Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 9 of 25

*_____________________________*
*Page 17&18*

Yayin da Abu Nisreen ya fito ƙofar gidan, sai ya iske ɗan aiken me gari a tsaye yana jiransa, ya fito. Yana ganinsa yace "yawwa Allah dama kai me gari ya aiko ni ba kira ka" cike da mamaki Abu Nisreen yace "Lafiya me gari yake nema na? ni da ban daɗe da dawo wa garin ba."

Koma menene idan ka zo zaka ji, iska Abu Nisreen ya furzar daga cikin bakinsa yace "ka je ka ce masa ina zuwa amma sai na yi sallah zan zo." cike da mamakin maganar Abu Nisreen ɗan aiken me garin ya dube shi yace "Yanzu saboda ka raina yallaɓai yace ka zo kace sai kayi wani uzuri sannan ka zo?

Abu Nisreen yace "kiran me gari ya fi kiran Allah ne" don haka ka je ka ce masa ina yin sallah zan zo, bai jira abinda ɗan aiken megarin zai ce ba ya juya ya shige cikin gidan ya bar shi a tsaye, riƙe da baki na mamakin Abu Nisreen.

Yana shiga cikin gidan, ya ga su Iya da Inna duk hankalinsu a tashe, sakin fuskarsa yayi yace "Ummu Nisreen taso mu tafi gida" miƙewa ta yi haɗe da goya jaririn a bayanta, da sauri lya ta sha gaban Aisar (Abu Nisreen) tace "ba ka faɗa mana menene yake faruwa ba zaka tafi gida, bayan tun tafiyarka muke nan muna jiran ka dawo mu ji abinda yake faruwa.

Murmushi yayi yace "Iya ba wani abu ba ne dama me gari ne yace na zo yana kirana, shine nace sai na yi sallah zan je." Da sauri Iya ta dafe ƙirji tace "me gari fa kace Aisaru" to me yasa yake nemanka? wallahi Iya sai na je can fadar sai in ji dalilin kiran amma yanzu ni ban san kome ba akai, an ce dai yana kirana.

Ajiyar zuciya Iya ta sauke tace "Allah yasa dai mu ji alkhairi, da amin gaba É—ayansu suka amsa, sannan Aisar ya ja hannun matarsa suka fice daga gidan. Rahila (Ummu Nisreen) zuciyarta fes yau ta samu É—a, kuma É—an ma namiji, abin da ta daÉ—e tana mafarkin samu idan ta yi aure wato É—a namiji, amma cikin hukuncin Allah sai ya bata Æ´a mace.

Amma hakan bai sa ta ƙyamace ta ba ko taƙi ta hasali ma soyayyar da ta nunawa Nisreen, Aisar har kishi ya rinƙa yi, saboda ba ya samun kulawa daga wajenta kamar da, kafin ta haihu, amma yanzu da ta haihu duk kulawar da take bashi ta koma kan ƴar ƙaramar ƴarsu wato Nisreen.

Yau shekararta takwas da haihuwar Nisreen, Allah bai sake ba ta wani cikin ba, ballantana ta saka ran samun namijin, har ta fitar da rai sai ga shi Allah ya kawo mata ɗan har gida, ita kuwa me zata yiwa Allah ba godiya ba? domin ya cika mata burinta na rayuwa ya kawo mata ɗa namiji har gida. Don haka a cikin ranta ta ɗauki alƙawarin sai ta yi azumi uku don nuna tsantsar godiyarta ga Allah (S.W.T), suna cikin tafiya Aisar ya fahimci halin da take ciki, ya kalli fuskarta, ya ga sai faman murmushi take saki kamar gonar auduga.

Cike da jin daɗin ganin matarsa a farinciki ya tambayeta abinda ya sakata murmushi haka, kamar wacce aka yi wa albishir da gidan aljanna.Ƴar dariya ta saka tace "haba Abu Nisreen akwai abinda ya saka ni farinciki fiye da wannan gagarumar kyautar da kayi mini?

Da mamaki a fuskarsa yace "ni kuma wacce gagarumar kyauta na yi miki da har take saka ki farinciki haka? nuna masa jaririn da yake bayanta ta yi, tace "akwai kyautar da tafi wannan a wajena?"

Girgiza kai yayi yace "babu domin na san yadda ki ke matuƙar son ɗa namiji" amma bari na yi miki wata tambaya, yi tambayarka kowacce iri ce insha Allah indai na sani zan baka amsarta.

Me yasa lokacin da na shigo da jaririn nan, ban ga fara'a da walwala a fuskarki ba kamar yanzu? Sake sakin wani murmushin ta yi tace "abinda yasa lokacin ba ka ga fara'a a fuskata ba, gaskiya ba zan ɓoye maka ba, abu ɗaya ne zuwa biyu.

Na farko shaiɗan ne yaso yayi wasa da zuciyata wajen saƙa mini mugayen abubuwa a cikin raina, lokacin da na ganka da jariri, sai na rinƙa tunanin ko ba farauta kake zuwa ba, shashancinka kake zuwa shine har ka samo ɗa ka zo ka ce tsinto shi kayi, abu na biyu kuma shine bayan na kawar da tunanin da shaiɗan yake ta aikin saƙa mini game a wannan jaririn, sai na ji ƙaunar yaron ta shiga cikin raina, na tuna ina masifar son ɗa namiji amma tun da ga shi na samu zan yi sake da damata, sai na ji tsoron kuma kada ka kai shi gidan me gari ya ƙwace shi ya bai wa wata matar ni kuma a bar ni da baƙin ciki, to ka ji abinda yasa ka ga ban yi maraba da yaron ba tun wuri.

