Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 25
[12/9, 4:30 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*
Story&writing
HUSSAINI YUSUF
Whtspp number
07069475482.
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alƙalaminmu ƴancinmu*
________________________________
Page 1&2
Sa'eed bn Abdul'aziz azzalumin mutum ne, kuma ƙwararren ɗan ta'adda, yana ɗaukar matasa masu yawan gaske, daga mabanbantan ƙasashe.
Yana koya musu ta'addanci, da sunan jihadi suke yi fisabilillah, haka kawai sai su shirya su hau kan babura su shiga ƙauyukan Fulani, su kashe na kashewa.
Su bar wanda kwanansa bai ƙare ba, duk yawan shanun da Fulanin nan suka tara, sai sun kora su, sun tafi da su, komi yawansu kuwa.
Yau ma kamar kullum, Æ´anta'addan sai shiri suke yi za su kai wa wani garin fulani hari, bisa umarnin shugabansu Sa'eed bn Abdulazeez.
Domin sun samu labarin garin suna da tarin, shanu da tumaki, har da awaki. Sa'eed ne ya kira wani mutum, cikin tantinsa domin babu wanda ya san inda maɓoyarsu take.
Duk lokacin da suka aiwatar da zaluncinsu, cikin wani baƙin jeji suke shigewa da zarar sun shiga wannan jejin, babu wanda ya isa ya bi bayansu.
Koda ya bi bayan nasu, ba isa ya gan su ba komi hatsabibancinsa kuwa.
Yayin da mutumin ya shiga cikin tantin ya tarar da shugabansa, a kishiginÉ—e akan wani buzu yana jan casbaha.
Sai ya tsugunna ya gaishe shi cikin ladabi, gyaran murya kawai yayi bai amsa sallamar da yayi masa ba, ballantana kuma gaisuwa. Murtuƙe fuska yayi yace "Ya kai Sahimu ya sunan ƙauyen da ka je ka gano a yankin najeriya?" duƙar da kai Sahimu yayi yace ya shugabana "Ba za mu kira wannan wajen ƙauye ba sai dai mu kira shi da gari." domin tarin albarkatun da suke da shi, ga su manoma ne sosai, sannan ga tarin shanun da Ubangiji ya albarkace su da su. Garin yana yankin jahar Taraba sunan shi Mambila.
"Da yaushe kake ganin zamu farmake su, ba tare da sanin jami'an tsaron yankin ba?" Sa'id ya tambayi Sahimu "Ai ina ganin mu je musu a daren yau ɗin nan" don akwai wani shagali da ake yi a garin matar shugaban ƙauyen ce ta haifi ɗa namiji, shi yasa shugaban nasu ya shirya shagali na musamman, domin taya shi murnar samun ɗa namiji.
Murmushin mugunta Sa'id yayi yace "Ka yi hanzari ka faÉ—a wa Æ´an tawaga kowa ya zama cikin shiri don zamu iya tafiya a kowanne lokaci.
Da sauri Sahim ya fice daga cikin ɗakin, ya sanar da saƙon shugaban nasu.
***
Garin sai shagali ake yi ko'ina jama'a ne rututu sai faman ci ake ana sha. Wani dattijo na gani a zaune gindin wata bishiyar magwaro, wacce sanyinta yake ratsa ƙashi da ɓargo ya shiga cikin jiki ya haifar da kuzari gami da ƙarfin jiki.
Wani yarone ya zo da gudunsa ya faɗa kan cinyar dattijon yana dariya, harara dattijon ya sakar masa yace "Anas har yanzu baka daina tsokanar ƙanwarka ba ki?" ka fi so kullum tayi ta raina ka ko?" A'a Baba ita ce fa ta fara tsokana ta, akan Inna ta aike ni in karyo itace a gona.
Au! ashe ma Innarka ce ta aike ka karyo ice, shine zaka taho nan? Shiru Anas ɗin yayi yana kallon Baban nasa, daka masa tsawa yayi yace "maza ka tashi ka je ka karyo mata itacen. Da gudu Anas ya tashi ya nufi cikin jejin, yana barin wajen ƙanwarsa Safna ta iso wajen tana kuka.
Faɗa masa abinda yayanta Anas yayi mata, haƙuri ya bata sannan ya kama hannunta suka nufi cikin gidan, dattijon yana shiga cikin gidan ya ga matarsa Inna Saratu tana ta faman aikin surfa dawa don ta ɗora musu sanwar rana. Zuwa yayi kama hannunta yace "Saro wallahi yau duk jikina nake ji babu daɗi, ina kyautata zaton akwai wani mummunan al'amari da yake shirin faruwa a garin nan ko kuma a kaina ko wani nawa. Cikin muryar fulatanci tace "Malam kai ka faɗa min duk lokacin da mutum ya ji fargaba tana ziyartarsa ya yawaita faɗin "Inna lillahi wa inna ilaiji raji'un". Idan ka manta yanzu na tuna maka, "ban manta ba Saro kawai dai na ji faɗuwar gaban nawa sai tsananta yake" to Malam Allah yasa mu ji alkhairi da amin ya amsa, sannan ya ɗauki buta ya nufi banɗaki.
A kan wata bishiyar kanƴa yake, yana ta ɓallo itacen da ya bushe yana jefo shi ƙasa, ɗaga kansa yayi ya hango wasu mahaya babura yawansu sun kai su ɗari. Sun nufo ƙauyen nasu sai faman harbi suke yi da bindigu, suna wani irin ihu! na mugunta.
Da gudu ya diro daga kan bishiyar, ya nufi cikin garin da gudu, Baffa yana alwala kawai ya ga Anas ya faɗo gidan da gudu. Yana zuwa ya tsugunna gaban Baffa, yana ta faman haki kai Anas lafiya kuwa? menene ya biyoka haka kake wannan gudun? Baffa ne ya jero masa waɗanan tambayoyin a jere, da kyar ya dubi Baffa yace "Baffa wasu mutane ne akan mashina, hannunsu riƙe da manyan bindigu suna ta harbi, Baffa wataƙila irin ɓarayin shanun nan ne da ka ba mu labari."
Da sauri Baffa ya miƙe yace "Kuma nan garin suka nufo?" Wallahi Baffa nan suka nufo sai ihu suke tayi.
Kafin Baffa ya samu damar furta harafi É—aya, suka jiyo harbi a waje take ya kama hannun Anas da Safna, ya nuna musu wani tsohon rumbu ko murfi babu yace "su shige ciki kada su kuskura su fito sai sun daina jiyo harbi da ihun mutane sannan su fito su yi ta gudu su koma cikin Gembu.
Da to Anas ya amsa yana kuka, ita ma Safna da ba ta cika wayo ba sai faman kuka take yi, ganin yayanta yana yi. Shafa kansu Baffa yayi yace Allah ya raya min ku Æ´aÆ´ana ya sanÆ´a albarka a cikin rayuwarku.
Sannan ya juya kama hannun Inna Saratu yace "ita ma ta shige cikin rumbun su zauna ita da Æ´aÆ´anta don baya so suyi maraicin uwa." Fashewa da kuka Inna ta yi, ta shiga cikin rumbun tana kiran Baffa shi ma ya zo ya shiga amma ko waigo su bai yi sai faman goge hawaye yake akan fuskarsa. ÆŠakinsa ya shige ya É—auko wata takobi sabuwa, da gudu ya nufi waje inda yake jiyo ihu gami da iface-ifacen mutane.
#Comment
#Share
HUSSAINI YUSUF
[12/9, 4:30 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*
Story & writing
HUSSAINI YUSUF
Whtspp kimber
07069475482.
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.