Complete Hausa Novels

A Wani Masarauta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 25 of 25

Page2⃣5⃣

Koda suka qarasa side din ko inda deeza take bata kalla bah ta wuce daki fuuu..
Ganin ran parveen ya baci yasa tama Yarima sallama ta shigo dakin. Kayan barci tarar parveen nasawa, ta qarasa ta zauna bakin gadon tana kallanta.
"Lapia?? Naga ranki ya baci"
Aiko kamar jira take tako hayayaqo mata
"Ina ruwanki dashi?? Menene hadinki dashi?? Kin wani barni ni kadai kinata wani washemai Baki waike kuna hira"
Dariya sosai abin yaba deeza, ta dade tana dariya hakan yasa parveen ta qara quluwa. Saida Ta gama Sannan ta Kalleta
"Parveen kishi??, Ana cewa ba'asan yarima anma gashi ana kishinshi"
Tsaki parveen taja tana yamutse fuska
"Allah ya kiyaye nai kishin yarima. I hate him!"
Dan murmushi deeza tai
"Umm zakizo kiban labari"..

Pillow parveen ta wurga mata
"Banasan iskanci deeza, Bakisan yanda na tsani guy din nan baneh"
Shawarwari deeza ta dinga bah Parveen Har barci ya daukesu..

Da Safe suna Kicin yarima ya leqo, Murmushi deeza tamai Sannan tace
"Morning"
Morning shima Yace Yana Kallan Parveen, Fuskanshi bah yabo bah Fallasa Yace
"Haba Amarya bah Gaisuwa"
Dagowa tai ta kalleshi da mamaki
Gira ya daga mata, tai saurin kauda kai tareda hade Rai
"Good Morning"
Kintashi Lapia??" chewar yarima
Batareda ta kalleshi bah tace
"Lapia"
Deeza ya kalla Yana yar murmushi
"Frnd idan kun Gama ki Shirya xan kaiki yawo tunda yau saturday"
Murmushi tai tana Kallanshi
"Thank you very much Frnd"
Baice komai bah Yabar Kicin din.
Tsalle Deeza tai Tana cewa
"Woaw! Kamar yasan abinda nakeso knan, Allah yarima nada kirki. Kece dai baki gane hakan bah"
Dogon tsaki Parveen taja tacigaba da abinda takeyi.
Murmushi Deeza tai tareda girgixa kai..

Suna Gamawa Deeza ta shirya Ta Kalli Parveen, pls ki tashi muje. Mugun Kallo ta bita dashi tareda jan tsaki
"Bah inda zani, keh dai da kike uwar yawo sai kin dawo"
Bah Yanda Deeza bataiba Akan Parveen tabisu taqi, Hakana ta haqura suka Fita itada Yariman. Yawo yakaita Sosai, Sun jaje wurare dayawa, dan Zaman da Yayi da Deeza ya samu Labarin parveen sosai da Halayenta. Basu dawo gidan bah Sai Qarfe tara na dare, kwance suka samu parveen kan 3seater har ta soma barci. Dagudu deexa ta qarasa inda Parveen take tai tsalle ta fada kanta..

Ihu ta saki tareda tureta, Dariya Sosai Abin yaba yarima yabar Wajan zuwa daki yana cigaba da dariya
"Yarinya sai Rashin kunya ga shegen Tsoro"
Tsarabanta Deeza ta bata, taqi amsa, saida tace mata da kudinta ta siyan mata sannan ta amsa tana dubawa. Abinci ta hada takai mai daki, Wannan karan knocking tai, saida Ya bata izini Sannan ta shiga, Gabanshi ta ajiye Ta juya zata Fita. Muryanshi ta jiyo yana cewa
"Were are you going bayan mijinki na buqatarki a kusa dashi"
Qarasawa tai Zata bude kofan taji yace
"Haba Mallama uwar Malamai, Koh kin manta Malaiku na Tsinewa Macen da ta qauracewa Shinfidar mijinta"
Juyowa tai tana Kallanshi gabanta na dukan uku uku
"Nibah Malama bace, Har yanzu ni daluba ce. Bana tutuiya da ilimin danake dshi, bah kamar kai da kake iqirarin wani bazai iya karatun dakayi bah."
Murnushi Yayi yana Kallanta
"Bah Wannan na tambayeki bah"
Tsaki taja tana kallanshi ido cikin ido
"Kada ka Taba Tunanin taraiya dani a rayuwarka, Allah ya kiyaye. Mutumin da yagama zina da matan arna yace yanzu kaizo gareni, Allah ya kiyaye"
Bata jira mai zaice bah tabar dakin dasauri..

Murmushi kawai yayi tareda girgiza kai, Baisan meyasa bah yanzu sam Maganganun Yarinyan basa batamai rai, Saima burgeshi datake Yanda take tsayawa a gabanshi tana fadamai maganan da ranta yake so. Kofan ya kalla tareda yin kwafa ya koma ya zauna...

Washe gari deeza zata koma, Sam Parveen bataso haka bah. Tun da safe take qunci, Taso ace ta Qara mata koda kwana biyu neh anma Taqi, Hakanan ta Haqura. Da zata tafi parveen harda dan kukanta, Side din fulani ta rakata tai mata Sallama suka fito. Taso raka Aminiyar nata anma jin Yarima neh zai kaita Airport yasa Ta Fasa sukai Sallama tashiga motan suka tafi..

Side dinsu ta koma Cikeda kewar aminiyar nata, Yarima na kaita tasha Ya juyo ya Wuce Gidansu Mahdi. Yakoci Sa'a Yana Gida, Hira sosai suka shiga yi har suka gangaro kan maganan Parveen
"Yadai mutumina Ina fata komai ya wakana"
Girgiza kai Yarima yayi
"Bbu komai mutumina Wallahi, ni Har mamakin kaina nakeyi. Narasa yanda zan tari yarinyan nan, tanamin kwarjinin dayawa"
Dariya Mahdi Yayi
"Haba Yarima bansanka da Tsoro bah, yanzu kasan meh za'ayi??"
Girgiza kai Yarima yayi kallanshi
Tashi mahdi yayi ya qaraso inda yarima keh zaune, magana yamai a kunne wanda ni kaina bansan meh ya fadamai bah.
Kallanshu Yarima yayi
"Are you sure hakan zaiyi?"
Gyada kai mahdi Yayi
"Kwarai kuwa mai zai hana"
Sun dan jima Suna hira Sannan yarima yamai Sallama yabar Gidan...

Ummy Abduol✍🏻

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.