Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 22 of 25
*Page 43/44*
Ammar yana gano mahaifinsa, ya kama mutsu-mutsu dole Lami ta yarda ta sauke shi, aikuwa tana sauke shi ya tafi da gudu wajen Mahaifinsa. Shi ma kuwa da ɗan gudunsa ya zo ya rungume ɗan nasa a ƙirjinsa, yana jin wata ƙaunarsa tana ratsa sassan jikinsa. Ɗaukar shi yayi ya nufi inda yake zaune, ya zauna ya zaunar da Ammar ɗin akan cinyarsa, dai-dai lokacin Lami ta ƙaraso wajen har ƙasa ta durƙusa ta gaisar da Alhaji fuska a sake ya amsa mata. Ajiye abincin ta yi ta ce "Abban Ammar abinci ne na kawo muku" murmushi yayi ya ce "Haba Lami da kin bar abincin nan yanzu ba tashi muke yi ba, har yanzu ban san a halin da Amina ƴar Aljanna take ciki ba" tsinkayo muryar Ammar suka yi yana cewa "Daddy ina Ummata take?" Kafin Daddy ya bashi amsa sai ga wata nurse ta zo a gigice ta dubi Daddy ta ce "Kai ne mijin waccan marar lafiyar wacce aka yiwa operat........Kafin ta ƙarasa ya riga ta ya ce "E nine, to kayi sauri ka zo tana son ganin......" Ai kafin ta ƙarasa ya ɗauki Ammar yayi cikin ɗauki da gudu. Cikin sanyin jiki Lami ta bi bayansu zuwa cikin ɗakin, a kwance take akan gado idan ka ganta baza kayi zaton tana tare da numfashinta ba, bata iya yin ƙwaƙƙwaran motsi ko hannunta ba ta iya ɗagawa.
Da kyar da siɗin goshi ta juyo da kanta ta fuskanci mijinta da ɗanta, da suka daɗe a tsaye suna kallonta, wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo daga cikin shanyayyun idanunta, cikin ƙarfin hali ta miƙo hannu alamun ɗanta Ammar ya je kusa da ita, da sauri Alhaji Abubakar ya miƙa shi, ƙaƙalo wani murmushi ta yi ta shafa kansa ta ce "Allah yayi maka albarka Ammar, Allah ya raya ka cikin Addinin Musulunci". Sannan ta juyar da idanunta akan mijinta, da ya ƙura mata idanu ya kasa furta ko da kalma ɗaya ne, ya tafi can wata duniya daban ta tunani, tun da ya ga matarsa a cikin wannan halin gaba ɗaya ya nemi nutsuwarsa ya rasa, tunani ne kala-kala suka cika masa rai, ba ya so ya rabu da matarsa abar alfaharinsa, mace ɗaya tamkar da dubu tun da ya aureta ba ta taɓa ɓata masa rai ba, idan ma ta yi masa wani abun da ransa bai so ba, idan ta kalli fuskarsa ta ga alamun bai ji daɗin abin da ta yi masa ba, to nan take ba shi haƙuri hankalinta ba ya kwanciya har sai ta gan shi ya dawo cikin nishaɗi da walwala.
Muryarta ce ta dawo da shi daga can wata duniyar da ya tafi, "Alhaji don Allah ga Ammar nan na bar maka shi amana, ka kula min da shi ka yi ƙoƙari ka ba shi tarbiyya irin ta Addinin Musulunci, domin ni yanzu tawa ta ƙare na tabbatar ba zan tashi daga wannan ciwon ba." fashewa da kuka Alhaji Abubakar yayi tamkar wani ƙaramin yaro, Ammar ma ganin Daddinshi yana kuka sai shi ma ya fashe da kukan, aka rasa mai rarrashin wani a tsakaninsu.
Sunkuyawa Alhaji Abubakar yayi dai-dai fuskar Amina, hannayenta ya kamo ya riƙe su sosai. Sai faman matsa su yake yi, bakinsa yana ta motsi alamun magana yake son furtawa amma bakinsa yayi masa nauyi.
Cikin raunin murya ya fara magana yana ce wa "Haba Aminatu bai kamata zafin ciwo yasa ki rinƙa faɗin irin waɗannan kalaman ba." "Ki sani cuta ba mutuwa ba ce sai kwana ya ƙare, ke kuwa na ki kwanan bai ƙare ba.
Hawaye ne ya zubo daga idanunta, da ƙyar ta iya buɗar baki ta ce "Don Allah mijina ka kula min da ɗana ka riƙe duk abin da na faɗa mak......"
Tana kai wa nan muryarta ta sarƙe, ta kasa cigaba da furta kalma ɗaya sai Kalimatush-shahada kaɗai Allah ya bata ikon furtawa. Tana kammala biyawa kuwa tace "Ga garinku nan".
