Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 4 of 25
*___________________________*
Page 7&8
Duk gudun da Inna take yi, domin ta tarar da su, Allah bai ba su ikon jiyo ko da takunta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci Inna ta tarar da su, yayin da ta zo daf da su, sai ta ɗaga wannan sharɓeɓiyar wuƙar ta caka wa ɗayan mutumin a ciki, ta zaro ta ta sake caka masa.
Nan take kuwa jini ya rinƙa fallatsi daga jikinshi, hancinsa da kunnuwansa suka rinƙa zubar da jini take ya sulale ƙasa matacce, idanunsa ƙur! akan Inna har ransa ya ƙarasa fita, daga gangar jikinsa. Mamaki ne ya hana ɗayan motsi, saboda bai taɓa ganin mace irin Inna ba.
anƴa kuwa wannan mutum ce? ya tambayi zuciyarsa, take kuwa yace "kai wannan ba mutum ba ce" shi dai a iya saninsa da mata ko da sanda ba sa iya riƙewa ballantana kuma har ta kai su da kisa.
Yana cikin tunaninsa ya ga Inna ta yo, kansa gadan-gadan da wuƙa a hannunta, sai ya ɗimauce ya zaro wata ƴar ƙaramar bindiga pistol daga aljihunsa ya saita Inna ya harba
ƙin bindigar ta yi, babi harsashi ko ɗaya a ciki ballantana har ya harbi wani.
Tuno wa yayi ashe babu harsashi a ciki, ɗazu ya ƙarar da shi wajen harbe wani mutum, bai ankara ba ya ji har Inna ta samu nasarar yankar shi a gefen wuyansa, kafin ya ƙara wani ƙwaƙƙwaran motsi ta caka masa wuƙar a kan cinyarsa, ta hagu.
Wani uban ihu ya tsadara, dai-dai lokacin wasu ƴanta'addan sun ƙaraso wajen, ganin ogan na su suka yi a cikin jini male-male. Can nesa kuma suka hango Inna tana ta faman gudu domin tseratar da rayuwarta, daga hannun mugayen ƴanta'addan nan.
Mamaki ne ya cika musu zuciya "wai mace ce ta yiwa ogansu wannan mummunan raunin, kuma ta kashe Saiham gaskiya wannan matar ta cika jarumar gaske, domin a iya zamansu da Sa'eed bn Abdul'aziz babu wanda ya taɓa ko da lakutar fatar jikinsa da sunan cutar da shi amma sai ga shi yau mace ce ta kai shi ƙasa.
Suna cikin tunaninsu suka tsinkayo muryarsa yana cewa " ku bita sannan ku tabbatar kun kamo min ita a raye domin nasan irin hukuncin da zan yanke mata, take kuwa suka bi bayan Inna wasu akan mashina wasu kuma a ƙasa, suna ihu da ƙaraji irin na mugayen ƴanta'adda.
Wasu ne suka yi sauri suka É—auke Sa'eed suka É—ora shi mashin, suka tafi da shi don su yi masa magani.
Anas da Safna sai tafiya suke yi a tsakiyar dokar daji, hannun Anas ɗauke da wannan jaririn da suka tsinta, Safna ce ta faɗi ƙasa tana kiran ruwa! ruwa!! ruwa!!! shi ma jaririn sai tsala wani uban kuka yake, da alama shi ma ruwan yake so.
Tsugunna wa Anas yayi a gaban Safna yana ta faman rarrashin jaririn domin yayi shiru amma ya ƙi daina kukan, kallon Safna yayi yace "Safna ki taso mu ƙara yin gaba wataƙila za mu iya riskar wani ƙauyen a nan gaba, ko kuma mu tarar da wani kogin, sai mu sha ruwan anan."
Inna sai faman gudu take yi, ta cikin ƙayoyi, ƙafafunta ko takalmi babu, ƙayoyin sai faman soke mata ƙafafu suke yi. Amma ko kaɗan bata damu da hakan ba, domin burinta kawai ta tseratar da rayuwarta, duk lokacin da ta saiga bayanta sai ta ga ba su daina binta ba, wasu akan mashina wasu kuma a ƙasa duk inda ta kutsa kai sai sun kutsa.
Wata duhuwa ta shige, a cikinsu babu wanda ya ga shigarta cikin duhuwar, tana shiga duhuwar bisa mamakinta sai ta ga wata siririyar hanƴa kuma da alama mutane suna bin hanƴar, domin duk ga sawun ƙofatan dabbobi nan, ga kuma sawun takalma nan birjik ko'ina.
Waigawa ta yi bayanta ta ga, mutanen ba sa biye da ita, wani farinciki ne ya ziyarceta take ta fara ɗingisa ƙafar tafiya don sai yanzu take jin zafin ƙayoyin da sossoketa.
Sai da ta shafe awa ɗaya da rabi tana tafiya akan hanƴar sannan ta hango wani ƙaramin ƙauye a jikin wani ƙaton tsauni.
