Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 25

*_________________________________*
*Page 23/24*

Yana shiga ya tarar da Rahila (Ummu Nisri) a zaune ta zuba tagumi, ko sallamar da yayi bata ji ba, ballantana ta amsa zuwa yayi kusa da ita ya tsugunna a gabanta, ya sauke mata hannuwanta daga haɓarta.......

Murmushi ta sakar masa amma kana gani ka san yaƙe ne kawai ta yi don bai kai cikin zuciyarta ba, shi ma zama yayi a kusa da ita yace "Haba farin cikin rayuwata, annurin zuciyata wacce nake kalla a koda yaushe na ji farinciki marar misaltuwa, menene ya saka ki a cikin wannan damuwar har nayi sallama ba kiji ni ba.........?

Murmushi ta sakar masa tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta tace "Babu komai mijina kawai ina tunanin inda zamu koma ne, ba mu san kowa ba, kuma babu wanda ya san mu" karkaɗa mata kai yayi yace "Ba wannan ne ya saka ki cikin damuwa ba, ki faɗa min gaskiya kin ji abinda mahaifinki ya faɗa ko........?

Fashewa ta yi da kuka cikin muryar kukan take cewa "wallahi ko da wasa bana son rabuwa da kai mijina, ko a mafarki bana tunanin rabuwar mu, don Allah karka tafi ka bar ni a garin nan, domin baƙin ciki ne zai kashe ni, ba zan taɓa iya rayuwa babu kai ba, don Allah ka taimaka karka ɗauki zantukan mahaifina, domin umarnin Goggo ne ita ce ta saka shi ya zo yace bai yarda na bika ba. Domin ta samu damar da zata muzgunawa rayuwata, son ranta...........

Kama hannunta Aisar yayi ya ja ta cikin ɗaki, ita kuwa sai bin shi take yi, kamar raƙumi da akala, bakin gado ya zauna ita ma ta zauna kusa da shi, ido cikin ido suka ƙurawa juna idanu, sun daɗe a haka kafin Aisar yayi ƙarfin halin cewa.........

Rahila kin san ina sonki ko? shiru tayi ta ƙura masa idanu, kuma kema kina so na, anan ma shiru tayi tana kallonsa ta kasa furta koda kalma ɗaya cigaba yayi da cewa.........

Tunda har kina sona to ki saka a ranki babu wanda ya isa ya rabamu, sai mutuwa ki cire duk wata damuwa daga cikin ranki na fargaban rabuwa da ni, domin duk inda zani tare za mu tafi kaf faÉ—in garin nan gaba É—aya babu wanda ya isa ya hana ni tafiya tare da ke tunda har kin amince za ki bini mu tafi...........

Jiyowa suka yi daga waje ana dukan ƙyauren gidan kamar za'a karya shi, sakin hannun Rahilat Aisar yayi ya fito da sauri, ganin su yayi a tsaitsaye a tsakar gidan, hannunsu ɗauke da makamai........

Suna ganin shi ya fito kallon rainin wayo wani daga cikinsu yayi masa yace "Sarkin dawa Aisar an turo mu ka bamu matarka da takardarta a hannu mu tafi da ita, idan kuma kayi taurin kai ance muyi maka lahani idan ya kama ma mu kashe ka mu tafi da ita.........

Fashewa da kuka Ummu Nisrin ta yi, ta lafe a bayan Aisar jikinta ban da tsuma babu abinda yake yi......

Cike da ƙwarin gwiwa Aisar ya dube su yace "Ku je ku faɗa wa wanda ya turo ku, kuce masa ya rasa waɗanda zai turo su tafi da matata sai ku? Kuyi maza ku faɗo masa, na fi ƙarfin nayi faɗa da ku sai dai ya turo na sama da ku.......

Maganar ta yiwa shugaban Æ´an'daban zafi, cikin fushi ya dubi wani daga cikin yaransa yace " zaki maza ka je ka gwada masa ko mu su waye ya daina raina mu"........

Cikin fushi wanda aka kira da zaki ya nufo Aisar da mugun nufi a cikin ransa, yana zuwa ya ɗaga wata ƙatuwar adda zai sari Aisar a kafaɗa, cikin zafin nama Aisar ya tare saran sannan ya kama hannun da ya riƙe addar ya murɗa ji kake ƙarararas! hannun ya karye wurgar da shi yayi a gefe yana ta faman ihu da ƙaraji na raɗaɗin karayar da ya samu a hannu.....

