Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 24 of 25

*Page 47/48*

Bayan ya shiga cikin É—akin, sai ya ga komai tsaf-tsaf, komai na É—akin sabo ne har da air condition, ga wani tamfatsetsen gado a shimfiÉ—e a É—akin. A hankali ya zo ya buÉ—e haÉ—aÉ—É—iyar wardrobe É—in da ya gani a manne jikin bangon É—akin, kaya ya gani dai-dai shi, an shirya su tsaf cikin wardrobe É—in. rufe ta yayi ya dawo gefen gadon ya zauna, tunani ne kala-kala ya cika masa zuciya, to "A ina su Aisar suka samu kuÉ—i har suka gina irin wannan gida haka?" Shi kaÉ—ai yake yi wa kansa wannan tambayar, amma ba shi da amsarta dole sai wajen su Aisar É—in zai ji komai.

Ganin wankin hula yana niyyar kai shi dare, sai ya tashi ya nufi toilet ɗin da ya gani a cikin ɗakin. A hankali ya buɗe ya shiga, "Masha Allah" shine abin da ji ya faɗa, a hankali ya rufe ƙofar bathroom ɗin, sannan ya shiga yin wanka, wani daɗi ne yake ratsa jikinsa jin sa yake tamkar an yaye masa duk wata damuwarsa. Bayan ya gama wankan, sai ya ɗauki ɗaya daga cikin tawul ɗin da ya gani a cikin banɗakin ya ɗaura shi ya ɗauki wani kuma yana tsane ruwan jikinsa.

A jikin wani irin dressing mirror ya tsaya, wanda ban taɓa ganin irinsa ba a rayuwata. Kayan shafe-shafe ne sun fi gaban a ƙirga, ga perfumes nan wajen kala ashirin sai wanda ya ga damar zaɓa. Just vasselin ya shafa, sannan ya buɗe wardrobe ɗin ya ɗauko wata baƙar jallabiya ya sanyata a jikinsa. Wow! ba ƙaramin kyau Anas yayi ba a cikin rigar nan, zuwa yayi ya zauna a gefen gado ya shiga tunani, nan da nan tunaninta ya faɗo masa. Shi kaɗai ya rinƙa sakin murmushi, tamkar gonar auduga yadda ta haɗe ranta ba ƙaramin burge shi ta yi ba. A ransa ya saka kafin ya koma bakin aiki sai ya bayyana soyayyarsa a gareta, ko da baza ta amince da shi ba.

Kamar an tsikare shi ya tashi ya fita daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Inna ya nufa. Tarar da ita yayi ta idar da sallah tana shirin kwanciya, ganin Anas ya shigo sai ta fasa kwanciyar ta zauna a gefen gado, shi kuma Anas ya zauna a ƙasa. Cike da ladabi ya sake gaisheta, ita ma da nuna kulawa irin ta uwa ta amsa masa gaisuwar tana mai shafa kansa tana sakin wani tattausan murmushi. Shi ma ban da sakin murmushin babu abin da yake yi, domin babu abin da ya fi so a duniya fiye da ya ga mahaifiyarsa a cikin walwala da farinciki.

Ƙasa-ƙasa yayi da muryarsa ya ce "Inna wai a ina ku ka samu kuɗin da har kuka gina wannan katafaren gidan?" Dariya Inna ta yi ta ce "Ka kwantar da hankalinka ba Baffanka ya ce da safe zai sanar da kai komai ba? To ka jira safiyar mana idan Allah ya kai mu." Ba ta jira abin da zai ce ba ta cigaba da magana "Ni kuwa Anas akwai maganar da nake son mu yi ni da kai, dama ina son a kirawo min kai kafin ka kwanta. Amma sai na yi tunanin ka gaji, sai na bar ka ka huta, idan Allah ya so da safe muyi maganar, amma tun da ga shi ka shigo shikenan sai muyi maganar ta mu.

