Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 25 of 25

*Page 49/50*

Murmushi Anas yayi ya ce "Baffa da ka ce masa ma ya zauna sai na je har gidan nasa na gaida shi".
"Anas kenan ka san halin mutumin naka da gardama, wallahi sai da na faɗa masa haka amma furr ya ƙi amincewa lallai sai dai ya zo da kansa ya sameka, a cewarsa kada a wahalar da kai.

Kafin Anas ya furta wani abun suka ji sallamar Sa'ad ya shigo cikin falon, da gudu Aisar ya je ya tare shi yana ce wa "Baffana sannu da zuwa da ka bari ma ai sai na zo da kaina mu gaisa ba sai ka zo ba" murmushi Sa'ad yayi ya ce "Ai zuwan da nayi yanzu, don na matsu na ganka ne shi yasa, amma ai na san zaka zo inda nake Anas É—ina."

Dai-dai lokacin su Nasreen da Safna da kuma Basmah suka fito daga ɗakinsu, cikin shirin tafiya school. Basmah ce ta hango Abbanta da Momynta a zaune, da gudu ta ƙarasa wajensu ta rungume su tana tambayarsu yaushe suka zo.
Sa'ad ne ya daka mata tsawa ya ce "Ke har yanzu ba ki daina wannan rashin hankalin ba ko? Ko haka ki ka ga sauran Æ´an'uwanki sun yi?"
"Haba Sa'ad me kuma yarinyar nan ta yi fisabilillahi, murna fa take yi da ganinku amma sai ka hau ta da wannan faɗan kamar za ka dake ta?" Cewar Aisar yana mai jin haushin Sa'ad akan takurawa Basma da yake yi, shi yasa ma ta zaɓi ta zauna da su Safna don ta daina fuskantar faɗan da take sha a wajen mahaifinta. Kamar ba shine ya haifeta ba haka yake rufeta da faɗa kullum ita da gidansu bata da sukuni, wannan halayya ta Sa'ad tana matuƙar ɓatawa mahaifiyar Basma rai, musamman idan ta kalli yadda Aisar yake tarairaiyar su Safna da Nasreen sai ta ji ina ma a ce haka mijinta yake yi wa tilon ƴarsu Basma, da ta fi kowa farinciki da jin daɗi, kullum idan sun zauna ban da aikin faɗa masa illar da abin da yake yi wa Basma take yi amma ya ƙi fahimta kwata-kwata.

Bayan Baffa Sa'ad ya zauna Baffa Aisar ya fuskance shi ya ce "Wai mene ne dalilin da yasa ka ke yawan yi wa Basma wannan kyarar kamar ba kai ne ka haife ta ba?" Numfasawa Sa'ad yayi ya ce "Ba wai ina kyararta ba ne don ba na son ta, a'a sai don ba na son na nuna mata gata irin wanda ake nunawa wasu kuma ƙarshensu ya zama marar kyau."
"A kan idona lokacin ina gidan haya tare da wani mutum, ya rinƙa nunawa ƴarsa gata yana ririta ta ko kaɗan baya son ganin laifinta, ko mahaifiyarta ba ta isa ta tsawatar mata ba, ƙarshe wannan yarinyar cikin shege ta je ta samo. Mutanen unguwa suka rinƙa tsangwamarsu daga ita har mahaifin nata, kuma shi duk ɗan abin da ya ke da shi yanzu duk ya ƙare. In taƙaice maka labari wannan yarinyar ta sanadinta ya haɗiyi zuciya ya mutu da baƙin cikinta, wannan shine dalilin da yasa ba na son yawan nuna mata gata, ba wai sonta ne ba na yi ba, kawai ina jiye mata tsoron ka da ta faɗa irin mummunar rayuwar waccan yarinyar da muka zauna da su a gidan haya ɗaya.

