A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 19 of 25
Page1β£9β£
Qarasa Maganan Tai Rai Bace
"Kai Qoqari ka Koma Islamiya Dan Har Yanzu jahilci na Dawainiya Dakai!"
Wani Kukan Kura Yarima Yayi ya Mike Tsaye, Mari kyawawa Guda biyu Ya Saukewa Parveen Wanda Saida Taga Stars.
Shaqeta Yayi Fuskan nan Nashi Na Chanza zuwa ja, inda Abinda Yarima Ya Tsana Bai wuce Parveen Ta kirashi jahili bah.
Huci Yake Sosai, Hannunshi Na Kan wuyanta Daya Maqure, Parveen ko Sai Tari Take Dakyar Idanunta Sun Firfito, Ganin Bah sarki Sai Allah Gashi Bah Iya Magana Zatai bah Yasa Ta Rarumi Glass Cup dinda Ke kusa da Ita Ta Bugamai Akai. Sakinta Yayi dasauri ta Fadi Kasa Tana Rike Da Wuyanta, Wurin data Bugamai cup din Ya Dafe Ta mike Dakyar Ta nufi dakinta A Guje Tareda Sa Key..
Ranshi Bace Ya bita Da Kallo, Hannunshi dake kanshi Ya Sauke Yana Dubawa, Allah Yaso Cup din Bai jimai Ciwo bah. Wayanshi Ya dauka Yabar Falon a Zuciye. Parveen Kan Gadonta ta Fada Ta Saki kuka Mai Karfi, Anya Kuwa Zata Iya cigaba da Zama a Gidan nan Da Yarima?? Tsagaita Kukan tai Tana Tunani. Inko Har Zata Cigaba da Zama dashi to dole Tadau Damara Dan Ta Nunamai Itama Macece. Da Wannan Tunanin Ta Yini Yar Yanma..
Satin Parveen Biyu kullum Idan tai Girki Sai Tasama Mai Martaba Da Fulani, Shiko gogan Idan ya Dawo Atika take Sawa Tai Serving Dinshi. Ranar data Cika Sati biyu Kuma a Ranan Zata Fara zuwa Schl, Da Safe Ta shirya Cikin Hadadden Shaddanta Purple, Dinkin Riga da Skirt. Side din mai Martaba ta Fara nufa Don Kwasan Gaisuwa, Tana Shiga Ya tareta Da Fara'a, har qasa ta Tsuguna Ta Gaidashi. Ya Amsa Fuska a Sake, Godiya ya Mata Akan Abincinda Take aikomai, Dan murmushi kawai Tai Sannan Tace
"Bakomai Ranka Ya Dade. Kaima Ai Mahaifina neh"
Gyada Kai Mai Martaba Yayi
"Hakaneh Parveen, Inajin Dadin Girkin da kike Min, Yanzu duk na aje Girkin Turawan nan"
Dan Dariya tai Qasa Qasa, Ta Sadda Kai
"Ranka Ya Dade Yau kace Zan Fara Zuwa Makaranta"
Kai Mai Martaba Ya Gyada
"Hakaneh yanzu idan kin Shirya sai Aima Sarkin Mota Magana Yakaiki, Kije ki Zabi duk motar da Kikeso a Kaiki a Ciki"
Dan Murmushi Tai Tareda Godiya, ta mike Tabar Side din Cikeda Farinciki..
Side din fulani Taje Ta Gaidata Sannan Ta Mata Sallama. A Wani Hadadden Buggatti aka Dauketa Zuwa Makaranta. Ta samu An Gama Mata komai, Lectures Kawai Zata Fara Attending, Dadi Taji Sosai, A Ranan Tai Sabuwar Qawa mai Suna Yasmeen...
A Gida Kuwa yarima Cikin Shiri Ya Fito dan Zuwa office, Dogarinshi na Binshi dauke da Jakan laptop dinshi. Wajan Motocin Gidan Suka Nufa, Ganin Bah Motan Da yayi niyan Fita Dashi Yasa Ya Hade Rai, juyawa Yayi Ya Kalli Dogarin. Jeka Kiramin Sallau, Tho Yace Ya Tafi dasauri.
