Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 13 of 25

*_______________________________*
*Page 25/26*

Shi kuwa Aisar yana zuwa gida ya tarar har Rahila ta gama haɗa musu kayansu, ita da Anas suna tsaye suna jiransa. Yana shigowa ya gansu, yace su zo sai su biya ta gidan su Iya su tafi, lokacin wani abokinsa ya shigo gidan a firgice. Ya dubi Aisar yace "Alhamdulillahi Aisar dama kai nake nema, kuyi sauri ku bar garin nan tun kafin a hallaka ku," kallon shi Aisar yayi yace "me yake faruwa ne, a firgice yace "wallahi Aisar ga su can a fadar me gari sai faman wasa makamansu suke yi wai za su zo su yaƙe ka tun da kai ɗanta'adda ne, don haka kuyi sauri ku fita daga garin nan, tun kafin su zo su iske ka suyi maka wata illar." Aisar nunawa yayi ko a jikinsa, Rahila da Anas kuwa ban da kuka babu abinda suke yi, kallon abokin nasa Aisar yayi yace "Mu'az zan baka amana idan har baza ka ci mini ba, cike da tausayawa Mu'az yace "Aisar bani duk amanar da zaka ba ni insha Allah zan riƙe maka ita hannu biyu."

"Alhamdulillah" shine abin da Aisar yace sannan ya dubi Mu'az yace ga dabbobi na nan, don Allah ka ɗauke su ka mayar da su gidanka ka cigaba da kula min da su, har lokacin da zan buƙace su, idan kuma baza ka iya kula min da su ba, to ka kai min su kasuwa, idan na koma inda za ni sai muyi waya.

Haka yace "to Aisar ni dai na karɓi wannan amanar taka hannu biyu," saboda haka yanzu zan kunce su na mayar da su gidana zan cigaba da kula maka da su insha Allah har zuwa lokacin da zaka buƙace su daga hannuna, godiya sosai Aisar yayi wa Mu'@z sannan ya ja hannun Anas da Rahila suka fita daga gidan suka nufi gidan su Iya.

Suna zuwa suka tarar su ma har sun gama haÉ—a kayansu, nan da nan suka fito suka bi wata siririyar hanÆ´a, wacce zata sada su da bakin titi.
Tafiyar minti talatin suka yi sai ga su, a bakin titi kasancewar titin motoci basa binsa sosai, sai faman jiran mota suke yi ta zo amma shiru har suka shafe awa guda suna jiran mota amma babu wacce ta zo zata wuce, sai wata guda É—aya ita ma kaya ne ta É—ebo saboda haka babu damar shigarta.

A cikin garin kuwa zugar ƴan'daba ne hannunsu riƙe da mugayen makamai, sun nufo gidan su Aisar sai faman wasa kansu suke yi, suna zuwa suka daki ƙyauren gidan da sandunan hannunsa nan take kuwa ƙyauren ya kakkarye, suka kutsa kansu cikin gidan, suna shiga suka tarar babu kowa, sai da suka lalube kowanne ɗaki na cikin gidan, amma ko motsin su Aisar basu ji ba.
Saboda haka suka fito suka nufi gidan Iya, nan ma dai ba su tarar da kowa ba, ba su tsaya wani ɓata lokaci ba, suka nufi bakin titi don su riski Aisar ɗin a can.
Har yanzu shiru babu motar da ta zo wuce wa, har sun ga ji da tsaiwa su Iya sun tsugunna, daga tsugunne Inna ta hango zugar ƴandaba sun nufo inda suke hannuwansu riƙe da makama. A firgice ta muƙe tsaye ta nunowa Iya su, Aisar ma yana waigowa idanunsa suka yi tozali da su, a firgice yace "su Iya su tashi su bar wajen.
Har sun tashi za su gudu, sai suka hango wata mota ƙirar golf ta nufo inda suke, tun daga nesa Aisar ya rinƙa ɗaga wa motar hannu, su kuma ƴan'daban koda suka hango motar tana niyyar tsayawa domin ta ɗauki su Aisar, sai suka rinƙa gudu domin su tarar da su kafin su hau motar.
Me motar yana zuwa dai-dai su Aisar sai ya ja burki ya tsaya, ya dubi su Aisar yace "Ina zaku je ne?" Cike da zaƙuwa Aisar yace "cikin Jalingo zaka kai mu" murmushi me motar yayi yace gaskiya kuna da sa'a, dama can na nufa yanzu kuyi sauri ku shigo.