Murmushi Aisar yayi ya ce "Ai ba da tsangwama ake bayar da tarbiyya ba, kulawa da yabawa su ma duk hanyar bayar da tarbiyya ne, shi wancan mutumin da kuka zauna tare gata ya nunawa Æ´arsa wanda ya wuce kima, kuma ga shi ka ce ba ya son laifinta. Wannan shine dalilin da yasa ta lalace, amma don Allah ka daina nunawa Æ´arka irin wannan tsangwamar kamar ba kai ne ka haifeta ba?"
Ba ƙaramin daɗi Husna ta ji ba, jin mijinta ya ce ya daina nunawa tilon ƴarsu tsangwama, a zuciyarta kuma tana yabawa Aisar akan ƙoƙarin da yayi wajen shawo kan matsalar da ta daɗe tana son magancewa sai ga shi a ɗan ƙanƙanin lokaci ya magance komai gaskiya dole a yaba masa.

Su Safna ne suka ɗauki tashi suka ce su za su tafi makaranta, don yau suna da lacture, Sa'ad ne yayi kiran Basma ya ɗauko kuɗi ya bata yana sakar mata murmushi dubu uku ne ya ce "Ta bai wa Safna da Nasreen dubu ɗai ɗai sannan ta riƙe dubu ɗaya ita ma" da murnarta ta karɓa tana ta yi masa godiya saboda tana matuƙar son Abbanta sai dai tsangwamar da yake nuna mata ne yasa bata sake wa da shi ko kaɗan.

Wata mota ce ƙirar prado tun sassafe take tsaye a ƙofar gidan su Anas, da alama akwai abin da suke jira domin sun ƙi tafiya ko kaɗan.
Su Safna ne suka fito za su tafi school ɗinsu, kawai wani mummunan mutum ya fito daga motar ya sha gabansu ya tsaya ƙiƙam kamar gunki.

Safna ce ta daka mai tsawa ta ce "Malam lafiya zaka xo ka sha gaban mutane suna cikin tafiya?" shiru yayi mata kafin kiftawar ido suka ga wasu manyan ƙarti majiya ƙarfi sun zagaye su, sun ritsa su da bindiga tare da nuna musu motarsu alamar su shiga. Kurma ihu Nasreen tayi ai kuwa kamata ɗaya daga cikin ƙartin yayi ya hankaɗa ta cikin motar har goshinta ya fashe, su Safna da Basma kuwa babu musu suka shiga motar suna kuka.
Suna gama shiga suma gaba É—ayansu suka shiga sannan suka jefo wata farar takarda waje, nan take suka ja motar da gudun gaske suka bar unguwar gaba É—aya.

Wani matashi ne da yake laɓe yana kallon duk abin da yake faruwa, da ya ga sun tafi sai ya fito daga maɓoyarsa ya ɗauki takardar ya nufi gidan su Anas da gudun tsiya, kamar kura ta biyo kare.
Yana zuwa bai tsaya wani tambayar izinin mai gadi ba, ya kutsa kansa cikin gidan, ai kuwa me gadin ma ya bi shi a baya yana cewa ya dakata amma inaaa! sai da ya dangano da falon gidan.

Suna cikin karyawa kawai suka ga mutum ya shigo falon kamar an jefo shi daga sama, Anas ne ya daka masa tsawa ya ce "Kai lafiya ka shigowa mutane babu sallama?" Daidaita nutsuwarsa matashin yayi ya ce "Yallaɓai wasu mutane ne suka zo da wata baƙar mota suka ɗauke wasu ƴan'mata da su uku da suka fito daga nan gidan" da sauri Anas ya miƙe tsaye da ƙarfin gaske ya ce "Whattt".

Aisar ma tuni hankalinsa ya tashi, ya dubi matashin ya ce "Su nawa ne suka zo suka É—auke su?"
"Wallahi ban ko du nawa ba ne domin wasu ba su fito daga cikin motar ba," Su Iya da Inna kuwa tuni sun fara zubar da hawaye, Husna kuwa gigicewa ta yi tana kiran sunan Æ´arta Basma.

