Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 25

*Page 19/20*

Tunda me gari ya fara magana, ran Aisar ya rinƙa ɓaci zuciyarsa ta rinƙa tafarfasa har wani ɗaci ya ji zuciyarsa tana yi masa, a fusace ya dubi me gari yace "Yallaɓai na san dai ka san ko ni wanene, kuma ka san mahaifiyata ita ma ko wacece.

Yakamata me gari idan an kawo maka irin wannan zancen, ka rinƙa bincike kafin ka yanke hukunci.

Kaiii! rufe min baki wawa kawai, shashasha kai har ka isa ka faɗa min gaskiya? me gari ya faɗa ransa a ɓace.

ya cigaba da cewa "dukkanmu nan da kake gani babu sa'an mahaifinka a cikinmu, da har ka ke É—aga mana murya, ko shi marigayi mahaifinka malam Habibu bai isa ina faÉ—a yana faÉ—a ba.

Kuma da kake cewa mun san kai wanene ta yaya muka sani? In ce malam Habibu ne a yawon farautarsa ya tsintoka, kai da mahaifiyarka, waye ya san daga inda kuka fito?

Nan take jama'ar wajen suka ɗauka dama tsintacciyar mage ba ta mage, fashewa da kuka Aisar yayi yace "yanzu Yallaɓai da kan ka kake tozarta ni a cikin jama'a? Rufe min baki, kuma na ƙara jin ka kira sunana, yanzun nan sai in keta maka rigar mutunci, me gari ya faɗa a fusace yana mai duban Aisar.

Shi ma Aisar cikin fushi yace "Wacce rigar mutunci ce kuma baka keta mini ba?" wallahi me gari ka ba ni mamaki da har ka ɗauki ƙarairayin mutane a kaina. Ban taɓa zaton haka daga gareka ba me gari, a zatona kai uba ne a gare ni, duba da yadda kuka yi zaman aminci da mahaifina. Ashe yadda na ɗauke ka, kai ba haka ka ɗauke ni ba, nagode da wannan sakayyar da ka yi mana.

Shiru me gari yayi domin ba shi da abin cewa, jikinsa yayi sanƴi haƙiƙa har a zuciyarsa bai taɓa ganin wani aibu na Aisar ba, da har za'a yi Allah wadai da shi.

Amma saboda shaiɗan ya riga ya mallake zuciyarsa, sai yayi sauri ya kawar da wannan tunanin daga zuciyarsa, ya dubi Aisar yace "Yanzu zaɓi biyu zan baka, dole ne ka zaɓi ɗaya daga ciki.

Zaɓi na ɗaya da zan baka shine gobe da safe ka je ka mayar da waɗannan yaran da ka zo da su inda ka ɗebo su, zaɓi na biyu kuma idan har ka nuna ba za ka mayar da su ba, to sai dai duk ku bar min garina gaba ɗaya, bana son na sake ganinka a garin nan idan har kace ba za ka mayar da su ba, to har mahaifiyarka ban yarda ta zauna a garin nan ba, tun da nawa ne ni nake da iko na bar mutum ya zauna ko kuma na kore shi.

Wanne ka zaɓa daga ciki? me gari ya tambaya yana kallon inda Aisar yake tsugunne, ya sunkuyar da kansa ƙasa.

Ɗagowa yayi da rinannun idanun shi, ya kalli me gari yace "Na zaɓi na bar garin nan akan na mayar da waɗannan yaran dajin da na tsinto su, ka sani me gari ƙasa ta Allah ce haka gari da kake ikirarin naka ne to ka yi kuskure, domin garin nan da kake gani na mutanen da suke zaune a cikinsa ne. Ka sani a yanzu idan na bar garin nan ba zan rasa inda zan zauna ba, tunda duniya ce Allah yayi ta da girma, kuma mutanen ƙwarai masu tausayin jama'a ba su ƙare ba, ba zan rasa wanda zai ji ƙaina ya taimaka mini ba.

Kai dakata ɗan samari Liman ya faɗa ransa a ɓace yace "ban taɓa zaton ba ka da wayo ba sai yau ɗin nan, yanzu akan waɗansu yara da ka tsinto a cikin daji ka yarda ka bar garin da Allah ya rufa maka asiri a cikinsa?" Ni dai shawarar da zan baka, tun lokaci bai ƙure maka ba kayi gaggawar canja shawara, domin idan ka bar nan ba lallai ka samu kamar sa.