Da gudu Alhaji Abubakar ya tafi kiran likita, ba su wani dogon lokaci ba sai ga su sun shigo a tare. Likita yana ƙarasawa kanta, ya ji jikinsa yayi sanyi. ɗaga hannunta yayi ya ga ya dawo, bayan ya gama aune-aunen da zai yi ya gama sai ya ja mayafi ya rufe mata fuskarta.
Ya juyo ya kalli Alhaji Abubakar ya ce "Alhaji sai dai haƙuri fa domin Amina ta riga mu gidan gaskiya" Tashin hankali......Wanda ba'a saka masa rana. Zubewa Alhaji Abubakar yayi a wajen, yana ta wani irin haki abin tausayi. Da sauri likita ya riƙe shi ya buɗa fridge ya ɗauko ruwa ya bashi kaɗan ya kurɓa sannan ya ji zuciyarsa ta fara yi masa sanyi.
Da kyar ya samu ya rarrafa kan gawar Aminar, rungume ta yayi ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Ammar ma da yake yaro bai san komai ba a lokacin, ganin mahaifinshi yana kuka shi ma sai ya rushe da kuka.
Da kyar likita ya rarrashi Alhaji ya daina kukan. Wayarsa ya ɗauko daga cikin aljihu, ya kira ƴan'uwa da abokan arziƙi ya sanar da su rasuwar Amina. Kowa idan ya samu labarin sai ya girgiza, saboda Amina mace ce mutunci da kima a wajen mijinta da dukkan wanda ya santa. Tana da hali mai kyau, babu ruwanta da shiga abin da bai shafe ta ba, iyakar kyautatawa tana yi wa mijinta shi yasa yake jin ba zai taɓa samun kamarta ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka yi mata wanka da sallah. Aka ɗauketa aka kaita gidanta na gaskita, ya Allah ka sa mu cika da imani don alfarmar Annabinka sallallahu alaihi wasallam.
Bayan rasuwar Amina Alhaji ya sa a ranshi, ba zai sake yin aure ba har sai Ammar ya girma ya mallaki hankalin kansa. Babu yadda ƴan'uwansa ba su yi masa ba, akan ya ƙara aure amma ya ce musu ba yanzu ba. Sai Ammar ya girma domin ba ya son ya je ya auro wacce za ta wahalar masa da tilon ɗansa Ammar. Tun Ammar yana yaro yake da burin zama soja, kullum idan suka zauna shi da mahaifinsa ban da zancen sojoji babu abin da yake yi masa. Shi kuwa ya ɗauki wannan buri na ɗansa ya sanya a ransa da ƙudurin sai ya cika masa shi.
Wannan shine labarin Ammar abokin Anas.
CIGABAN LABARI
Shirye-shirye su Anas suke yi sosai, Aisar da kansa ya shiga kasuwa yayi ta siyowa su Anas abubuwan da ya kamata ya tafi da su.
Da ranar tafiya ta zo, Inna har kuka ta saka. Ji take kamar kar ta bar Anas ya tafi, tana matuƙar son su shi da Safna fiye da kowa a rayuwarta. Aisar ma ji yayi duk duniyar babu daɗi domin ya shaƙu da Anas shaƙuwa mai tsanani.Nasiha mai ratsa jiki Inna da Aisar suka yi masa har ma da Sa'ad sai da yayi masa tasa nasihar.
Gaba É—ayansu suka É—unguma suka tafi raka shi gidan Alhaji Abubakar, suna zuwa kuwa suka iske har Ammar É—in ya gama shiryawa yana zaune Alhaji Abubakar yana ta yi masa nasiha da jan hankali.
Bayan Daddy ya gama yi wa Ammar tasa nasihar, da kansa ya ja hannunsu shi da Anas. Bakin wata mota suka zo suka tsaya, da gudu wani direba ya zo ya buÉ—e musu suka shiga.
Sannan ya nunawa su Aisar wata motar, suka shiga wani direba ya zo ya ja suka tafi. AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT suka nufa kai tsaye. cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka isa, bayan sun yi parking kowa ya fito.
Inna ce ta kirawo Anas yana zuwa kusa da ita, kallon shi ta yi, ta kasa magana. Wuf ta yi ta rungumeshi ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Da kyar ya samu Inna ta sake shi, aikuwa tana sakinshi ya É—auki jakarsa ya nufi inda jirgin yake a ajiye.
Tunda Alhaji Abubakar ya ƙyalla idanu ya ga Inna, nan take ya ji ta burge shi, cikin salo da dabara ya tambayi Aisar ya ce "Waccan ita ce mahaifiyar Anas?" Amsa masa Aisar yayi, nan ya shiga ba shi labarin haɗuwarsu da Anas da kuma ita Innar tasu.
Bayan su Anas sun gama shiga cikin jirgin, ba tare da ɓata lokaci ba ya tashi ya nufi Kaduna. Su Anas kuwa sai murna ake yau za'a shiga NIGERIAN DEFENCE ACADEMY (N.D.A) cikin kankanin lokaci suka isa nan Kadunar. Neman mai taxi suka yi, ya ɗauke su ya kai su cikin makarantar.