Murmushin farinciki ta yi, sannan ta cigaba da tafiya, tana isa ƙauyen kowa hankalinsa ya dawo kanta, tana zuwa bakin wata rijiya ta ga mata da yara sai ɗiban ruwa suke yi, a rijiyar.
Bata yiwa kowa magana ba, ta tsaya tana ƙarewa mutanen ƙauyen kallo, zubewa ƙasa ta yi bisa gwiwoyinta.
A hankali take kiran ruwa! ruwa!! ruwa!!! wani tsoho ne ya kalli ƴan'matan da suke ɗiban ruwan ya daka musu tsawa yace "ba za ku taimaka mata da ruwan ba ne?" Nan take suka miƙo mata ruwan a cikin wani ƙoƙo mai ɗan girma.
Tunda ta kafa kai a ƙoƙon ruwan, bata ɗaga ba sai da ta ga ya ƙare, sannan ta miƙa musu ƙoƙon tana ta faman sauke ajiyar zuciya.
Wata tsohuwa ce ta zo ta kama hannunta tace "taso mu je gidan me gari kiyi masa bayanin inda kika fito babu musu kuwa Inna ta tashi ta bi tsohuwar a baya.
Lokacin da su Inna suka isa gidan me gari, tarar wa suka ana ta faman fadanci, tsugunnawa tsohuwar ta yi ta kwashi gaisuwa, Inna ma ta yi koyi da ita, suka gaishe da megarin a tare.
Tsohuwar ce ta yiwa me gari bayanin inda ta ga wannan baƙuwar matar wato Inna, me gari ne ya buƙaci Inna ta faɗa masa inda ta fito.
Tana zubar da hawaye ta faɗa masa komai, hatta su Anas ƴaƴanta da ta tura su, su tafi domin su tseratar da rayuwarsu bata ɓoye musu ba.
Gaba ɗaya jama'ar fadar sun tausayawa Inna, me garine da kansa ya umarci tsohuwar da ta tafi da Inna gidanta tunda ya lura kamar akwai shaƙuwa a tsakaninsu.
Tsohuwa da murnarta ta kama hannun Inna suka nufi gidanta, dama ita kaÉ—ai ce a gidan, yanzu ta samu abokiyar zama.
******
Al'amarin su Anas da Safna kuwa yayin da suka ci gaba da tafiya a wannan ƙungurmin dajin, suna ta neman ruwa amma ko alamun sa babu.
Faɗuwa ƙasa Safna ta yi ta saki wani uban kuka mai karyar da zuciyar mai sauraro, wani gurnani suka rinƙa jiyowa yana kusanto inda suke, firgita suka yi gaba ɗayansu suna zazzare idanu.
Gaba ɗaya sun ƙurawa inda suke jiyo gurnanin ido, a hankali suka rinƙa jiyo gurnanin yana kusanto su, babu wanda ya furta koda kalma ɗaya ballanta su samu damar guduwa daga wajen.
Wani ƙaton murjejen zaki ne ya fito daga wata duhuwa, da kallonsa yunwa ce ta fito da shi daga maɓoyarsa.
Kalle-kalle yake yi, yana bin ko'ina na dajin da kallo, karaf idanunsa suka sauka akan Anas da Safna, take kuwa yace "da wa Allah ya haÉ—a ni ba da ku ba?"
Cikin wani irin gudu ya yo kansu domin ya hallaka su gaba ɗayansu, tsugunnawa ƙasa suka yi, suka rufe idanunsu suna jiran zakin ya afko musu, can gefe ɗaya kuma sun ajiye jaririn yana ta faman tsala kuka, kamar ana mintsinin shi a jiki.
Kwatsam! ba zato ba tsammani suka ji ƙarar faɗuwar zakin, can waje ɗaya, da mamaki a idanunsu suka ɗago kawunansu suka ga zakin ya ƙurawa wani lungu idanu.
Gani suka yi zakin ya ja da baya, sannan ya nufi cikin lungun da mugun nufi, gani suka yi an sake wurgo shi waje, mamaki ne ya cika musu rai.
Waye wannan yake bugo zakin nan haka? ki kuma da aljanu yake faÉ—a? gani suka an cillo wani mashi mai tsinin gaske daga cikin lungun.
Mashin bai tsaya a ko'ina ba, sai a jikin wannan murjejen zakin, nan take kuwa ya sulale ƙasa matacce jini yana fallatsa daga jikinshi.
Ƙarar tafiya suka jiyo, daga cikin lungun duhuwar, ƙurawa wajen idanu suka yi domin su ga wanda zai fito daga wajen.
Hussain YusufâœÂï¸Â
[12/9, 4:32 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ðŸ«Â🫠ANAS MALEEKðŸ«ÂðŸ«Â*
Labari/Tsarawa
HUSSAINI YUSUF
My Whatsapp number
07069475482
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.