Dakata liman Aisar ya faÉ—a a hasale "wallahi liman ka ba ni mamaki da har ka biyewa son zuciyarka, kake faÉ—an son ranka akan wani É—an abin duniya da za'a baka wanda bai taka kara ya karya ba.

Sannan ya kalli me gari yace "Yallaɓai ni na yarda zan bar garin nan, amma ina roƙon wata alfarma guda a wajenka. Kallon shi me gari yayi sannan ya kalli liman yace "malam liman ya kake gani mu yi masa alfarmar?"

A fusace Liman yace "kawai ka yi abin da ya dace, yaron da akan idonka ya gama ci mini mutunci amma ka kasa cewa komai shine yanzu zaka hau tambayata wai ayi masa alfarma? kawai idan ka ga zaka yi masa kayi masa idan kuma baza ka iya ba kace kai tsaye ba zaka yi ba."

Kallon fuskar Aisar me gari yayi gani yayi ya masa wani irin kwarjini, take yace "faÉ—i alfarmar da kake son nayi maka idan zan iya sai na yi maka."

Dama alfarmar da zan nema ita ce ka bar ni na zauna tsawon sati biyu idan na kammala shirye-shiryena sai na tafi gaba É—aya. ÆŠaga kai megari yayi sama yana nazari, sai da ya É—auki tsawon minti biyu a haka sannan ya kalli Aisar yace "na yarda babu matsala ko wata guda ka ce zaka yi na yarda.

Godiya Aisar yayi wa me gari sannan ya tashi ya nufi gida, zuciyarsa ban da suya babu abinda take yi, ji yake kamar ya koma ya shaƙe me gari ya kashe shi kawai don ya huce haushin kiran mahaifiyarsa da ƴarta'adda da yayi. Shi ba korarsa ne yafi ɓata masa rai ba, kawai cin mutuncin mahaifiyarsa da aka yi ne yake ƙona masa rai.

To wai wanne munafikin ne ma ya ganni lokacin da na shigo da su Anas garin nan? har yayi min sharrin zina, a zuciyarsa ya ƙudiri aniyar zai yi bincike ya gano kowane, idan kuwa ya gano shi sai ya keta masa rigar mutunci kafin ya bar garin.

Ya saƙa wannan ya kwance da haka har ya ƙaraso gida, yana shiga ya tarar da Rahila (Ummu Nisreen) sai faman zarya take yi a tsakar gidan, ta kasa zaune ta kasa tsaye, tana ganin Abu Nisreen ta yi ajiyar zuciya.

Tambayar shi ta shiga yi, me ya faru ake kiran shi a gidan megari? bai yi mata magana ba, ya kama hannunta suka je wata tabarma da take shimfiɗe suka zauna, Anas ma ya zo ya zauna ya zuba tagumi gabanshi sai faman faɗuwa yake yi, kamar ana daka shi da taɓarya, yana bayar da wani sautin duf!duf!!duf!!!

Addu'a yake yi Allah yasa ba akansu bane me gari ya kira Aisar, shi damuwarsa É—aya idan suka bar wajen bai san inda za su je su zauna ba, cikin aminci da kwanciyar hankali.

Shi a nasa tunanin ko'ina Æ´anta'adda ne, duk inda ya je sai sun gan su sun hallakasu gaba É—aya, ballantana kuma Inna tace suna nemanta saboda ta yiwa ogansu rauni.

Shi yasa ko da wasa ba ya son su bar wannan É—an garin da Allah ya jefo su ta hannun Abu Nisreen.

Shiru ne ya wanzu na É—an lokaci, shi Abu Nisreen yayi shiru yana tunanin ta yadda zai faÉ—awa matarsa abinda yake faruwa ba tare da hankalinta ya tashi ba, gaba É—aya ya rasa yadda zai yi ya faÉ—a mata an kore shi daga garin, kan shi ya kulle sosai, ya rasa yadda zai yi.

