta Mun Gama Magana Da Mai Martaba nan da Sati Biyu saiki Fara"
Dagowa Parveen Tai Fara'a Kwance Akan Fuskanta
"Nagode Allah Ya Qara Girma"
Fulani ta Amsa da Ameen
Mikewa Parveen tai tace
"Na Barki Lapia"
Fulani Cikeda Sigan Wasa tace
"A Gaidamin da Ango"
Murmushi Parveen Tai Tabar Dakin..
Koda Ta koma Yanda Tabar Abincin Haka Tadawo tasameshi, Tsaki Tai ta Kwashe Kwanukan Takai Kicin. Daki ta Koma Tai Kwanciyarta Tareda Jawo Wayanta, Numbern Umma Ta kira, Yana Fara Ringing ta dauka. Ajiyan Zuciya Parveen Tai Sannan Tace
"Barka da Safiya Umma"
Umma Cikeda Murna Tace
"Parveen kin Tashi Lapia? Ya Kwanan Ango?"
Jim Parveen Tai Sannan Tace
"Yana Lapia lau"
Tho Madallah
"Umma Ya Mai Martaba??"
"Yana Lapia Lau, Dazu koh muka Gama Maganan ki"
Murmushi Tai "Ina Gaidashi"
Insha Allahu Zaiji..Kashe Wayan Umma Tai, Parveeb Tabi wayan da Kallo. Tayi Missing din Ummanta, Nan da Nan Hawaye Suka Fara zuba A Idonta...
Kwanciya Tai Ta Lumshe Idonta, A Haka Barci Ya dauketa Cikeda Kewan Gida..
Haka Suka dau Tsawan Sati, Kullum Sai yarima Ya kawo Yanmatan shi. Sam Parveen Hakan Bai Damunta, Tunda Tazo gidan Magana bai Taba Hadasu dashi bah. Ita Hakan mah Yafi mata.. Ranar da Takai Sati Daya Fulani ta Umarceta data Fara Girki..Da Yanma Ta Daura Tuwon Shinkafa Miyan Ugu, Kasancewar Komai Na Dangane da Kayan Miya Akwai a Cikin Kicin din..
Nan da Nan gidan ya Gauraye da Kamshi, Saida Ta Gama Komai Ta zuba a flask Ta Kawo Dinning, Mai Martaba ta Zubamawa a Wasu Hadaddun Kuloli. Baiwar dake Taimaka Mata da Goge Goge Taba Takai Ita kuma Ta Koma Dakinta dan Watsa Ruwa...
Watsa Ruwa Tai Ta Fito Daure da Towel a Kirjinta, Sai Qarami datake Tsane Ruwan Kanta, zama Tai kan Stool din Mirrow Tana Cigaba da tsane Kan nata. Saida Ta Gama ta dago ta Kalli kanta a Mirrown, Ganin Mutum kawai tai Kan gado Yana Kallanta, Dasauri ta mike Tareda Kwalla ihu. Saura Kadan Towel dinda ke Kirjinta ya Fadi, Sam batama Lura da Waye bah Tabar dakin a Guje. Baiwarta Atika Taci Karo da Ita, atika ta Kalleta Hankali Tashe
"Lapia Ranki Ya dade Maiya Faru??"
Dakinta Ta Fara nunama Atika a Rude
Har atika ta Nufi dakin Taga Yarima Ya Fito Hannunshi daya Cikin Aljihunshi, Fuskan nan Daure Tamau. Barin wajan Atika tai Kanta a Qasa Kamar munafuka...
Sai a Sannan Parveen Tasan Yarima Neh, Dogon Tsaki Taja Tareda Kauda kai Gefe. Dariya yarima Yaso yi anma Ya Dake, Shima Tsakin Yayi yabar Falon Zuwa Dakinshi
"Anma Allah ya Isa, Mutum Yayita Abu kamar bah musulmi bah"
Dakinta ta koma Ta Shirya Sannan Ta Fito. Kan Dinning Ta Sameshi Yana Daddana Wayanshi, Guntun Tsaki Taja Ta Qarasa Wajan Tahau Zubamai Abincin...
Malmala Hudu tasamai Gasu Manya Sannan Ta Zuba mai Miya a Dayan Plate din, Kallanta kawai Yarima Yake Da Mamaki, Tana Gamawa Ta juya Zata Bar wajan, Tsawa Ya Daka Mata,
"Ke Dabban inace da Bakisan Yanda Ake Serving Mutane Bah. Wannan Abincin Suwa kika zubama Wah?? Koh kin dauka ni kece da Baki Saba Cin Abinci bah".
Saurin Katseshi Tai Rai Bace
"Karka Qara Kirana Dabba, Tunda Baka Ganni da Jela Bah Balle Qaho, Kai Yakamata Ka Kira Kanka Dabba Kaida Bakasan Darajan dan Adam bah. Kai kanka Kasan Nafi Qarfin Abinci, Koh Ka manta daga Gidan da Nafito neh."
Qarasa maganan Tai Rai Bace
"Kai Qoqari ka Koma Islamiya dan Har Yanzu Jahilci na Dawainiya dakai!"
Wani Kukan Kura Yarima Yayi Ya Mike ...
Tho Fah??..
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
*A WANI MASARAUTA*
π€π€π€ π
By *Ummy Abduol*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.