Gyara zama Anas yayi ya ce "Ina sauraronki Inna" murmushi ta yi ta ce "Ta so ka dawo nan kusa da ni sai ka fi fahimtata" tashi yayi ya koma kusa da ita ya zauna yana mai fuskantarta. "Tun bayan da ka tafi neman aikin soja, Alhaji Abubakar yake ta yi min aike wai yana son ya aure ni domin yana da yaƙinin zan iya riƙe masa Ammar na kula masa da shi. Na bashi taimakon da duk wata uwa take bai wa ɗanta, kuma ya ce idan na aure shi sai na haɗa da ku da Ammar ɗin na riƙe ku, ni na zama tamkar mahaifiyar Ammar da ta rasu tun yana yaro. Shi kuma ya zama tamkar mahaifinku da kuka rasa.

Kullum idan ya aiko min haka nake faɗa masa, sai ka dawo na yi shawara da kai, tun da hankalinka ya kai a saurare ka a ji ra'ayinka a cikin wannan magana. Shiru Anas yayi ya ɗaga kansa sama yana tunani, sai da Inna ta dafa shi, kamar an soka masa allura ya dawo hayyacinsa. Duban Inna yayi ya ce "Inna a iyakar sani na ba mu daɗe da rasa Baffa ba, muka samu madadinsa" da sauri Inna ta gyaɗa kai alamar gamsuwa da maganar Anas cigaba yayi da ce wa "Baffa Aisar shi ya zamar mana kamar Baffanmu da muka rasa, akanmu ya rabu da garinsu, akanmu aka ci masa mutunci aka nemi ya mayar da mu inda ya tsinto mu ko kuma ya bar garin, amma ya zaɓi barin garin akan ya mayar da mu inda ya same mu." Ban da hawaye da yake zuba a idanun Inna babu abin da take, domin ta tuno irin wahalar da suka sha kafin su baro ƙauyen nan da yake yankin Mambila a can Jahar Taraba.

Muryar Anas ce ta doki dodon kunnenta, in da yake ce wa "Inna ni a gani na babu wani uba da zamu samu bayan Baffanmu fiye da Baffa Aisar" shiru Inna ta yi tana nazarin maganar Anas tabbas gaskiya ya faɗa ita bata taɓa yin wannan tunanin ba ma, nan take ta shiga mamakin kaifin hankali gami da hangen nesa irin na Anas. Cigaba yayi da ce wa "Inna ke kin sani da a ce Baffa Aisar yana da damar kai ni makarantar horon sojoji, ba zai taɓa barin Abban Ammar ya kai ni ba, da kansa zai so ya kaini." Da sauri Inna ta girgiza kai alamar gamsuwa har yanzu ta kasa magana saboda a baya duk ba ta yi wannan tunanin ba, sai yanzu da Anas ya ankarar da ita sannan ta gane irin halaccin da Aisar yayi musu a rayuwa.

"Haka Inna idan muka duba Daddin Ammar yayi mana halacci a rayuwa, da bai kamata mu watsa masa ƙasa a ido ba" ita dai Inna ta yi shiru tana sauraren ɗan nata ta kasa furta ko da kalma ɗaya "Don haka Inna ni na amince ki auri Daddin Ammar, amma ke kaɗai zaki koma wajensa mu muna tare da Baffa Aisar, tun da shine ubanmu na ainihi bayan Baffanmu da ya mutu. Amma kafin ki sanar da shi ki fara faɗa wa Baffa Aisar mu ji shi kuma abin da zai ce akai" murmushi Inna ta yi ta ce "Haƙiƙa na daɗe ina nazari akan maganar auren nan amma ban taɓa yin kwatankwacin wannan tunanin da kayi yanzu ba."

"Amma game da maganar na sanar da Baffanka Aisar, ai tun kafin na sani ma shi ya rigani sani. Domin ta hannunsa saƙon ya iso gare ni, kuma shi ya rinƙa roƙona akan na amince da maganar auren, ni na ƙi amincewa na ce sai na yi shawara da kai na ji ta bakinka sannan na amince. Yanzu ka tashi ka je ka kwanta, idan Allah ya kai mu gobe zan sanar da su ce wa na amince da auren." Tashi Anas yayi ya ce "To Inna sai da safe" murmushi ta yi ta ce "Allah ya kai mu" sannan ya fice tare da jawo ƙyauren ɗakin.