Ita kuma Ummu Nisreen ta yi shiru tana sauraron ta ji abinda mijin nata zai faɗa mata, gani ta yi yayi shiru ya ƙi magana sai faman tunani yake yi, magana ta fara yi masa amma sam bai jiyo muryarta ba ballantana ta saka ran zai amsa mata, saboda ya tafi can wata duniya daban da wacce muke ciki(wato duniyar tunani).

Gani ta yi gaba É—aya hankalinsa da nutsuwarsa basa tare da shi, sai ta haÉ—a hannuwanta waje É—aya ta tafa, firgigit! ya dawo daga duniyar tunanin da ya tafi, ya hau sosa kai alamun rashin gaskiya.

Kallon shi kawai take yi kamar tana son gano wani abu game da shi, amma ta gagara hakan, marairaice murya ta yi tace "Haba Abu Nisreen me yasa kake son ɓoye mini damuwarka ne? Bayan ka san indai ka faɗa mini zan san yadda zan shawo kan matsalar?

Shafa kai yayi yace "wallahi Ummu Nisreen kaina ya kulle ne gaba É—aya, me gari ne yace da ni gobe da safe na mayar da su Anas inda na tsinto su, ko kuma na bar garin gaba É—aya.

A firgice Anas ya dubi Aisar ya saka kuka mai sauti, ya taso daga inda yake ya zo har gaban Aisar ya tsugunna yace "don Allah don Annabi Abba karka mayar da mu wani wajen, wallahi idan muka bar nan kashemu za'a yi, don Allah ka taimaka mana.

Kama kafaɗunshi Anas yayi yace "taso ka zauna anan kusa da ni babu musu kuwa ya taso ya zauna, sannan Aisar ya dube shi yace "ka kwantar da hankalinka Anas ban zaɓi na mayar da ku inda na tsinto ku ba hasali ma na zaɓi na bar garin nan gaba ɗaya duk don saboda ku.

Kallon Ummu Nisreen yayi yace "haƙiƙa a tarihin rayuwata ba a taɓa ci mini mutunci ba kamar yau ɗin nan a fadar megari, sun kira ni mazinaci, kuma sun kira mahaifiyata da ƴarta'adda sai ya fashe da kuka.

Nan take ita ma Ummu Nisreen ta fashe da kukan, haka shi ya karyarwa da Anas zuciya shi ma ya saka kukan, sun daɗe suna yi aka rasa me rarrashin wani a cikinsu. Shi Abu Nisreen abinda ya saka shi kuka, tozarta mahaifiyarshi da aka yi ne kuma bai samu dama ya rama ba, shi yasa zuciyarsa take yi masa wani irin zafi kamar ana ƙona masa ita da garwashi wuta.

ita kuma Ummu Nisreen abinda ya sakata kuka, tunanin halin da za su shiga take yayin da suka bar garin, don dole ne ta bi mijinta duk inda zai shiga a duniyar nan, domin bata da kamarsa a tarihin rayuwarta, domin shine ya zamar mata uwa da uba, duk da mahaifinta yana raye amma bata samu wani gata da kulawa daga wajensa ba, kamar yadda kowanne ɗa yake samu daga wajen ubansa. Mahaifiyarta kuwa ta daɗe da mutuwa, don bata fi shekara biyar ba a duniya Allah ya karɓi ran mahaifiyartata. Tun tasowarta ba ta san wani abu wai shi gata ba, sai da Allah ya haɗa ta da Aisar ya rinƙa bata kulawa a matsayinta na matarshi, duk da ba wani soyayya suka yi ba, an aura masa ita ne, kawai don a ƙuntatawa rayuwarta, bisa umarnin matar babanta, sai ga shi kuma cikin ikon Allah da tayi haƙuri sai mijinnata yake tsananin jin tausayinta fiye da kowa, kuma yake tallafawa rayuwarta fiye da yanda take tunani. Saɓanin ƴaƴan Goggo (wato matar babanta) da aka aura musu waɗanda suke so, sai labari ya sha bambam domin kullum su a cikin tashin hankali suke, kullum suna hanƴar gida kai ƙarar mazajensu ko kuma su yo yaji, babu wanda zai zo bikonsu sai dai su gaji don kansu su koma.......

To be continue.........
Comment and share

_*Hussaini Yusuf ✍🏻*_
[12/9, 4:35 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐ANAS MALEEK🫐🫐*

*Story and writing by:*
HUSSAINI YUSUF

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.