Da sauri Aisar ya buɗe motar, sai da ya tabbatar kowa ya shiga. Sannan shi ma ya shiga gaba, me motar kuwa ya ja suka tafi, ƴan'daban kuwa dai-dai lokacin da motar ta tashi suka ƙaraso wajen, wasu daga cikinsu suka ɗauki duwatsu, suka rinƙa jifan motar, amma ko kusa da motar jifan bai kai ba, na gaba yayi gaba na baya........Gudu sosai direban yake yi da su Aisar, kallon Aisar yayi yace "daga Jalingo ina kuma zaku nufa?" Murmushi Aisar ya saki yace "za mu nemi motar Kano ne, don na ji an ce can ɗin yafi daɗin zama shi yasa na ɗebo iyalina zamu koma can da zama."
Murmushi direban ya saki yace "gaskiya ne ka iya zaɓan wajen da zaka koma, don Kano indai ka tashi ka nema to insha Allahu zaka samu, yanzu a nawa zan kai ku can Kano ɗin, saboda nima haifaffen Kano ne, yanzu da ka ganni a Taraba, wasu fasinjoji na kawo, shine na shigo nan yankin Mambila domin na wasa idanuna, sai kuma Allah ya haɗa ni da ku, ka ga yanzu na huta zuwa tasha in jira lodi.
Shi ma Aisar ɗan murmusawa yayi yace "Yanzu kenan kana nufin har can Kanon zaka kai mu?" Gyaɗa masa kai direban yayi kafin yace "ƙwarai da gaske ma kuwa, don yanzu ma can na nufa da ku.

Hamdala Aisar yayi, sannan yace "to direba kana ganin a kamar nawa zaka kai mu can Kano ɗin?" Ko kallon Aisar ɗin bai yi ba, yace "ni ko nawa ku ka bani Allah yasa musu albarka" dubu biyar Aisar ya miƙa masa, karɓa yayi har da godiya.

Ana kiraye-kirayen sallar magriba su Aisar suka iso Kano, ba su san inda za su nufa ba, saboda haka direban da ya ga haka, sai ya ji tausayinsu kai tsaye ya yace bari ya kai su gidansa, da safe sai ya nemo musu inda za su zauna.Godiya sosai Aisar da su Iya suka yi masa, saboda halin kirkin da ya nuna musu, a unguwar Darmanawa gidansa yake, saboda kai tsaye can ya nufa da su.Lokacin da suka isa, sai ya tsayar da motar a ƙofar wani gida, ɗan madaidaici, sannan ya fito su ma gaba ɗayansu suka fito daga cikin motar.

Tsayar da su yayi a ƙofar gidan, sannan shi ya shige ciki domin yayi musu iso a wajen matarsa, yana shiga da sallama da gudu wata yarinƴa da ba tafi shekara biyar ba, ta fito ta tarye shi tare da rungume shi tana kiran ga Baba ga Baba, shi ma rungume ta yayi, tare da ɗaga ta sama yana dariyar farinciki, ita ma yarinyar sai faman dariyar take yi.Dai-dai lokacin wata tsohuwa ta fito daga wani ɗaki tana cewa "Aah Sa'idu an dawo kenan?" ajiye yarinyar yayi ya durƙusa har ƙasa, ya gaisheta, lokacin matarsa ta fito da banɗaki, ita ma murmushin ta saki tace "me gida an dawo kenan" shi ma murmushin ya saki cikin sigar zolaya yace "da ban dawo ba zaki ganni ne?" Murmushi kawai ta yi tace "sannu da zuwa amsawa yayi tare da zaunawa" ya dubi tsohuwar nan wacce ko ba'a faɗa maka ba ka san mahaifiyar shi ce, sannan ya dubi matarshi yace "Ammi Husna a tare suka amsa suna mai ƙura masa idanu, ya cigaba da cewa akwai wasu bayin Allah da na ɗauko daga Jalingo, na kawo su nan Kano, za su nemi gida su zauna, to kuma mun iso dare yayi ban ta inda zan fara nema musu gidan ba, shine nace me zai hana na kawo su nan gidan su kwana idan yaso da safe sai na je na nemo musu gidan da za su zauna.

Wani kallo Ammi ta watsa masa tace "yanzu kai Sa'idu dama da baƙi ka zo shine ka shigo kamar ba tare da kowa kake ba?" Husna ma cewa tayi me gida me zai hana sai su shiga wancan ɓangaren tun babu kowa a ciki, ka ga kenan ba sai ka tafi wahalar nemo musu gida ba, indai mutanen kirki ne to nan ma ai gida ne.

Godiya yayi wa Allah da ya bashi uwa ta gari da mace ta gari, Ammi ce tace "maza ka tashi ka je ka shigo da su, ban da abinka Sa'idu ka san ni dai ba zan ƙi saukar baƙo ba, amma ka tsaya ka bar bayin Allah a waje haka?

Tashi yayi ya fita daga gidan, domin ya je ya shigo da su Aisar cikin gidan.......

To be continue........
Comment and share

_Hussain Yusuf_
[12/9, 4:36 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*
*NA*
*HUSSAIN YUSUF*

*_______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*______________________________*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.