Chan Sai Gasu Tare, rai Bace Yarima Ya Kalleshi, Ina Motar danasaka Ka Wanke. Sosa Kai Sallau Ya Fara. Tsawa Yarima Ya dakamai
"Kai make Saurare"
"Ranka Ya Dade Gimbiyace Tace Abata Motan Dashi Za'a Kaita Makaranta"
Wace Gimbiya??"
"Amarya Ranka Ya Dade"
Tsawa Yarima Ya Dakamai
"Har Ni Inyi Magana Akan Inason Abu, Anma ka Dauka Kaba Wani Chan??"
Dogarin Dake Gefe Ya Kira Tareda Bashi Umarnin A Tafi da Salihu amai Bulala Hamsin Sannan A koreshi.
Dasauri Sallau Ya rusunna yana Bada Haquri
"Dan Allah Ranka Ya Dade Kamin Rai, Da Wannan sana'an Nake Cida Iyayena da Iyalina. Na Yarda Amin Bulalan Anma Kar a Koreni"
Tsaki Yarima Yayi, ya Shiga benz dinda Ke Kusa Dashi Drivern Ya Tada Sukabar haraban Gidan...
Parveen bata dawo gidan bah Sai Bayan La'asar, Side dinta ta nufa Saboda ta Gaji, Wanka tai ta Sauya Kaya Zuwa 3quater da Yar Qaramar Pink Tshirt, Saboda Lokacin Xafi neh. Kicin Ta Shiga ta Fara Hada Abincin Dare, Qulunta na waina ta bude Ta duba taga ko ya tashi har Yafara zubewa, Nan da Nan ta Fara Hada Miyan Alehonta Dayasha Kayan Hadi. Tana Gamawa Tahau Suyan Wainan. Bata Gamaba Saida Aka Kira Sallan Magrib, Sallah taje Tai Sannan Tazo Ta bada namai Martaba..
Zama Tai Taci Nata Sannan Ta koma Falo Ta kunna Tv tana Kallo, Yarima Bai Shigo Gidan bah Sai Wuraren Karfe Shadaya. Har Barci Ya kwasheta Tana Zaune Taji Bude Qofan Falon, Juyawa Tayi Taga Mai Shigowan, Yarima neh Ya Shigo Hannunshi Cikin na Wata Budurwa wacce bata wuce Sa'ar Parveen bah, Sanye Cikin wani dan qaramin Skirt, da Riga Half vest. Tsaki Parveen tai ta Mike Tabar Falon Zuwa Dakinta..
Washe Gari da Safe Tana Idar da Sallah Tadau qur'aninta Tana Karantawa, Bude Qofan Dakin Akai Aka Shigo, ganin Yarima neh Yasa Tace
"Sadaqallahul Azim"
Ta Rufe Tareda Hade rai Tana Kallanshi
Shima Fuskan Nashi a Hade Ya kalleta
"Yau Zan Fita da Wuri, Ki Tashi ki Hadamin Breakfast, Sannan Babyna Plantain Takeso da Egg Yau. Idan Na Fita Kiyi Qoqari Ki Gyaramin Dakina Kafin nadawo"
Bai Jira Cewarta Bah Ya Juya Zai Fita.
Murmushin Takaici Parveen Tai Tace
"Ai Baka Aje Yar Aiki bah a Gidan da Zata Maka Duk Wannan Aikin. Koh Ka Ajene ni Bansani Bah"
Juyowa Yayi ya Kalleta Rai Bace
"Ai Dake da Bayin Gidan nan Babu Maraba a Wajena, Duk daya Kuke. Dan Haka Ina Jiran Breakfast Nan da 1hour idan Bah Haka bah..kwafa Yayi Yabar dakin Tareda Bugo qofan Dakin"
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
*A WANI MASARAUTA*
π€π€π€ π
By *Ummy Abduol*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.