Sa'ad kuwa har yanzu ya kasa furta komai akai yayi shiru haÉ—e da dafe kanshi da yake barazanar tarwatsewa.
Sai a wannan lokacin matashin nan ya tuno da takardar da suka jefar ya tsinta, fito da ita yayi ya miƙa wa Anas ya ce "Su ne suka jefar da wannan takardar amma ban karanta ba" da sauri Anas ya karɓa hannunsa yana karkarwa ya fara karanta rubutun kamar haka:

_Saƙo daga wajen shugaban ƴanta'addan Najeriya, CAPTAIN ANAS ABDUL-MALEEK ka sani ina sane da duk shirye-shiryen da ku ke yi a kaina._
_Ka sani kome kuke shiryawa ina da labari, yanzu haka an barku ku zo gida ku huta sannan ku dawo da shirin yaƙata. To burinku ba zai taɓa cika ba, domin ina da masu bani bayanan kome kuke shiryawa ina da labari, amma ku sani burinku ba zai taɓa cika ba._

_Ni ne nan shugaban ƴanta'adda Sa'eed bn Abdul'aziz, ka sani ni ne nan na kwashe ƴan'uwanka, matuƙar ka cika kai cikakken soja ne ka zo ka ƙwace su daga hannuna._
_Kuma ka sani idan zaka zo ka zo kai kaÉ—ai, kuma ban yarda ka zo da makami ko É—aya ba, muddin kuwa ka kuskura ka yi É—aya daga cikin sharuÉ—an nan to zan yi wa Æ´an'uwanka gunduwa-gunduwa sannan ka zo ka kwashe su. Muna nan a cikin dajin Falgore ka sani ka kaÉ—ai ne ka san inda nake amma ka kuskura ka taho da wani to rayuwar Æ´an'uwanka tana cikin haÉ—ari sai ka zo muna jiranka, domin akwai wani aiki da muke so ka yi mana._
_Sai ka zo muna jiranka._

Anas yana gama karanta takardar ya kurma wani uban ihu, da gudu ya haura sama É—akinsa ya shiga, yana shiga wayarsa ya ciro da take caji, lambar ogansu ya lalubo nan take ya danna masa kira.
Bugu ɗaya ya ɗauka ya ce "Anas ya aka yi ne?" nan take Anas ya faɗa masa komai, ya ƙare da cewa "Oga umarni na ke jira daga gareka ka barni na tafi yanzu haka ma shirya wa zan yi domin na je na karɓo ƴan'uwana.
Shiru ogan nasu yayi har sai da Anas yayi zaton ya katse kiran ne, can ya ji muryarsa yana cewa "Anas ba ka san wani Sa'eed ba labarinshi kawai ka ke ji amma wannan mutumin ba shi da imani da tausayi ko kaÉ—an."

Ni a tunanina abin da yasa yayi maka haka, idan ba ka manta ba mun taɓa artabu da wasu tawagar ƴanta'adda to shugaban y'anta'addan nan shine babban yaron Sa'eed kuma kaine ka kashe shi.
Don haka ni a ganina da tunani na ya kafa maka tarkone da Æ´an'uwanka yadda zaka kai kanka har wurinshi domin yayi maka hukunci dai-dai da abinda ka yi masa, na kashe masa babban yaronsa da ka yi.
Don haka ni a shawarata ka tsaya dama akwai shirin da muke yi masa ka ga sai mu farmake shi ta inda bai yi zato ba, amma akwai haÉ—ari idan ka tunkari mutumin nan kai kaÉ—ai. Domin hatsabibancinsa ya wuce duk inda ka ke tunani, ka tsaya sai mu haÉ—a ka da tawagarmu ku je ku farmake shi duk da ba mu san shirin da yayi mana ba.

Da sauri Anas ya ce "A'a oga ni kaɗai ya zaɓi na je kuma yanzu zan je izininka kawai nake Nema."
"Anas ba ka san irin mutanen nan ba ne shi yasa ka yarda zaka kai kanka wajensu, ka sani yaudararka zai yi sannan ya kashe ku kai da Æ´an'uwan naka."
"Oga ka sani ni kome zai yi min ba zan taɓa bari rayuwar ƴan'uwana ta salwanta ba, duk kokarin da yakamata na yi zan yi shi kawai abu ɗaya nake nema a wajenka izini."
Sanin taurin kan Anas da kafiyarsa ya sa ogan nasu ya amince da ya je amma za'a saka sojoji su kewaye dajin don tabbatar da tsaro, nan ma Anas ya ce baya buƙata ya bar shi kawai shi yasan yadda zai yi ya ceto rayuwar ƴan'uwansa.
Babu yadda ogan ya iya dole ya ƙyale shi, amma yana jinjina abin a cikin ransa yana tunanin ta yadda Anas zai kawo ƙarshen wannan mugun kuma hatsabibin ɗanta'addan, duk da yarda da Anas ɓangaren jarumta da sa'a a duk abin da yasa a gabansa, amma yana jiye masa tsoron Sa'eed domin ba ƙaramin makiri ba ne.