Daddy kuwa tun da ya koma gida, tunanin Inna ne ya hana shi sukuni. Tabbas ya ji zuciyarsa ta gamsu da halayen Inna, yadda ya ga ta rungume ɗanta tana kuka ya san idan ya aureta baza ta wulaƙanta masa Ammar ba.
Kasa daurewa yayi, ya ɗauki waya ya kira Aisar ya ce "Ya zo gida ya same shi za su yi wata magana mai muhimmanci." Ba tare da ɓata wani lokaci ba, Aisar ya nufi gidan Alhaji Abubakar, yana zuwa kuwa ya buɗe ya shiga mai gadi bai yi yunƙurin hana shi saboda har sun yi sabo a ɗan zuwan da yake yi.
A wani ƙayataccen falo ya samu Alhaji Abubakar a zaune, yana kurɓar juice a cikin kofi. Sallama yayi masa sannan ya samu wuri a ƙasa ya zauna, da sauri Alhaji Abubakar ya ce "A'a tashi mana ka dawo kan kujera".
Tashi Aisar yayi ya koma kan kujerar ya zauna yana mai fuskantar Alhaji Abubakar, wani É—an murmushi ya saki ya ce "Aisaru wata muhimmiyar magana za mu yi ni da kai, shi yasa na kirawo ka." Gyara zama Aisar yayi ya ce "To Alhaji ina sauraronka" gyaran murya yayi kafin ya fara ce wa "Aisaru ya sunan mahaifiyar Anas?" murmushi Aisar yayi ya ce "Alhaji sunanta Saratu amma muna kiranta da Inna."
Murmushi Alhaji Abubakar yayi ya ce "Masha Allah" sannan ya cigaba da ce wa "Maganar gaskiya Aisaru ba zan ɓoye maka ba, daga lokacin da naga wannan matar na ji ina son ta kasance a matsayin matata."
Murmushi Aisar yayi ya ce "Amma na ji daÉ—i sosai Alhaji amma kafin nan ta ina kake son na taimaka maka?"
"Yawwa Aisaru an zo dai-dai wajen da nake so, yanzu so nake ka shawo min kanta ta amince da ni kafin na fara zuwa wajenta mu fahimci juna."
"Indai wannan ne Alhaji ba ka da damuwa, yau ɗin nan insha Allahu zan isar mata da saƙonka mu ji yadda za ta amshe shi." Da sauri Alhaji Abubakar ya ce "Yawwa Aisar ka daure ka faɗa mata mu ji yadda zata amshi wannan ƙudurin nawa."
"Baka da damuwa Alhaji zan faɗa mata duk yadda muka yi da ita zan sanar da kai ta waya" miƙewa Aisar yayi ya ce "Alhaji ni zan koma" godiya sosai Alhaji Abubakar ya rinƙa yi wa Aisar kamar wanda ya ba shi wata gagarumar kyauta.
A hanya kuwa Aisar sai faman tunanin yadda zai tunkari Inna da wannan labarin yake yi. Domin yana matuƙar jin kunyarta da nauyinta don haka kawai ya yanke shawarar zai sanar da Iya sai ta sanar da ita.
Su Safna da Nasreen da Basma da suka dawo daga makaranta aka shaida musu Anas ya tafi makarantar horon sojoji. Safna da Nasreen wuni suka yi suna kuka, Basma ce ma ta saki ranta don bata yi wani sabo mai yawa da Anas ba.
Haka suka ƙari ƙuncinsu suka gama, har kewar Anas ɗin ta sake su sosai suka saki ransu, sai kuma suka hau lissafin kwanakin tafiyar Anas.
Da dare yayi Aisar ya je har ɗakin Iya, ya sanar da ita saƙon Alhaji Abubakar, ya roƙi da ta sanar da Inna idan ya so da safe sai ta sanar da shi amsar da ita Innar ta bayar. Yana gama faɗa mata ya tashi ya fita, yana fitowa sai ga Inna ta fito daga banɗaki, gaisar da ita Aisar yayi sannan ya nufi ɗakin Ummu Nasreen.
Inna tana shiga ta tarar da Iya tana shirin kwanciya, fasa kwanciyar ta yi ta ce "Saratu zo nan ina son magana da ke" zuwa ta yi kusa da Inna ta zauna tana mai fuskantar ta. Gyara zama Iya ta yi ta ce "Saratu a yanzu idan ki ka samu miji zaki yi aure kuwa?"
DuÆ™ar da kai Inna ta yi tayi shiru............âœðŸ»
To be continue.......ðŸ“ðŸ“ðŸ“
*Hussaini Yusufâœï¸*
[12/9, 4:38 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*
*NA*
*HUSSAINI YUSUF*
*_______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*______________________________*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.