Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 23 of 25
*Page 45/46*
Sai da Iya ta maimaita tambayar sannan Inna ta yi gyaran murya ta ce "Me zai hana Iya idan na samu mijin da ya dace da ni."
"Yawwa yanzu nima gani na yi da zamanki haka gara ace kin yi aurenki, shine zai ƙara fito miki da darajarki da kimarki" Iya ce ta cigaba da ce wa "A yanzu haka da nake yi miki wannan zancen, akwai wanda ya aiko yana neman aurenki idan kin amince."
Zaro idanu Inna ta yi ta ce "Ni kuma? ni da ba na fita yawo ko ina, a ina ya gan ni har ya ce yana so na da aure?"
Murmushi Iya ta saki ta ce "Sai na faÉ—a miki sunan mutumin ma sannan zaki yi mamaki" da sauri ta ce "Waye wannan Iya?" Iya ce ta cigaba da ce wa "Ni dai abu É—aya nake nema a wajenki Saratu, don Allah ki amshi maganar mutumin nan hannu biyu, domin mutumin kirki ne. Ba wani ba ne ya aiko yana neman aurenki sai Alhaji Abubakar mahaifin Ammar."
Domin yayi miki kyakkyawar shaida ya ce yana da yaƙinin ke ce kaɗai zaki iya riƙe masa tilon ɗansa Ammar.
Shiru Iya ta yi tana sauraron Inna domin ta ji amsar da zata bata, sai da Inna ta É—auki dogon lokaci sannan ta É—ago da kanta ta ce "Iya ina son ki bani lokaci domin in yi shawara da zuciyata."
Babu yadda ta iya dole ta bar ta domin ta yi shawarar, amma sai ta ce "Kafin gobe da safe ta tabbatar ta yanke shawarar da zata yi, domin ta sanar da ita amsar." Tashi Inna ta yi ta shige cikin É—akin da yake cikin falon, kwanciya ta yi amma tunani kala-kala sun cika mata zuciya.
Tsakaninta da Allah har yanzu ba ta daina son tsohon mijinta ba, mahaifin su Anas har yanzu zuciyarta ba ta daina tunani da begenshi ba duk da yanzu ba ta tabbatar yana raye ba.
**** **** ****
Su Anas sosai suke karɓar horon da ake ba su, sun sha wahala sosai kafin jikinsu ya saba da horon. Cikin ƙanƙanin lokaci jikin Anas da Ammar ya fara murɗewa, suka fara tara damtse, idan ka gan su sai kayi zaton irin manyan mutanen nan ne masu ƙirar samudawa.
Har wata ƙasumba Anas ya tara, ƙirjinsa ya kumbura sosai kamar na mace. Anas irin mutanen nan ne, da ba za ka ga ƙirar da Allah yayi musu ba idan suna sanye da kaya, amma idan babu kaya a jikinshi ka gan shi sai kayi zaton kamar dutse aka cusa masa a damatsansa, saboda ƙirar da Allah yayi masa.
Haka Ammar ma yake idan ka gan shi jikinsa duk ya murɗe, shi ji yake ma kamar ya gama karɓar horo kawai ɓata musu lokaci ake yi.
Yau za'a fara koya musu harbi da bindiga, sosai Anas yake murna saboda babban burinsa a aikin soja shine ya gan shi ya riƙe bindiga yana harbi. Anas bai sha wata wahala ba wajen koyon harbin, domin da can ma yana harbin tsuntsaye da danƙo don haka ya iya saiti sosai.
Haka Ammar ma shi ya ɗan sha wahala kafin ya gama koya, kafin wasu watanni sun ƙware a harbi sosai, yadda ba ka zato.
*BAYAN SHEKARA BIYU*
Sanye su ke cikin kakin soja, sun yi layi irin na sojoji suna jiran umarni. Wani babban soja ne ya zo ya tsaya a gabansu.
Bayani ya shiga yi musu, "Yanzu dai ku ne zaɓaɓɓu kuma horarrun sojojin da zamu yi aiki da su, ina fatan zaku ba mu haɗin kai?" Gaba ɗayansu suka amsa "Insha Allahu yallaɓai" murmushin jin daɗi babban sojan yayi ya ce "Za mu je yaƙar wani hatsabibin ɗanta'adda ne a can jahar Taraba a yankin Mambila, mai suna Sa'id bn Abdul'aziz" ko da Anas ya ji sunan ɗanta'addan nan take tsigar jikinsa ta tashi.
Kowanne gashi da ya je jikinsa ya miƙe, jikinsa ya hau tsuma tamkar wanda ya ke jin sanyi, saboda tsananin ɓacin ran da ya shiga.