Sauran ƴan'dabar tsorata suka yi, suka tsugunna suna baiwa Aisar haƙuri, ogansu ne kawai ya ƙi ja da baya, duban Aisar yayi yace "Ni nan da ka ganni ba zan taɓa tafiya ba sai da Rahila, kuma an yi min alƙawarin indai ka sake ta ni za'a aurawa ita, ta zama matata ta har abada.....

Cikin fushi Rahila ta dube shi tace "ƙarya kake wallahi kai baka isa na zama matarka ba, sai ko idan bana numfashi, sannan sai ka auri gawata.....

Cikin fushi ya taho wai zai doke Rahila, riƙe shi Aisar yayi yace "Ka yi kuskure da har ka yarda ka kawo kanka waje na, kuma wannan furucin da kayi kace Rahila ta zama matarka to sai ka yi nadamar yinsa.....

Yana gama faɗar haka ya dube shi ya wanka masa wani gigitaccen mari a fuska, take kuwa haƙorinsa ya fito daga bakinsa ya faɗi can waje ɗaya, amma duk da haka Aisar bai bar shi ba ya kwarfe shi ya faɗi ƙasa ji kake tim wata ƙara ya saki, kana ji ka san ta irin wanda ya sha wahalar nan ne......

Ɗaga ƙafa yayi zai taka shi, da ƙyar ya iya ɗaga hannunsa alamun Aisar yayi haƙuri fasa taka shi yayi, ya dubi sauran ƴan'daban, duk sun tsure sai muzurai suke yi jikinsu yana rawa, a fusace Aisar ya dube su yace " waye ya turo ku ku raba ni da matata.......?

Cikin muryar tsoro suka ce "Goggo ce da me gari da malam Inusa (mahaifin Rahila) suka ce kar mu dawo sai da Rahila, kuma sun yi wa Ƙaura alƙawarin indai ya dawo da ita za su aura masa ita, dama tsohuwar budurwar shi ce ada.......

Kaiiii! Aisar ya daka musu tsawa yace "yi min shiru ko na yanke harshenka, wawa kawai yanzun nan ku je ku shaida musu tare da Rahila zan bar garin nan, tun da har ta yarda zata bini mu tafi babu wanda ya isa ya hanani tafiya da ita.......

Tashi suka yi jikinsu yana tsuma, za su bar wajen, dakatar da su yayi yace "ku zo ku É—auke waÉ—annan banzayen ku tafi da su, ko kuma anan za ku bar min su.......?

Cikin sanÆ´in jiki suka dawo suka É—auke su ranga-ranga rai a hannun Allah suka fita da su banda huci babu abinda Aisar yake yi..

Suna fita Aisar ya dubi Rahila yace "ki fara haɗa mana kayanmu yau zamu bar garin nan, yanzu zan je na faɗawa su Iya suma su shirya sai mu tafi domin na ga kawai ana son hallakamu a garin nan yafi kyau mu bar shi cikin lumana tun kafin mu zo muna nadamar ƙin barinsa da wuri.....

Fita yayi daga gidan ya nufi gidan Iya domin ya faÉ—a musu su shirya, yana cikin tafiya a kan hanÆ´a tunani kala-kala sun cika masa ransa, ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa, a ransa yake ji barin garin shi yafi alkhairi fiye da zama a cikinsa....

Kamar daga sama ya ji ance "Aisar sannan aka bushe da wata mahaukaciyar dariya, waigawa yayi domin ya ga me dariyar wani mutum ya gani, yan nufo shi abokin zuwa farautarsa ne, ba tun yanzu yake takun saƙa da Aisar ba, kullum burinsa shine ya ga Aisar a ƙasa, ko kuma ya rushe masa zaman lafiya a garin....

Yana ƙarasowa kusa da Aisar ɗin, sai ya bushe da wata dariya, ya dafa kafaɗar Aisar yace "Aisar a zatonka waye ya haɗa maka wannan munafurcin aka tsane ku a garin nan? Girgiza kai Aisar yayi yace ban san waye ba, amma kafin na bar garin nan ina son na gano ko waye, domin na ɗauki fansar abinda yayi min....

