Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 11 of 25

*_______________________________*
*Page 21/22*

Ita kuwa Ummu Nisreen tana zaune a gidanta lafiya, haka yasa suka ɗauki karan tsana suka ɗora mata, sai su zo har gida su zazzageta tas idan ta yi magana su yi mata ɗan banzan duka su tafi, amma ko da wasa ba ta taɓa faɗawa Aisar ba.

Lokaci zuwa lokaci sai sun zo sun yi mata rashin mutunci, a cewarsu asiri ta yi musu shi yasa suka ƙi zaman aure, ita kuma da suke zaton ba zata zauna a gidan auren nata ba, sai ta basu mamaki, take zaune da mijinta lafiya ba ta taɓa zuwa gida yaji ba, ballantana ma har ya kai ga an saketa.

Shi yasa suka sakata a gaba banda hassada da ƙyashi, babu abinda yake tsakaninsu.

Wata rana suka zo suka tarar da ita, tana wanke-wanke suna shigowa babu wacce ta yi mata magana a cikinsu kawai suka hau ta da duka babu sassauci balle tausayi, ihu take yi tana neman taimako amma saboda zalunci suka rufe mata baki ko ta yi ihun babu wanda zai ji ballantana a kawo mata É—auki.

A haka Aisar ya shigo gidan ya tarar da su, ai kuwa bai tsaya wani jinkiri ba, ya koma ya rufo gidan ya ɗauko wani ƙaton icce ya rinƙa jibgarsu suna ihu suna bashi haƙuri, amma saboda ransa ya riga ya ɓaci ko sauraronsu ba yayi kawai dukansu yake.

Sosai jama'a suka taru a ƙofar gidan, sun rasa ta yadda za su shiga domin su taimaka musu, da ƙyar dai wasu suka ɗare katangar gidan suka haura sannan suka zare sakatar gidan sauran jama'ar suka shigo da ƙƴar jama'a suka ƙwace su daga hannunsa.

Aikuwa ana ƙwatarsu suka fice daga gidan a guje, suna ihu da kururuwa, saboda ba ƙaramin wahala suka sha a wajen Aisar ba.

Tun daga ranar ba su ƙara zuwa gidan Aisar ba, kuma ita ma Rahila ba ta ƙara zuwa gidansu ba, saboda ko ta je ta san sai sun rama dukan da mijinta yayi musu, shi yasa tayi zamanta a gidanta bata damu da zuwa gidansu ba.Ko mahaifinsu idan hanƴa ta biyo da shi, yana zuwa su gaisa sannan ya wuce, saboda ba ƙaramin daɗi yake ji ba da yaga Rahila tayi zamanta gidan mijinta, duk da ba zaɓinta aka bata ba amma a haka ta yi haƙuri ta zauna, tana yiwa mijinta biyayya dai-dai gwargwado.

Haka ne yasa take tsananin ƙaunar Aisar fiye da komai, ko mahaifinta bata yi masa son da take yiwa Aisar, domin kuwa Aisar ba baya bane wajen iya soyayya da tarairaya, duk abinda take so ya sani. Yana iya ƙoƙarinsa wajen sauke nauyinta a wuyansa, bai rageta da komai ba na rayuwa shi yasa take jin bazata iya rabuwa da shi ba, sai dai idan mutuwa ce ta raba su, ko kuma shi yace baya sonta.

Don haka ta ɗauki alƙawari a cikin ranta duk inda Aisar zai shiga a duniyar nan indai ya amince tare zasu shiga.

Kallonta Aisar yayi ya ga tayi shiru, gaba É—aya bata tare da nutsuwarta, kama hannuwanta yayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, kallonta Aisar yake yi kamar yana son gano wani abu dangane da ita.

Cikin sanÆ´in murya yace "Ummu Nisreen ki cire duk wani tunani a cikin ranki, Allah yana tare da mu, kuma insha Allahu ina ji a jikina barin garin nan shine yafi zama alkhairi a gare mu.

Yanzu ki tashi ki gyarawa Anas wancan É—akin ya kwanta, da safe zan je na sanar da su Iya abinda yake faruwa, daga nan sai mu samu mafita mu san garin da ya kamata mu koma.

Da kyar ya samu ya rarrashi Anas yayi shiru daga kukan da yake yi, da kansa ya raka shi har cikin É—akinsa ya kwanta, sai da ya tabbatar yayi barci sannan ya bar É—akin ya nufi na Ummu Nisreen.

Sosai ya mantar da ita duk wata damuwa da irin soyayyar da ya nuna mata a cikin wannan daren, sai wajen ƙarfe uku na dare sannan ya barta ta huta, shi sai da yayi wanka sannan ya zo ya kwanta. Ita kuwa Ummu Nisrin barci ne yayi gaba da ita, sai da safe ta yi nata wankan.

💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫

Washe gari da sassafe Aisar ya fita daga gidan, ya nufi gidan su Inna, domin ya sanar da su abinda yake faruwa.

Yana shiga cikin gidan ya ga babu kowa a tsakar gidan, É—akin Iya ya nufa yana shiga ya tarar da ita akan sallaya tana lazimi, zaunawa yayi akan wata tsohuwar kujera, ya jira har ta gama laziminta ta shafa addu'a.

Juyowa tayi ta kalli inda Aisar yake zaune, tace "lafiya Aisaru na gan ka da sassafen nan?" ji tayi yayi shiru kiran sunan shi ta ƙara yi "Aisaru! Aisaru!!" firgigit ya dawo hayyacinsa, yana sosa kai yana wani murmushi domin ya ɓoye damuwar shi, gudun kada Iya ta fahimci halin da yake ciki ita ma hankalinta ya tashi.

