Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 25
*Page 31/32*
Bayan an idar da sallar a tare suka fito daga masallacin, a ƙofar gidan suka zauna Aisar ya shiga ba wa Sa'ad labarin yadda kasuwar ta kasance yau, fatan alkhairi Sa'ad yayi masa, hira sosai suke yi har aka yi kiran sallar Isha'i suka tafi masallaci.
Bayan sun dawo Sa'ad ya shiga ya fito musu da abinci, shi ma Aisar ya shiga ciki sai ga shi da nasa abincin.Da mamaki Sa'ad ya kalle shi yace "Aisar abinci ka bayar aka dafa maka ne?" murmushi Aisar yayi yace "E wallahi gani nayi nauyin zai yi maka yawa, ga su Ammi ga mu ai abin da yawa, shi yasa nace daga yau ba zan sake barin ka da wannan nauyin ba.
Ɗan ɓata fuska Sa'ad yayi yace " me yasa kake haka ne Aisar? na riga na shaida maka ku baƙina ne har yanzu baku zama ƴan gari ba, to wai ma kwata-kwata nawa ka samu daga fara sana'arka zaka fara kashe kuɗi haka? so kake ka cinƴe jarin da wuri haka?"
Murmushi Aisar yayi yace "gani nayi kai ma samunka ba wani ƙarfi ne da shi ba, mota fa kake ja wata ran ka samu fasinja wataran kuma ba zaka samu.....waya gaya maka? Aisar ya faɗa yana mai duban Aisar, ya cigaba da cewa "Ai ni nan da ka ganni ina da motoci sama da guda biyar kuma duk haya na bayar da su, har wannan da na ke ja guda shida, duk wata ake kawo min balance, kuma a haka zaka ce samun mu ɗaya?
Ka ga kenan tun da na fika samu dole ne na taimaka maka, yanzu ma abinda nake so da kai shine, ƴaƴan nan naka zan kai su makarantar boko da Islamiyya, kuma ni zan ɗauki nauyin karatunsu har su gama insha Allahu na ɗauki alƙawari, insha Allahu.
Aisar ne yace "Haƙiƙa tun da nake a rayuwata ban taɓa ganin mutum mai karrama mutane da ganin darajarsu kamar ka ba, kana da mutunci ƙwarai da gaske. Ka duba tunda Allah ya kawo mu nan gidan, ba ka taɓa tambayar labarinmu da abinda ya baro mu daga gida ba, haka mahaifiyarka da matarka ma ban taɓa ganin wani a cikinsu ya nuna mana tsangwama ko kyara ba, kullum cikin kokarin kyautata mana suke yi.Ba mu da bakin da zamu gode muku, sai dai muyi ta yi muku addu'a, har ƙarshen numfashinmu, kuma Allah ya bamu ikon saka muku da abin da kuka yi mana, fiye da shi ma Allah ya ba mu mu saka muku.
Dafa kafaÉ—ar shi Sa'ad yayi yace " Aisar duk abin da ka ga nayi muku, nayi muku ne saboda Allah don haka bana neman wata sakayya daga gare ku, a wajen Allah nake neman sakayya ta. Nan dai suka cigaba da hira har suka cinÆ´e abincin, suka tattauna akan sana'ar Aisar wato gwanjo, bayan sun gama cin abincin kowa ya tashi ya tafi lungunsu.
Yayin da Aisar ya shiga sai ya tarar da Rahila ta idar da sallah, nan da nan kuwa suka hau yin hira, sai wajen sha É—aya da rabi na dare sannan suka kwanta.
Washe gari da safe kowa ya tafi sana'ar shi, Husna kuwa bayan ta gama duk wasu Æ´an ayyukanta, sai ta taho wajen Rahila suka hau hira sai wajen sha biyu na rana ta tafi domin ta É—ora abincin rana.
Wata rana bayan sallar Isha gaba É—ayansu sun haÉ—u a wajen Ammi suna ta hira, idan ka gan su a wannan lokacin sai kayi zaton family É—aya ne, idan ba'a faÉ—a maka ba. Anan ne Aisar ya shiga bai wa su Sa'ad labarin abin da yasa suka baro garinsu suka tahi Kano.
Ammi da Rahila sai da suka yi kuka sosai na tausayin su Inna, nan take kuwa Sa'ad ya ɗauki alƙawarin zai ɗauki nauyin Aisar har zama soja ya cika burin shi na ɗaukar fansa akan ƴanta'adda. Su Ammi kuwa mamaki suke yi da aka ce Aisar da Anas ba dangi ɗaya suke ba, amma idan ka gan su sai ka rantse dangi ɗaya suka fito.
****** **** *******
Washe gari yau ta kama monday, da sassafe Sa'ad yace "idan su Anas sun gama breakfast su shirya zai kai su makaranta. Murna a wajen Anas kuwa bata faɗuwa, saboda zumuɗi ya kasa cin abincin karyawar ma, Safna kuwa ita bata yin wata murna, don dama can a ƙauyensu bata yin makarantar Aisar ne kaɗai mai yi, shi yasa yake jin daɗi da aka ce yau za'a mayar da shi.
Nasreen ma sosai take murna yau za'a kaita makaranta, bayan sun gama karyawa Sa'ad ya É—auke su a motarsa ya nufi makarantar da su.
