A Wani Masarauta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Wani_Masarauta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 25
Page1β£6β£
Sarauniya Fulani ce Tace Idan na Daujeka Naje na Dauki Amarya, Tace a Mota Daya za'a Kaiku..
Dogon Tsaki Yarima Yaja Ya Juyar dakanshi Yana Kallan Window..
Koda Sukaje Gidan Amarya Duk Qawayenta da Yan uwanta Sun Tafi daga Ita Sai Deeza..
Drivern neh Ya Fita Ya musu Magana, Parveen Ta Miqe Deeza Na Biye da Ita, Drivern Ya Bude mata Qofan motan Ta Shiga Ta zauna, Sam Bata Lura Da Yarima bah saida ta Zauna Sosai, Juyawa Tai Suka Hada Ido da Yarima, Dasauri Ta bude motan ta Fita Dagudu, Deeza Datake qoqarin Shiga Gaban Motan Taga parveen ta Fito a Guje. Binta tai tana kwala mata kira..
Shiko Yarima Kafada Ya Daga Ya Kira Drivern Yace Su wuce. Bah Musu drivern yaja Suka Bar Haraban Wajan, Taro Yayi Taro, Duk wanda Aka Gaiyata Ya Halarta Amarya da Ango kawai ake jiran Isowarsu. Dai dai Bakin kofan Wajan Drivern Yayi Parking, Mahdi da Sauran abokanan Ango tareda Qawayen Amarya Suka Qaraso wajan Dan Musu Rakiya Zuwa Ciki. Mahdi ne Ya bude Kofan Motan Ganin bah Amarya Yasa Ya Kalli Yarima
"Were is our Bride??"
Kafada Yarima Ya Daga Ya cigaba da Daddana Wayanshi
Sassauta Murya Mahdi Yayi
"Kaifa Dan Iska Neh Fardeen. Ina Amarya Pls?? Komai ya Tsaya a Wajan nan ku kawai ake jira"
Tsaki Yarima Yaja
"Pls Mallan Karka dameni"
Wayanshi Ya Ciro Ya Kira Layin Bilal dan Yasan Bai riga Ya Iso bah, saida Yayi Ringing so biyu Sannan Ya daga
"Pls Bilal kana Ina??"
"Ina Gida Yanzu zan Fito"
"Dan Allah idan Fulani basu Taho bah Ka Fada Mata Amarya Ake Jira"
"Tho" kawai bilal Yace Tareda Kashe kiran..
A Falo Parveen ta Cire Takalman Qafanta ta wurgar Ta nufi bedroom dinta a Guje tana Kuka. Deeza na Shigowa Tayi tuntube da Takalmin Saura Kadan ta fadi, Dakin Ta nufa tana Cigaba da Kwallama Parveen kira. Kwance Ta Sameta Ruf da Ciki Ta kuka Da Qarfi. Dasauri Ta Qarasa Tareda Dagota Zaune
"Why all dis Parveen?, Yanzu bah Lokacin kuka baneh"
Dagowa Parveen tai Tana Kallanta Cikin Kuka
"Deeza Uh Mean Ya..Yarima ne Mij..M..mijina??"
Gyada Kai Deeza tai Tana Share Mata Hawaye
"Ki Shafawa Zuciyarki Ruwan Sanyi Pls Parveen. Try to Fight Wannan Damuwan, Karki Sama Kanki Ciwo. Believe Me Evrything Wil Change Insha Allah"
Kuka Parveen Ta Cigaba Tana Dukan Gadon da Hannunta
"Why! Why!! Umma, Meyasa tuntuni Baki Fadamin Yarima neh mijina bah"
Sanda Saqon Mahdi yakaima Fulani, Dasauri Itada Mutanenta Suka Nufi Side din Amarya, Har Yanzu tana nan kwance Tana Kuka. Fulani na shiga Bedroom din ta qarasa bakin gadon Dasauri Ta Riko Parveen Tana Kallan deeza Tace
"Meya Sameta??"
Bayanin duk yanda Ya faru Deeza Taima fulani..
Shiru Tai Tana Tunani, Dakyar ta Samu ta Lallasheta aka sake mata kwalliya motarsu daya da Fulani Suka Nufi wajan. Mutane Sun Gaji da jira, Mutane Har sun Fara Tafiya...
Wuraren karfe Tara da Kwata motarsu fulani ta iso wajan, Har Yanzu ango na Cikin mota sai Waya yake da Yanmatanshi. Fulani ta fito tareda Kuyanginta, Deeza Ta riqe Hannun Parveen Suka Fito daga Motan, Mahdi Ya Qaraso wajan, Fulani Tace
"Kacema Yarima Ya fito"
Dasauri ya nufi motan da Yarima ke Ciki ya fadamai Saqon Fulani, Ya Fito Yana Taku irinna Qasaita. Daidai Inda Parveen ke Tsaye Suka Jera zuwa Cikin Hall din. Itadai Parveen kanta na Qasa bah Abinda Take Sai Zubda Hawaye...
Suna Shiga wajan Ya gaure da tafi da Kidi har Suka Qarasa inda Aka tanada musu suka zauna. Raye Raye aka Fara Tareda abubuwan bada Dariya, anci Ansha Sannan Aka Umarci Amarya da Ango su Tashi dan Yanka cake. Gaban Parveen Ya Fadi anma Ta dake Ta mike suka qarasa inda Cake din yake, Shiya Fara Riqe wukan Sannan Itama Ta Riqe Chan Qarshe Suka Yanka. Tafi akai musu, Mc Ya Umarci Ango Yaba Amarya Cake a Baki. Dakewa Yarima Yayi ya Yanko Yakai Mata Baki, Kauda kai Tai Tareda Yamutse Fuska. Tuna Mutane na Kallansu Yasa Ta Maida Fuskanta Ta gutsura Kadan. Tafi aka qara Musu Sannan Mc ya Umarci amarya taba Ango a Baki..
Dakyar ta Yanka qato ta dan dago Suka hada ido, kuda kai tai dasauri, Yadan rankafo takai mai Baki. A Hankali ya bude Bakin, ganin baida niyan Budewa Yasa Ta Tura Mai a Baki duka. Dariya akai Tareda Tafi, Yawancin Mutanen abin ya burgesu, Itako amarya da Gaiya Tamai dan Kawai ta batamai rai. Dakyar ya iya Cinyewa Ysa Hankie Ya goge Bakinshi, Ga Mamakina Gani nai Ya Kama Mata Hannu suka nufi wajan Zamansu, Suna Qarasawa Ta Fizge Hannunta Tana Turo Baki. Murmushin Mugunta yayi ya kauda Kai...
An Raba kyaututuka Iri Iri tun daga kan Joters, colenders, Takunkuna, Hankies, dinner sets, mugs, Ceramic plates dadai Sauransu, Haka Akai Dinner kowa Ya watse cikeda Farinciki. Kamar dazu Amarya mota Daya Suka koma gida da Fulani. Shiko Gogan Motarda Ta daukoshi Ita ta Maidashi Gida...
Ummy Abduolβπ»
π€π€π€π
*A WANI MASARAUTA*
π€π€π€ π
By *Ummy Abduol*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.