Bushewa da dariya yayi yace "Aisar kenan ban taɓa ganin kasawa a tare da kai ba, kullum zuciyarka a dake take, irin zuciyar mazan jiya ce da kai Aisar, ka sani ba kowane ya haɗa maka wannan cakwakiyar ba, face ni ɗin nan da kake gani a tsaye a gabanka, kuma kafin ka bar garin nan sai na haɗa maka wata cakwakiyar da zata saka mutanen garin nan suyi maka bore kafin ka.......Ji kake fauuuu! cikin fushi Aisar ya dunƙule hannunsa da iyakar ƙarfinsa ya daki bakin mutumin.......

Take kuwa haƙorinsa yayo fitar burgu daga bakinsa, jini ya cika masa baki, amma haka bai sa Aisar ya ƙyale shi ba, ya hau shi da duka da bugu ya rinƙa tattaka ruwan cikinsa, tun yana ihu yana neman taimako, har ya daina motsi sannan Aisar ya ja shi cikin wata duhuwa ya wurgar da shi yayi tafiyarsa abinsa.....

Babu wanda ya ga lokacin da yayi masa wannan abin domin hanyar ba mutane ne suke binta sosai ba, shi yasa tun lokacin da ya fara dukansa babu wanda ya zo wajen ballantana ya cece shi daga wajen Aisar É—in.....

Sauri kawai Aisar yake domin ya isa gidan Iya, zuciyarsa fes ya ɗauki fansa akan wanda ya haɗa shi da ƴan garin, ko kaɗan bai yi nadamar abinda ya aikata ba domin ya tsani munafiki, tsana ba ta wasa ba, da wannan tunanin ya ƙaraso gidan Iya, shiga yayi ya gaishe su bai jira sun amsa ba yace " Iya kuyi sauri ku haɗa kayanku yanzun nan domin so nake mu bar garin nan kafin wani abun ya faru da mu.....

Tambayar shi abinda ya faru Iya ta yi, cike da zaƙuwa yace "Iya yanzu ba mu da lokaci, ku dai kawai ku shirya mu tafi, idan mun samu nutsuwa zan faɗa muku komai....

Nan take kuwa suka hau shiri, dama ba wasu kayane masu yawa da su ba, nan da nan suka gama shirinsu suka biyo bayan Aisar suka fice daga gidan....

Gidan Aisar suka nufa, akan hanÆ´arsu ta komawa ne suka haÉ—u da wani abokin Aisar a firgice ya dubi Aisar yace "Yawwa Aisar dama neman ka nake yi ruwa a jallo, kuyi sauri ku bar garin nan domin naga matasa yaran ÆŠanliti sai wasa makamansu suke yi wai me garine da mahaifin matarka Rahila suka turo su, su hallakaka du É—auki matarka su tafi da ita, ba ka ga shirin da suke yi ba, wallahi so suke su kashe ka a cewarsu kai É—anta'adda ne....

Fashewa da kuka Iya da Inna suka yi, shi kuwa Aisar ransa ne ya ɓaci matuƙa, ba don yana son ya tseratar da rayuwar su Iya ba, da sai ya tsaya ya koyawa me gari da sauran mutanen garin hankali.

Cikin sauri ya ke tafiya su Iya suna bin shi a baya, su Nisreen da Safna ma, su har gudu-gudu sauri-sauri suke yi, hannuwansu sarƙe da na juna, addu'a yake yi a cikin ransa Allah yasa ba su je gidansa ba.

********
Farkawa yayi daga dogon suman da shafe awa ɗaya yana yi, ganin shi yayi a cikin ciyawa a kwance, an jefar da shi kamar mushe da sauri ya tashi zaune, nan take ya rinƙa tuno abinda ya faru tsakaninsa da Aisar, shafa bakinsa yayi yaji jini, hawayen baƙinciki ne ya zubo masa kamar an tsikare shi ya miƙe tsaye ya kurma wani uban ihu.

Ihuuuuuuuu! Aisar gani nan bisa kan ka, falfalawa yayi da gudun tsiya cikin garin domin ya je ya shirya yaransa su yi wa Aisar kisan wulaƙanci......

To be continue............
Comment and share

Hussain Yusuf
[12/9, 4:36 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*

*NA*
*HUSSAIN YUSUF*

*______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.