*ABIDDEEN NURSERY AND PRIMARY SCHOOL DARMANAWA* naga an rubuta jikin wata makaranta, me kyawun gaske horn yayi me gadin makarantar ya zo da gudunsa ya buÉ—e masa, sai da ya bincike motar tsaf sannan ya bar shi ya shiga ciki.
Bayan yayi parking ya buɗe musu suka fito gaba ɗayansu, riƙe hannunsu yayi suka nufi cikin makarantar. Wani masinja suka gani a zaune yana jin rediyo, ƙarasawa wajensa Sa'ad yayi, sallama yayi masa cike da kulawa ya amsa. "Don Allah malam ina ne ofishin shugaba makarantar nan? Sa'ad ya tambayi masinjan, tashi tsaye yayi yace ku biyo ni a baya.
A hankali suke bin sa har ya kawo su office É—in bayan ya nuna musu sannan ya juya yayi tafiyarsa. Da sallama suka cikin office É—in.
Tunda suka shiga cikin office ɗin, su Anas da Safna suke ta faman kalle-kalle, musamman ma hotunan da ke manne a jikin bangon office ɗin, suka fi mayar da hankalinsu akai.Hoton wani Soja ne sanye da kaki irin na jajurtattun sojojin nan, shine ya tafi da Anas can wata duniya, ya rinƙa jin sanyi a cikin zuciyar shi tare da fatan Allah yasa shi ma ya zama fiye da wannan sojan.
Shugaban makarantar yana zaune a wata kujera ta alfarma, gabansa ga wani tebur nan me girman gaske, ga takardunan masu yawa zube a kansa. Bayan su Sa'ad sun gama samun wajen zama, sai shugaban makarantar ya dube shi yace "Malam barka da zuwa" da fara'a Sa'ad ya amsa "barka dai yallaɓai, dama yara ne na kawo ko za su samu gurbin zama a wannan makarantar?"
Da fara'arsa yace "me zai hana? mu kullum burinmu ai shine mu ga ana ta kawo mana ɗalibai ko da yaushe mu kuma muna karɓewa" ya karashen maganar da salon zolaya, murmushi Sa'ad yayi yace "masha Allah to ga ƴaƴana nan suma a ba su aji."
Kallon Anas shugaban makarantar yayi yace "ɗan samari ya sunanka?" cikin sanyin murya Anas yace "sunana *ANAS ABDUL MALEEK* masha Allah shine abin da shugaban makarantar ya faɗa, sannan ya rubuta a jikin wata paper, ya sake duban Anas yace "ka taɓa yin makaranta?" "E na taɓa yi a can kauyenmu" good ajinka nawa a can kauyen naku? Ajina huɗu zamu shiga na biyar shine muka baro kauyen.
"Masha Allah yanzu ka iya karatu da rubutu?" "E na iya" ɗauko wata farar paper yayi ya ajiye akan desk ɗin da yake gabansa yace Anas ya rubuta masa A, B, C, D, cike da nutsuwa ya rinƙa rubuta masa har ya gama tsaf. "Good hand writing" shine abin da shugaban makarantar ya faɗa, sannan yace ya rubuta masa sunansa nan ma ya ga Anas ba baya bane, wajen iya rubutu, da karatu, anan dai yayi ta faɗo masa sunayen abubuwa da turanci yana rubuta masa, ko kuskure ɗaya bai yi ba.
Sosai Anas ya burge shugaban makarantar da Sa'ad, tun da aka fara yi wa Anas screaning ya ke ta faman murmushi, nan take ya ji yana alfahari, ya rinƙa jin sa tamkar ɗansa na jini.
Kallon Sa'ad shugaban makarantar yayi yace "hakika na yaba da kokarin Anas Abdul Maleek, don haka naga yafi dacewa da primary six (class 6) anan zamu saka shi, shekara tana kewayowa sai su zana jarrabawar common interest ya shiga secondary school.
Murmushi Sa'ad yayi yace "haka yayi wallahi ni ban yi zaton kokarinsa ya kai har haka ba."
sannan ya dubi Safna da Basma yace "yan mata ku kuma ya sunanku?" Safna ce ta fara cewa "Ni sunana Safnatu Abdul Maleek" ƴar dariya shugaban makarantar yayi yace *"Safnat za ki ce ba Safnatu ba kin ji ƴan mata?"* girgiza kai tayi tace "to malam" sannan yayi mata wasu ƴan tambayoyi har dai ya gane ita ba ta taɓa shiga aji ba Nasreen ma dai ba ta taɓa shiga aji ba saboda Aisar yana niyyar kai ta makarantar sai kuma suka bar garin, haka ne yasa ba'a samu damar kai ta ba sai a birnin Kano Allah yasa za'a kaita, Basma kuwa mahaifinta yana kusa bai bari ma an yi wasu tambayoyi ba, yace "yau ya fara kawo ta makaranta".
Nan dai bayan an gama abin da za'a yi aka kai kowa ajinsa Anas shi aka kai shi class 6 Safna da Nasreen da Basma aka kai su primary 1 a cewar shugaban makarantar sun yi girma a nursery.
Nan take Sa'ad ya biya kudinsu gaba daya, aka damkawa kowanensu uniform da littattafai na karatu da na rubutu dai-dai ajinsu, sannan yace tomorrow su fara zuwa makaranta......
To be continue.........
Comment and share
Hussaini Yusuf
07069475482.
[12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*
*NA*
*HUSSAIN YUSUF*
*_______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*______________________________*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.