Sosai ya jinjinawa matar tasa bisa wannan ƙoƙari da ta yi, kuma ya godewa Allah da ba ta bi son zuciyarta ba da ruɗin shaiɗan.

Cike da nishaɗi suka isa gidan, suna shiga buta Aisar ya ɗauka domin an fara kiran sallar Isha, bayan ya gama alwalar ya miƙe tsaye yace "Ummu Nisreen ni zan tafi masallaci, kuma daga can zan wuce gidan me gari, domin na ji kiran da yake yi min sannan ya dubi Anas yace idan ya gama ta shi alwalar ya same shi a masallaci."

Murmushi ta saki tace "To Abu Nisreen Allah ya dawo min da kai lafiya, cike da jin daÉ—i ya amsa da amin sannan ya fice daga gidan.

Bayan ya fita Ummu Nisreen ta dubi Anas tace "idan ka dawo daga masallacin ka zo ka karɓi abinci, amsawa yayi da to sannan shi ma ya fita daga gidan domin zuwa ya samu jam'i.

Bayan an idar da sallar Abu Nisreen ya cewa Anas ya koma gida ya ci abinci, shi zai je domin amsa kiran me gari, babu musu Anas ya nufi gida, shi kuma Aisar kai tsaye ya nufi gidan me gari domin ya ji dalilin kiran shi da aka yi.

Yayin da ya iso fada sai ya ga fadar cike da jama'a, sun kewaye me gari da yake zaune akan wata kujera, wacce aka haÉ—ata da katako. Yana iso wa jama'ar wajen suka dare, suka buÉ—a masa hanÆ´a ta tsakiyarsu, ba tare da tunanin komai ba ya shige yaje har gaban me gari ya tsugunna ya kwashi gaisuwa, a wajen dagacin.

Amma ko ci kanka babu wanda yace da shi a wajen ballantana yasa ran za'a amsa masa gaisuwarsa, gaba É—aya jama'ar wajen shiru suka yi suna sauraren su ji abinda me gari zai ce.......akan Aisar.

Sai da aka É—auki dogon lokaci sannan me gari yayi gyaran murya, yace "wato yanzu kai Aisaru abin naka har ya kai ga haka?" Cike da mamaki Aisar yace "ranka ya daÉ—e me na yi kuma?"
Cikin ɗaga murya me gari ya fara faɗa yana cewa "yanzu in ban da ka raina mu, mu tashi ɗan aike mu ce ya faɗa maka ka zo yanzun nan ana son ganinka a fada, amma saboda ba ka ganin girmana na shugaban ƙauyen nan, ka ƙi zuwa har sai da ka kammala abinda kake sannan ka kwaso wasu shegun ƙafafunka ka zo.

Sunkuyar da kai Aisar yayi cike da ladabi yace "Allah ya baka yawan rai, ba ƙin amsa kiranka na yi ba gani na yi lokacin sallah yayi shine nace idan mun idar da sallar sai na zo.

Rufe min baki ja'iri kawai ni zaka nunawa sallah? me yasa ba ka zo nan mun yi sallar tare da kai ba? me gari ya faɗa a hasale. Murmushin takaici Aisar ya saki yace "yallaɓai a yi haƙuri na tuba" mtssss! me gari ya ja wani dogon tsaki yace.

"Dama abinda yasa na aika a kiraka ba komai ba ne, sai dangane da wani zargi da mutane suka fara yi akan ka, kai da mahaifiyarka, da sauri Anas ya ɗago da kansa ya kalli me gari yace "yace Yallaɓai me mutanen suka ce mun yi musu ni da Iyata?" Ni dai a iyakar sanina ina zaune da kowa lafiya.

Me gari ne ya cigaba da cewa "zarginka suke yi wai idan ka fita farauta, matan banza ka ke bi shine har ka samu ƴaƴa ka ɗauko su ka kawo su garin nan, yau ɗin nan ance ka zo da wasu yara har da jariri. Ita kuma mahaifiyarka ana zarginta da taimakawa ƴanta'adda domin an shaida min cewa " matar nan da mahaifiyarka ta taimakawa ƴar leƙen asiri ce, ta zo ne domin ta ga yadda ƙauyen namu yake ta shaidawa ƴanta'adda su farmake mu su kashe mu su ƙwace dukiyoyinmu, sannan su raba mu da rayuwarmu.

Ƙarya take domin an shada mana a ƙauyen da ta baro, babu ko mutum ɗaya da ya tsira da rayuwarsa ƙarya ta faɗa mana domin kawai ta samu damar da za ta aiwatar da aikinta ba tare da wani ya gano shirinta ba, ballantana ya tona mata asiri, da yake Allah ya riga ya karemu sai ya tona mata asiri shirinta ya watse cikin ƙanƙanin lokaci......

To be continue.......
Comment and share

Hussaini Yusuf✍🏻
[12/9, 4:34 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐*

Labari da Rubutawa
HUSSAINI YUSUF

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

*_________________________________*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.