Tun da ya je ya kwanta tunaninta ya sake faÉ—o masa a rai, Allah-Allah yake gari ya waye domin yayi tozali da kyakkyawar fuskarta, mai sanyaya masa zuciya, nan take kuma ya koma tunanin hanyar da zai bi domin sanar da ita muradin zuciyarsa, amma sam ya rasa da wannan tunanin barci yayi gaba da shi.

*WASHE GARI*

Misalin ƙarfe 8:30am kowa ya hallara a dining area, abincine kala-kala sai wanda mutum ya zaɓa sannan zai ci. Dubawa Aisar yayi bai ga Anas ba, nan ya tashi Basma ya ce ta je ta kira wo shi yayi break fast. Fuskarta a murtuƙe ta tashi ta nufi ɗakinsa, domin ko kaɗan Basma ba ta son abin da zai haɗa ta da Anas ko kaɗan, kwata-kwata ba ta son haɗa wata mu'amala da shi, amma yanzu wai a rasa wanda za'a tura kiranshi sai ni kaɗai?" A hankali ta tura ƙofar ɗakin, shi kuma Anas lokacin ya fito daga bathroom yana tsane jikinsa da wani ɗan ƙaramin tawul, ji yayi an shigo ɗakin ba tare da neman izini ba.
Da sauri ya waiga domin ya ga wanda ya shigo, numfashinsa ne ya nemi É—aukewa yayin da yayi tozali da kyakkyawar fuskarta, mai É—auke da wani haske mai sanyaya zuciya, dara-daran idanuwanta da dogon hancinta da kyawun dirin da Allah ya bata sune suka fi ruÉ—ar shi ya ji tamkar Basma ta kasance tauraruwar Æ´an'mata ko kuma kai tsaye za'a iya kiranta da autar mata, saboda irinsu kaÉ—an ne a cikin al'umarmu ta Hausawa.

Yayin da ta gama buɗe kyauren ɗakin sai ta koma da sauri saboda tun da take a rayuwarta bata taɓa ganin namiji a haka babu riga a jikinsa ba. Murtuƙe fuska yayi cikin dakakkiyar murya ya kira ta "Ke zo nan" kamar kar ta koma haka zuciyarta ta rinka raya mata, amma da ta tuno irin muguntar da yake yi musu tun kafin ya tafi soja, to yanzu da ya dawo muguntar ai sai ta ninka ta da, tana gama wannan tunanin ta kutsa kanta cikin ɗakin.
Kanta a sunkuye ta ƙarasa shiga ciki, tana ta faman wasa da ƴan yatsun hannunta, murtuƙe fuska yayi kamar ba shi ba ya ce "Me ya kawo ki ɗakina?" cikin harɗewar harshe ta fara magana "Dam....dam...dama me min tsaya kina wani Kame-kame" da sauri ta ce "Dama haka aka ce na kirawo ka ka zo ayi breakfast" tana gama faɗar haka ta juya da sauri ta bar cikin ɗakin tare da jawo murfin da ƙarfi, alamun ranta ya ɓaci.

Bayan ya gama shiryawa ya ɗauko wata dakakkiyar shadda fara ya sanya ta a jikinsa, ba ƙaramin kyau Anas yayi ba dama ga shi asalin bafulatanin Mambila. Ya ɗauko wani agogo mai tsadar gaske ya ɗaura shi a tsintsinyar hannunsa na dama, sannan ya ɗauko wasu zobuna masu ɗan karan kyau da tsada ya zura su a zara-zaran yatsunsa, buɗe wardrobe ɗin cikin ɗakin yayi ya ɗauko wata hula kalar milk, ya ɗorata akansa wow! ba ƙaramin kyau Anas yayi ba sai ma kun gan shi musamman mata sai kun ƙyasa wallahi lol.
A hankali ya buɗe ƙofar falon ya fito, ɗaya bayan ɗaya yake take stairs ɗin kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, ko kuma kamar wanda tafiya take wahalarwa. Yana ƙarasowa cikin falon, sai ya hango su a wani keɓantaccen waje wanda iya wani dogon dining table ne a wajen a jera abinci kusan kala goma, kowa sai dai ya zaɓi abin da zai ci hankalinsu kwance kowa sai faman zura lomarsa yake abinsa.
Samun ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye table ɗin yayi ya zauna, bayan ya gaishe da kowa a wajen, sannan su Safna da Nasreen har da Basma ma suka gaishe shi, Safna ce tayi saving na shi zaunawa yayi ya fara cin abincin har sai da ya ƙoshi.