"Aisaru wai me yake faruwa da kai ne? ina ta yi maka magana amma hankalinka baya tare da kai" lafiya kuwa?

Zaunawa yayi kusa da Iya fuskarsa cike da damuwa ya gaishe da ita, amsawa tayi tana tambayarsa abinda yake faruwa, domin ta matsu ta ji abinda ya saka Aisar cikin wannan damuwar da bata saba ganin shi a ciki ba.

Labarin abinda ya faru jiya da daddare a gidan me gari ya baiwa Iya, bai rage mata komai ba. Sosai ta shiga cikin tashin hankali, nan da nan ta nemi nutsuwarta ta rasa. Tunani ta fara yi a cikin ranta, dama mutanen garin nan a matsayin Æ´arta'adda suke É—aukarta duk tsawon shekarun da ta É—auka a garin, ashe su mutanen garin a banza suke ganinta?

Ashe duk mutanen da take mu'amala da su, a Æ´arta'adda suke É—aukarta? ita kuwa ya zata yi da rayuwarta? ko da me gari bai ce su bar garin ba, ya zama dole su bar shi.

Ko don su tsira da mutuncinsu, duban Aisar ta yi tace "Aisaru yanzu je ka kira min Innar su Anas na sanar da ita abinda yake faruwa.....

Tashi yayi ya fice daga ɗakin, yana shiga ɗakin ya ganta a zaune tana jan carbi, har ƙasa ya durƙusa ya gaisar da ita, sannan ya sanar da ita Iya tana son ganinta a ɗakinta yanzu......

Ba ta wani ɓata lokaci ba ta biyo shi a baya har ɗakin Iya, basu ɓoye mata komai ba, sosai Inna ta shiga tashin hankali, fashewa da kuka ta yi tana neman yafiyar su Iya da Aisar akan baƙin jinin da suka jawo musu ita da ƴaƴanta.....

Aisar bai baro gidan ba, sai da suka tsayar da garin da yakamata su koma, Inna ce tace "Kawai su koma Kano domin can yafi daɗin zama da kwanciyar hankali, duk da tarin Jama'ar garin amma hankalinsu a kwance yake, domin Baffa lokacin da yake da rai yana zuwa har can ya siyo kaya yazo nan ƙauyensu ya siyar.......

Babu musu Aisar da Iya suka amince da shawarar Inna, domin shi ma Aisar yana jin labarin garin duk da bai taɓa zuwa ba amma yaji hankalinsa ya kwanta da garin na Kano.........

Tashi Aisar yayi yace "bari yaje ya sanar da Ummu Nisrin inda suka yanke za su koma, sannan ya je ya siyar da dabbobinsu don su tanadi guzuri da kuma kuÉ—in da zaiyi sana'a idan sun koma can Kanon........

Tun daga nesa ya hango mahaifin matarsa yana ta faman zuba masifa shi kaɗai, kamar wani mahaukaci sai faman zarya yake yi a ƙofar gidan ya je nan ya je can, kana kallon shi zaka gano rashin nutsuwa a tattare da shi, yana ganin Aisar ya nufo gidan nutsuwa yayi ya ƙurawa Aisar ɗin idanu yana cewa "Alhamdulillahi..........

Tsayawa yayi har Aisar ɗin ya ƙaraso kusa da shi, har ƙasa ya durƙusa ya gaishe shi amma ko kallon inda Aisar ɗin yake bai yi ba, maimakon ya amsa gaisuwar sai ya fara masifa yana cewa......

Aisaru dole ne ka sakar min ƴata Rahila, babu inda ka isa ka je da ita, ban yarda ba, yau da safen nan naje fadar me gari naji yana cewa wai an koreka daga garin nan akan wasu shegun yara da ka tsinto, kuma ana zargin mahaifiyarka da ta'addanci, ina jin haka ban tsaya wani jinkiri ba na zo nan domin ka bai wa ƴata takardar sallamarta in saka ta a gaba mu tafi saboda kar ku je can wajen ƴanta'adda da ita, ita ma ta koyi ta'addancin don ni insha Allahu ba zan taɓa haifar ƴanta'adda ba a cikin zuri'ata..........

Miƙewa tsaye Aisar yayi yace "Baba kai ne kaɗai zaka zo har ƙofar gidana kayi min irin wannan cin mutuncin na ƙyale ka ka tafi lafiya ba tare da nayi maka wani abun ba.........

Ka sani muddin Rahilat ta yarda zata bi ni duk inda za ni, babu wanda ya isa ya hanata bi na, yanzu Aisar rashin kunƴarka har ya kai ina faɗa kana faɗa a matsayina na surukinka? To muddin ka ce bazaka sakar min ƴata ba, zaka ga waɗanda zan turo su tilasta dole ka bata takardarta ko kuma su yi maka lahanin da baza ka moru ba ballantana kuma ka samu ƙwarin gwiwar barin garin........

Sannan ya juya ya tafi a fusace, ya bar Aisar a tsaye yana ta mamakin yadda mutanen garin nan suka juya musu baya karo É—aya, dole akwai munafikin da ya haÉ—a duk wannan abin, kuma ya zama dole na nemo kowaye kafin na bar garin nan Aisar ya faÉ—a a cikin zuciyarsa, sannan ya nufi cikin gidan nasa..............

To be continue..........
Comment and share

HUSSAIN YUSUF
[12/9, 4:35 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐*

*Story and writing by:*
Hussaini Yusuf

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.