Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 25

______________________________
Page 3&4

Kisa kawai suke yi babu tausayi, ballantana imani a ciki. Ai sai da imani tausayi yake shiga, to su dai waɗanan babu ko ɗaya a tare da su (imani ko tausayin), yara sai kuka suke su da mata, duk wani namiji majiyin ƙarfi sai sun hallaka shi.
Yayin da Baffa ya fito daga gidansa, hannunsa riƙe da wata zabgegiyar takobi, tsaye yayi yana zubar da hawaye takaici duk ya cika masa rai. Yanzu ace "saboda zalunci wasu su zo lallai sai sun raba ka da dukiyarka, bayan an raba ka da dukiyar taka ma baza'a ƙyale ka ba, sai an raba ka da rayuwarka?"
Goge hawayen takaici yayi, dai-dai nan ya ga wani mugun É—an ta'adda, ya É—auki wani jariri ya cilla shi can sama, ya bushe da wata irin dariya mai kama da haushin kare, ya tsaya ya harÉ—e hannuwansa don yaga yadda jaririn zai faÉ—o.
Cikin zafin nama, Baffa ya tafi da gudun gaske wanda bai taɓa yinsa ba, a iya tsawon rayuwarsa, kafin jaririn ya iso ƙasa Baffa ya je saitin da zai faɗo ya tare shi. Ji yayi alamun jaririn ko motsi babu a tare da shi, haka ta sa yayi zaton ya mutu sai ya ɗauke shi ya kai shi can gefen hanƴa ya ajiye shi, yana ajiye shi kafin ya juyo ya ji an buga masa wani ƙaton sanda. Bai san lokacin da ya faɗi ƙasa ba a matuƙar galaɓaice, yana fitar da numfashi sama-sama.
Ɗanta'addan ne ya zo kan shi ya raba ƙafafun shi, yayi wani shu'umin murmushi wanda kai tsaye zamu iya kiran shi da kuka, domin ya fi kama da kukan. Damƙo gashin kan Baffa yayi yace "wato kai tsoho shine ina nishaɗina zaka zo ka katse ni ko?" waye kai ɗin ina iyalinka?" Shiru Baffa yayi yana ta kallon fuskar ɗanta'addan, ganin Baffan ba zai ba shi amsa ba ne ya zaro wata bindiga pistol, ya ɗamawa Baffa a ciki, nan take kuwa Baffa yayi shahada.
Yayin waɗanan azzaluman ƴanta'addan, suka ga sun tarwatsa ƙauyen sun kashe na kashewa, sai suka tattaro duka shanun da suke garin, suka tare su a waje ɗaya. Sannan wasu daga cikinsu suka kora shanun suka yi gaba da su, su kuma sauran suka suka rinƙa cillawa ƙauyen wuta.

Har yanzu Inna da ƴaƴanta biyu ANAS DA SAFNA, suna maɓoyar da Baffa ya ajiye su, sai faman haɗa gumi suke yi. Ji suka yi rumbun da suke ciki ya ɗauki zafi sosai, da sauri Inna Saratu ta fito ta leƙo gani ta yi ko'ina na gidan ya kama da wuta, sauri ta yi ta fito daga cikin rumbun sannan ɗaya bayan ɗaya ta zaro ƴaƴanta.
Bayan sun gama fitowa, sai ta ɗauki Safna ta goya ta a bayanta sannan ta kama hannun Anas ta ja shi suka fita daga gidan da gudun gaske, banda gawarwakin mutane da suke haɗuwa da su a hanya babu abinda suke gani, sai gidajensu da aka cillawa wuta. Suna jiyo hayaniyar mata da ƙananan yara, a can tsakiyar garin, kuma har yanzu ƴanta'addan ba su tafi ba. Don daga inda suke suna jiyo, ihunsu da kururuwarsu, suna yiwa matan ƙauyen kashedi. Gudu-gudu sauri-sauri su Inna suke tafiya, a cikin garin, hango wani ɗanta'adda Inna ta yi ya nufo inda suke, gani ta yi alamun bai gan su ba, sai ta yi sauri ta ja hannun Anas suka shige cikin wata duhuwa, suka ɓuya. Cikin takun ƙasaita, ɗanta'addan ya zo dai-dai inda su Inna suka ɓuya ya tsaya. Nan take ya hau yiwa kan shi kirari, "Sai ni uban maza mai mayar da ƙananan yara marayu, sai ni mai mayar da mata zawarawa, sannan ya ƙwalla kabbara da ƙarfin gaske, har sau uku "Allahu akbar! Allahu akbar!! Allahu akbar!!!" dai-dai lokacin wani ɗanta'addan ya ƙaraso wajen, ya kawo masa wata bindiga ƙirar AK47, duban wanda ya kawo masa bindigar yayi yace "ya kai Sahimu aikinka yana yin kyau sosai don haka a cikin ganimar nan da aka samu kana da kaso mai tsoka." take Sahim ya tsugunna ya hau yin godiya, duk abinda yake faruwa akan idon Inna da Anas yake faruwa, ita kuwa Safna tana bayan Inna a goye kamar wata jaririya.
Nan take tunanin Baffa ya faɗowa Inna, hawaye ta shiga zubarwa tana wani kuka marar sauti taso ta ɗaga muryarta tayi kuka ko zata ji sauƙin raɗaɗin da zuciyarta take yi mata. Sai dai ina? babu halin aiwatar da haka domin kada ƴanta'addan nan su jiyota, yanzu babban burinta bai wuce ƴaƴanta su rayu ba, saboda ta saka a cikin ranta duk rintsi sai ta tseratar da rayuwar ƴaƴanta abun alfaharinta.
ƙarar bindiga ne ya doki dodon kunnensu, yadda wannan mutumin ya riƙe bindigar nan sai faman harbin sama yake yi da ita, ƙarar bindigar ce ta firgita su Inna Safna da take goye a bayan Inna ce ta ƙwala wani ihu! mai ƙarfin gaske, take kuwa ƴanta'addan nan mutum biyu suka jiyo ihun! yarinƴar take suka fara laluben inda suka jiyo Ihun! hango Inna suka yi tana ta faman tiƙar gudu hannunta riƙe da wani ƙaramin yaro bayanta kuma goye da wata ƙaramar yarinƴa, take kuwa suka ce "da wa Allah ya haɗa mu ba da ke ba?" Take su ma suka rufa mata baya cikin matsanancin gudu.

Gudu sosai Inna da Anas suke yi, da ƙyar Inna take iya ɗaga ƙafarta domin ta yi mata nauyi sosai, ga goyon Safna a bayanta amma hakan bai hanata gudun ba domin ta tseratar da rayuwar ƴaƴanta koda ita zata rasa rayuwar tata. Gani tayi sun tserewa ƴanta'addan sosai haka yasa suka sake shiga wani lungun suka cigaba da gudun don kada ƴanta'addan su riske su.
Da gawar Baffa Inna tayi karo a kwance a kan hanƴa, wata razananniyar ƙara ta saki, sannan ta sulale ƙasa sumammiya...✍️

COMMENT AND SHARE FANS🙏🙏🙏

HUSSAINI YUSUF
[12/9, 4:32 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐ANAS MALEEK🫐🫐*

Labari/Rubutawa
HUSSAINI YUSUF

Whatsapp number:
*07069475482.*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.