Ba zai taɓa mantawa da fuskar ɗanta'addan nan ba. Shine silar barin garinsu, shine ya kashe masa mahaifinsa, sannan ya mayar da yara sama da ɗari biyu marayu a ƙauyensu. Don haka duk yadda zai yi sai ya yi wa Sa'id bn Abdul'aziz kisan wulakanci wanda ba'a taɓa yi wa wani mahaluƙi a bayan ƙasa ba.
Muryar shugaban nasu ne ya katse masa tunaninsa.... "Don haka yanzu zamu bar ku ku je gidaku huta, sosai sannan ku dawo da niyyar fita filin daga.
A tare suka haÉ—a baki suka ce "Thank you sir" sannan suka juya da fareti suka bar filin taron.
Sai faman haÉ—a kaya Anas yake yi, zuciyarsa cike da farinciki yau zai je ya ga danginsa wanda rabonsa da su yau shekara biyu da watanni, amma musababbin murnar ta shi ita ce yau zai yi tozali da fuskar da ya daÉ—e yana mafarki, tunaninta ya hana shi sakat gaba É—aya ba shi da walwala ko kaÉ—an. Amma da zarar ya tuno da kyakkyawar fuskarta sai ya ji nan take zuciyarsa ta yi fari sai ya ji tamkar an shiga zuciyarsa an saka hannu an zare masa duk wata damuwarshi.
Yanzu ma sai faman murmushi yake zubawa kamar gonar auduga. Ammar ne ya shigo É—akin ya gan shi yana haÉ—a kaya yana murmushi, zama yayi kurum ya zubawa abokin nasa idanu yana mamaki. "Wannan wacce yarinya ce da take hana Anas sakewa?" Shi kaÉ—ai yake yi wa zuciyarsa waÉ—annan tambayoyin, amma ko kaÉ—an bai samu amsar su ba.
Ganin wankin hula yana niyyar kai su dare sai ya kada baki ya ce "Anas don Allah wace ce wannan yarinyar da take yawan shiga cikin tunaninka tana hana maka walwala da jin daÉ—i?"
Murmushi kawai Anas yayi ya ce "Me kake ci ba baka na zuba? Idan ka yi haƙuri da zarar mun koma gida zaka ga ko wacece wannan yarinyar, da take sanyani nishadi da walwala a koda yaushe....."
Shi ma Ammar ɗin kawai yayi ya ce "Idan ta yi tsami ai zamu ji" daga haka bai ƙara cewa komai ba shi ma ya duƙa ya fara haɗa kayansa a cikin jakarsa, domin ƙarfe huɗu da rabi jirginsu zai tashi zuwa Kano.
***** ******** *****
Gaba ɗaya gidan murna suke yi yau Anas zai dawo, sai faman girke-girke ake yi. Safna da Nasreen ma sun fi kowa murna domin ba ƙaramin kewar Anas suke yi ba, tun suna irga kwanakin da yake yi har suka dawo irga sati sai watanni ga shi yau shekararsa biyu baya tare da su dole ne su yi kewarsa.
Ita kuwa Basma ko a jikinta domin a cewarta "Kada Allah yasa ma Yaya Anas É—in ya dawo" domin tun yana nan haushi yake bata ba kaÉ—an ba, akan yana yawan yi musu faÉ—a.
Ƙarfe 6:00pm dai-dai gaba ɗaya ƴan gidan suka shirya suka nufi AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPOT domin taron Anas da ya shaida musu jirginsu ya taso. Ko kaɗan Safna ta kasa ɓoye murnarta, ji take kamar ta je can Kadunar su dawo tare da Anas ɗin saboda zumuɗi.
Zaune suke a reception sun zubawa sararin samaniya idanu, jira kawai suke yi su ga dirar jirgin, ƙarfe shida dai-dai sai ga shi na ya keto gajimare yana yin ƙasa-ƙasa alamun sauka yake son yi.....Ba'a ɗauki wani dogon lokaci ba, jirgin ya gama sauka, a hankali aka buɗe murfin jirgin nan da nan mutane suka fara sauka......
Gaba ɗaya dangin Anas sun zuba ido su ga Anas, can suka hango shi shi da Ammar kowanne riƙe da jakarsa a hannu yana ja, ai da gudu Safna da Nasreen suka tafi suna rungume shi, suna ce wa "Yaya Anas sannu da dawo wa".
Hango Basma yayi can wajen su Aisar a tsaye ta haɗe rai, ko kaɗan babu alamun fara'a a fuskarta, gani yayi gaba ɗaya ƴan'matan sun ƙara girma sun zama cikakkun ƴan'mata.