Aisar ne yayi gyaran murya ya ce su Safna su tashi su shiga da ciki, babu musu kuwa su duka ukun suka tashi suka shiga, bayan sun tafi Aisar ya juyo ya kalli Anas ya ce "Yanzu zan faɗa maka dalilin da yasa ka gan mu a wannan ƙerarren gidan. Gyara zama Anas yayi ya ce "To Baffa ina sauraronka" numfasawa Aisar yayi sannan ya cigaba da cewa. "Bayan tafiyarka neman aikin soja, mahaifin Ammar ya nuna yana son auren mahaifiyarka, ita kuma ta ƙi amincewa ta ce "Har sai ka dawo ta ji ra'ayinka sannan ta amince."

Amma duk da haka mutumin nan bai daina yi mana hidima, da na faɗa masa sana'ar da nake yi ta sayar da gwanjo sai ya haɗa ni da wani babban dealer, ya ara mini kuɗi masu yawan gaske. Sannu a hankali kasuwancina ya rinƙa haɓaka, da ni da ke bai wa sarin kaya na dawo ni ne mai bayarwa, har na zo duk faɗin kasuwar Wambai babu inda ba'a sanni ba" "Na gina manyan shaguna na gani na faɗa, wasu ina kasa kayana wasu kuma na bayar da su haya ana kawo min balance ko wacce shekara."
Wata rana na je na saro kaya da yawa, na zo shago ina ta duddubawa kwatsam na ga wata ƴar madaidaiciyar jaka a ciki, ban yi wani jinkiri ba, na ɗauko ta ina dubawa kawai sai na ga dalolin kuɗi a ciki, a zatona ko me bamu kayanne yayi mantuwa amma sai na ga wata ƴar ƙaramar takarda ce wa "Zakka ce duk wanda ya samu rabonsa ne kuma halak ɗinsa ne" ai kuwa da sauri na ɗauki jakar na nufo gida da ita, da na nunawa Sa'ad ya ce "Wannan ba ƙananan kuɗi bane, nan da nan muka ɗebi kaɗan daga ciki muka je wajen canji, nan muka ga an bamu kuɗi masu yawan gaske wajen 30 million naira, nan muka shiga murna, da mamaki don ni ban taɓa ganin dala ba sai a wannan lokacin.

Nan da nan kuwa kasuwanci ya bunƙasa, a hankali muka rinƙa canjar da kuɗin, har suka ƙare mun samu kimanin naira biliyan ɗaya a kuɗin Najeriya. Yanzu haka ina da manyan shaguna da nake sayar da atamfofi da kayan sakawa a kasuwar kantin kwari.
Kuma kai ma na gina maka ƙaton mall na mallaka maka shi halak malak, kuma akwai wasu kuɗi da na tanadar maka, idan ka gama zama sojan zan baka su ka rinƙa ɗan taɓa kasuwanci. Kuma wannan gidan da kake gani da ribar
da na samu a shekara É—aya na gina shi, amma insha Allahu zan gina wanda ya fishi nan gaba kaÉ—an.

Numfasawa Anas yayi ya ce "Baffa haka Allah yake yin lamarinshi, idan ya soka da arziƙi yanzu ne zaka fi kowa, haka idan ya soka da talauci babu wanda ya isa ya fitar da kai daga ciki idan ba shi ba" "Wannan gaskiya ne Anas" cigaba Anas yayi da cewa "Amma Baffa shi kuma Baffa Sa'ad me ka yi masa?" murmushi Aisar yayi ya ce "Ai na gina masa ƙaton gida, a can unguwar Ƴar akwa kuma na bashi naira miliyan ɗari yayi jari, yanzu haka ma ya samu labarin dawowarka yana hanya zai zo ku gaisa......

Hussain Yusuf✍🏻
[12/9, 4:38 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*

*NA*
*HUSSAINI YUSUF*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu 'yancinmu*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.