Ba Ƙaramin daɗi Anas ya ji ba da hukumarsu ta sojoji ta amince ya tunkari Sa'eed, nan take kuwa ba tare da ɓata wani lokaci ba ya fara shiri cikin ƴan mintuna ƙalilan ya gama kimtsawa ya fito cikin shigarsa ta sojoji. A hankali ya rinƙa saukowa ƙasa har ya gama saukowa su Aisar ya gani a tsaitsaye suna jiranshi ya sauko, kallonsu yayi ɗaya bayan ɗaya sannan ya ce "Yanzun nan zan je domin dawo da ƴan'uwana ku taya ni da addu'a."
Yana gama faɗar haka ya juya zai fice daga falon, "ANAS" muryar Aisar ta daki dodon kunnensa, juyowa yayi a hankali fuskarsa tana zubar da hawaye ya dubi su Inna ya ce "Ku gafarce ni Inna idan na mutu ku yafe min don Allah domin ban sani ba ko ba zan dawo a raye ba. Inna na yarda ki auri Daddin Ammar ko da ba na raye, domin ina da yaƙinin zaki samu farinciki da walwala a wajensa."
Kowa a wajen zubar da hawaye yake yi, Aisar ne ya buÉ—i baki cikin raunin murya ya fara magana "Anas ta yaya kake zaton za mu barka ka tafi kai ma ka hallaka? So kake mu rasa ku gaba É—aya ne, me kake faÉ—a haka ka, tsaya a bi komai a sannu mana, ka sani gaggawa aikin shaiÉ—an ce."

Murmushi Anas ya saki duk da ba wai murmushin murna ba ne, kana ganin murmushin ka ga murmushin takaici gami da alhini amma haka bai hana fuskar Anas haskawa ba, domin Anas irin samarin nan ne da mata suke mafarkin samu a rayuwarsu, ga ilimi ga kyau ga kuɗi sannan kuma jarumta, sai kuma babban abin da yayi wa rayuwarsa ado shine tausayi, Anas yana matuƙar tausayawa mace a rayuwarsa ko kaɗan ba ya so ya ga abin da zai ɓata mata rai kome ƙanƙantarsa kuwa.

Share hawaye Anas yayi daga idonsa ya ce "Baffa ba su Safna suke buƙata ba, ni suke buƙata na kai musu kaina shi yasa suka yi garkuwa da ƴan'uwana domin su same ni cikin sauƙi kuma ga shi sun samu."
"Ka sani da zarar yanzu na kai kaina zasu dawo da su har nan gida a yadda suka yi alƙawari ba za su cutar da ko ɗaya ba, indai ban karya musu dokokinsu ba. Don haka yanzi ni na tafi ba insha Allahu idan su Nasreen ba su dawo yau ba to gobe za su dawo wannan alƙawari ne na yi muku."

Yana gama faɗar haka ya juya zai tafi, sake dakatar da shi Aisar yayi ya ce "Ungo wannan ka ɗaura shi a damtsen hannunka na dama insha Allahu babu abin da suka isa suyi maka" ya faɗa yana mai miƙa masa wani kambu wanda aka naɗe shi da fatar zaki.
Karɓa Anas yayi da sauri ya fice daga falon don kada su sake tsayar da shi, ya zo dai-dai ƙofar gidansu ya ga Ammar shi kuma ya zo gidan.
Da sauri Ammar ya fito daga motarsa yana tambayar Anas ko lafiya, shiru Anas yayi hawaye yana kwararowa akan kyakkyawar fuskarsa sai da ya daidaita nutsuwarsa sannan ya dubi Ammar cikin nutsuwa ya ce........................✍🏻

To be continue.............📝📝📝

HUSSAINI YUSUF✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.