Ƙurawa Basma ido yayi ya ga ta yi wani haske, ta ƙara kyau sai a lokacin ya gama ƙarewa Basma kallo kyakkyawa ce ajin farko. Wannan ɗan ɓata ran da ta yi, sai ya ƙarawa fuskarta wani irin sihirtaccen kyau. A hankali ya ƙarasa wajensu, ya gaisa da Aisar da Sa'ad sannan ya je ya gaisa da su Inna da Iya.
Dai-dai lokacin Alhaji Abubakar ya aiko da motoci biyu domin a kwashe su, gaba ɗaya aka kwashe su sai gida. Maimakon Anas ya ga an nufi gidansu da ya sani, sai ya ga an nufi cikin unguwar Hausawa estate. A ƙofar wani ƙerarren gida na gani na faɗa motar tayi parking, danna horn direban nasu yayi sai ga shi nan da nan gate man din ya zo ya wangame gate ɗin.
Shi kuwa Ammar tuni direban shi ya wuce da shi can gidan mahaifinsa amma ya ce wa Anas zai zo su gaisa da mutanen gidan. Motsi bakin Anas yake yi, alamun yana son tambayar wanne gida ne wannan, da sauri Aisar ya dakatar da shi ya ce "Ya tsaya sai sun zauna." Bayan sun shiga falon kowa ya zauna, Aisar yasa Safna ta kawo wa Anas ruwa mai sanyi, karɓa yayi ya sha, sannan ya ajiye ajiyar zuciya.
Kallon Inna yayi ya ga ta warware ta ƙara haske, ainihin haskenta na bafulatanar usuli ya fito, ta ƙara yin ƙiba sosai. Wani irin daɗi ne ya ziyarci zuciyar Anas saboda ya dawo ya iske ahalinsa a cikin walwala da kwanciyar hankali fiye da yadda ya tafi ya bar su.
Aisar ne yayi gyaran murya ya ce "Da fatan dai Anas an samu abin da aka fita nema?" Sunkuyar da kansa ƙasa yayi ya ce "Insha Allahu Baffa mun samu, yanzu mun gama karɓar horo, kuma kafin a gama hora mu ma, wajen sau biyar muna fita yaƙi kuma cikin ikon Allah duk muna cin nasara. Yanzu ma an ba mu hutu ne, na wata biyu kacal, idan mun koma zamu fita wani babban yaƙi wanda ba iya tawagar mune kaɗai za su je ba.
Murmushi Sa'ad yayi ya ce "Yanzu ɗana kenan ya zama babban soja" sunkuyar da kai Anas yayi yana murmushi ya ce "A'a Abba zamu zama dai" gaba ɗaya suka saka dariya. Sai a sannan Inna ta yi magana ta ce "Yanzu Anas kana nufin nan da wata biyu zaku koma wani yaƙin? E Inna idan mun huta mun koma zamu fita, girgiza kai Inna ta yi ta ce Allah ya ba da sa'a" gaba ɗaya suka amsa da amin.
A can gidan su kuwa yana isa Alhaji Abubakar ya gan shi, take ya shiga yi wa Allah godiya da dawo masa da ɗansa lafiya, domin tun bayan tafiyar Ammar aikin soja, ya daina barci mai daɗi abinci ma idan yana ci baya jin daɗinsa, kawai yana ci ne da kada ya zauna da yunwa. Rungume Ammar yayi a ƙirjinsa wani sassanyan farinciki yana ratsa zuciyarsa, ji yake kamar kada ya sake barin shi yayi nisa da shi.
Falo suka shiga Daddy ya ce "Ammar É—in ya je ya yi wanka, sannan ya dawo ya bashi labari" cike da ladabi Ammar ya ce "To Daddyna bari na shiga ciki, to Ammar É—ina kayi sauri domin ina nan ina jiranka."
Su Anas ana zaune sai faman hira ake sha, amma duk wannan hirar idanun Anas suna kan Basma, ya ƙura mata idanu, tun ba ta ankara yana kallonta ba har ta zo ta kula, gaba ɗaya sai ta ji ta takura tashi ta yi ta tafi part ɗinsu domin gaba ɗaya ta tsani wannan kallon da Anas yake binta da shi.
Kiran sallah aka fara yi a Masallacin unguwar, gaba ɗaya suka tashi suka shiga ciki suka ɗauro alwala suka nufi Masallaci. Su ma su Inna da Iya miƙewa suka yi, suka tafi domin su gabatar da tasu sallar.
Bayan sun dawo daga Masallacin, Aisar ya ce "Anas ya je yayi wanka ya kwanta ya huta, da safe sai suyi magana, tashi yayi ya nufi É—akin da aka nuna masa nasa ne.......âœï¸
To be continue.....ðŸ“ðŸ“ðŸ“
*Hussaini Yusufâœï¸*
[12/9, 4:38 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*
*NA*
*HUSSAINI YUSUF*
*______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*______________________________*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.