A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 25
Page5β£
Dare Ya tsalla, Duhu ya mamaye bah Abinda kake gani sai Hasken Fitulu ko ina. Masu iya magana kance Dare mahutar bawa. Duk mai Rai yana Barci a wannan lokacin, Parveen na hango tsaye a dakinta Sai safa da marwa take, A hankali na qarasa dakin don in tabbatar da abinda idona ke nunamin, hawaye ne chabe Chabe a idonta, lokaci bayan lokaci takan zauna tareda Fashewa da wani sabon kukan, Dakyar ta kwanta badan tasamu mafita bah, Saidai tuna idan tacigaba a haka batai barci bah zata cutu, dakyar bacci barawo ya saceta duk da bah baccin dadi bneh...
Fardeen Kwance Kan makeken Gadonshi, daga gefenshi wani Kyakyawar Yarinya cikin bargo sai sheka Barcinta take, Dan Tsaki yayi lokacinda ya juya ya kalleta, Ya mike Ya shiga toilet, Wanka yayi ya fito ya zauna, Abinda yafaru dazu ya tuna, Ya saki Qayataccen Murmushi, lokaci guda ya hade rai tuna abinda yagani dazu, A hankali ya furta "I have to do something" tsaki yaja ya mike Yasa kayan barcinshi Ya koma Falo dan bazai iya kwantawa akan gadonba kuma...
Dasassafe ya Shirya cikin Kayan motsa jiki, yana fitowa suka hade da bilal shima cikin shiri, Bilal yadanyi dariya Yace "dama nasani banzo bah najira kabiyomin" hararanshi yayi yace "kataba ganin nabiyama wani" wani dariyan ya saki yace "Aa ban taba gani bah, Anma ka kusa" Tsaki Yarima yaja Yace "Dallah mutafi dan indai kaine sai akai gobe kana zuba", Gum Bilal yayi suka nifi gym dinda keh gidan, Wai! Nayi Matukar mamaki yanda naga Yarima na daukan Qarfe, A raina nace Lallai dama haka yakeda Qarfi, labewa nai inata kallansu har suka gama. Wani bawa na riqe da towel dinshi yana tafiya cikin isa dan qarasawa side dinshi, Daidai nan Parveen ta fito Daga side dinta cikin Kaya na Alfarma Altine natake mata baya, Koh Kallanshi Bataita haka shima har suka qarasa side din Fulani. Da Sallama ta shiga dakin sannan tama Altine alaman ta tsaya, Fulani dake kishingide jakadiya na gefenta ta amsa Fuskarta dauke da murmushi, Wuri tasamu ta zauna Tareda Gaida Fulani cikeda ladabi, Fulani ta amsa Fuska a sake..
Jakadiya tai Saurin Gaidata Sannan ta mike Tabar dakin, Shiru neh ya ratsa dakin, Chan Tai Qarfin Halin Cewa "Fulani dama inaso nakoma Qasarmu neh" Mamakine Qarara a Fuskan Fulani, Ta mike Yazauna Tareda Kallanta Tace "Saboda meh Parveen?? Koh Wani ya bata miki Rai neh?? Dan Allah ki Fadamin, kwananki Fah uku knan shine Har zaki tafi" Shiru tai kanta na Qasa. Fulani Cikeda damuwa tace "koh Umman nakine Tace kidawo??" Girgiza kai tai Alamar Aa, Fulani tamike tadawo kusada ita ta zauna tace "Fadamin Parveen meh ya faru meh aka miki" bude baki tai zatai magana anma ta kasa saima fashewa da kuka datai, A hankali tace "Ina kewar Umma neh" Murmushi Fulani tai tace "Allah ya shiryeki Parveen" dakyar ta lallasheta tai Shiru suka cigaba da hira anma Har lokacin bata saki jiki bah...
Mai martaba zaune shida mutanen Fada, Yarima neh Ya shigo da Sallama tareda Rakiyan Bilal, Guri suka samu suka xauna tareda gaida Sarki da mutan Fada, Sarki Ya Kalli Yarima Yace "Maganar Ginin Asibitin danama Alqawari Ya tabbata, Yanzu Haka an Fara Gini dan Haka saika zama Cikin Shiri Saboda kasan Bazai dau lokaci bah, Sannan Abu na biyu ina Fata mahaifiyarka tama bayani??" girgiza kai Yayi Alamar Aa! Cikin isa mai martaba Yace "Kaje Wajanta zataima bayani" Ya Mike sukai musu sallama Suka nufi side din fulani, Bilal sai tsokanarshi Yake yana Kiranshi "Dah Proffesional Doctor" Yarima koh Sai hade Rai yake.
Fulani ita kadaice Zaune Sai Hadimanta daketa kaiwa da komawa, Bilal neh Yayi Sallama Ta amsa suka Shiga, Har Qasa Ya Tsugunna Ya gaida Fulani, Ta Amsa cikeda kulawa. Yarima koh kan 1seatern dake gefen fulanin Ya zauna yana Hade Rai, Bilal Yace "Dama Mai Martaba neh Yace muzo akai wani saqo daya bari" Fulani takalli Yarima daketa Hade Rai Tace "Bah komai baneh, Mai Martaba Yace Kai Qoqari ka Fitoda Mata kai Aure" Zaro ido yayi Yace "Aure Fulani??!" tace "Kwarai Aure" bata Fuska yayi Ranshi a bace Yace "Haba Fulani har nawa nake da Za'ace nai Aure am just 26 fah" Hararanshi tai Ta Kalli Bilal Tace "Kutashi Kuban Waje", Suna Qoqarin kiqewa Parveen tashigo dakin dagudu tareda Fa'dawa jikin Fulani tana dariya Tace "Fulani gst what??" fulani tana Murmushi Tace "Wht??" fara'a kwance kan fuskanta Ta kwalla ihu Tace "Umma na zuwa" itama dariyan tai Qasa Qasa Tace "Allah ya kawota Lapia" Sam Parveen bata lura dasu Yarima bah, Hankalinta ya tafi, Suko su Yarima Tv tazaman musu Sai Kallant suke, Muryan bilal datajine yana cewa mun tafi fulani Yasa ta juyo suka hada ido da Yarima, Hararanshi tai suka bar dakin...
Zune Take Cikin Garden din Gidan Sanyanyan iskan dake Wajan sai bugunta yake cikeda nishadi, Zaman jiran qarasowan Ummanta kawai take, Jakadiya ce Tashigo Garden din Ta durqusa Har qasa Takwashi Gaisuwa Sannan Tace "Mai Martaba nasan Ganinki yanzu Yana haraban gida yana jiranki" Tho Tace tareda miqewa Altine na biye da ita, A Haraban Gidan suka iskoshi tareda fadawanshi, Ta Karasa dasauri tareda tsugunnawa, Saurin tareta yayi yana murmushi yace "Tashi Tashi" ta mike tana Murmushi, Ya kalli fadawanshi yace "ku tsaya anan" Sannan ya kalli Parveen yace "muje koh??" murmushi tamai suka Fara tafiya yana janta da hira...
Bayan gidan suka nufa, sai bata labarai yake masu dadi daban dariya, Parveen koh dayake ansamu abinda akesi sai dariyan take, sunyi tafiya mai nisah har Suka Qarasa wani rafi dake bayan gidan, Carpet neh shimfide a wajan sai wasu bayi dake tsatsaye a wajan, nuna mata yayi ta zauna Shima ya zauna, aka Fara hidima dasu da kayan ciye ciye kala kala, Mai Martaba Ya Kalli Parveen Yace "Mahaifinki mutumin kirki neh, haka mahaifiyarki kiyi qoqari kibiyo hali irin nasu" murmushi Parveen tai kanta na Qasa. Yace "Parveen ina jinki kamar Yarima, Ki saki jikinki. Dake da Yarima duk daya kuke a wajena" Murmushi tai Batace komai bah. Shima murmushin Yayi Yace "Mahaifiyarki na hanya koh??" Kai ta gyada yace "Allah ya kawota Lapia" Ameen Tace suka cigaba da hiransu cikin nishadi. Sun dade suna hira Sannan Suka bar Wajan, Mintina kadan motoci suka Shigo gidan, Sam Parveen batasan Fulani ta fita bah saidai Ganinta tai an Bude mata qofan mota ta fito Sai Ga Umma itama ta fito, Ai a 360 ta tafi ta rungume Ummanta tana dariya harda hawaye, dakyar ta saki umman nata sukai Side din Fulani dukansu Cikeda Farinciki, Bama kaman Parveen...
Muje zuwa...!
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
A WANI MASARAUTA
π€π€π€ π
By Ummy Abduol
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.