Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 25
*______________________________*
*Page 11&12*
Lokacin da Ummata ta shiga cikin kogon, sai ta ga cikinsa duhune sosai, haka yasa ta tsaya daga wajen ƙofa.
Ta rakuye jikin wani ɗan ƙaramin dutse, jikinta ban da rawa babu abinda yake yi, sannu a hankali ta fara hango hasken wuta a can cikin kogon.
Tafiya ta fara yi a hankakli, cikin sanÉ—a tana nufar cikin kogon, domin ta ga wanda ya hura wannan wutar, addu'a take yi a cikin ranta Allah yasa kada na farka daga dogon barcin da na koma.
Daga inda take ta hango wani mutum, sanye da kaya irin na mafarauta, yana gasa nama da alama ci zai yi, domin sai faman jujjuya naman yake yi akan wutar yana barbaÉ—a wani abu a kai, ko ba'a faÉ—a maka ba ka san gishiri ne.
Hamdala Ummata tayi sannan ta nufi wajen mafaraucin, tun daga nesa ya hangota, mamaki ne ya cika mi shi rai har yake tantama a cikin ran shi anÆ´a kuwa wannan mutum ce? Amma bai razana ba kasancewarsa gwarzon jarumi, kuma ba haka kawai yake shiga irin wannan dajin ba.
Bai ɗauke idanunsa daga kanta ba, har ta ƙaraso inda yake, ta yi tsaye akansa tana muzurai, kallonta yayi yace baiwar Allah mutum ko Aljan?
Cikin sanÆ´in murya irin ta wanda ya sha wuya sosai Ummata tace "Ni mutum ce kamarka."
Miƙewa tsaye yayi yace "idan ke mutum ce ya aka yi kika zo nan?" Zaunawa Ummata tayi a ƙasa tace ka taimake ni da ruwa, idan na samu nutsuwa sai na ba ka labarina, miƙa mata wani ƙaramin ƙoƙo yayi cike da ruwa, karɓa Ummata ta yi ta kafa kai sai da ta ji ya ƙulle mata ciki sannan ta ajiye, tare da yin wata ƙatuwar gyatsa.
Bayan ta samu nutsuwa, sai ta kwance ni daga bayanta ta ajiye ni akan cinÆ´arta, har lokacin sharar barcina nake yi, ba abinda ya dame ni.
Kallon mafaraucin nan ta yi, tace ka shirya yanzu zan baka labarina, da na dalilin zuwana wannan dajin mai matuƙar ban tsoro.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta ba shi labarin abinda ya barota da garinsu da gidansu har da mijinta da ya koma domin yaƙar ƴanta'addan bata ɓoye masa ba.
Har hawaye sai da mafaraucin ya zubar, saboda tausayin Ummata da ya cika mishi zuciya yace "kash! dama mijinki bai yi gangancin komawa garin ba, tunda har ya riga ya gudo ba tare da sun gan shi ba." Amma yayi namijin ƙoƙari, tunda har ya tseratar da rayuwar iyalinsa, ko ba komai ai ya bar baya.
Wuƙa ya ɗauko ya miƙawa Ummata yace "ta yanki naman zomon da yake gasawa ta ci iya cinta ta ƙoshi."
Yankar naman zomon Ummata ta rinƙa yi, tana ci har sai da ta ji ta ƙoshi. Sannan ta miƙa masa wuƙar shi ma ya fara yanka yana ci, har ya ƙoshi sannan ya sake miƙowa Ummata ruwa ta karɓa ta sha, sannan shi ma ya sha.
Miƙewa tsaye yayi yace Ummata ta biyo shi a baya, take kuwa ta bi shi, wata siririyar hanƴa ya bi da ita, nan take kuwa hanƴar ta kai su har wata bukka wacce aka yi ta da itatuwa.
Tsayawa yayi a ƙofar bukkan yace "Ummata ta shiga ciki ta kwanta washegari, shi zai kwanta a waje." Ummata ta kalle shi tace "Me zai hana nima na dawo wajen mu kwana tare?" Wani kallo ya watsawa Ummata har sai da ta firgita, yace "ke ba musulma ba ce?" Kinsan dai Addinin musulunci ya hana mutum ya keɓe da matar da ba muharramarsa ba ko? To gaskiya ni ina kiyaye addinina don haka ki shiga ciki ki kwanta ni zan kwanta anan.
Idan kuma ba zaki iya kwanciya a ciki ba, ki fito ki kama hanƴa ki tafi ya faɗa a fusace, ba yadda Ummata ta iya ta shiga cikin bukkar ta kwanta, tunowa ta yi da Sallolin da bata yi ba, don a yau iya Sallar Asuba ta yi. Bata samu damar aiwatar da sauran sallolin da suka wajaba akanta ba, firgigit ta tashi ta fito waje tambayar inda zata samu ruwa tayi zata yi Sallah, nuna mata wani tulu yayi da yake cike da ruwa, ta ɗauko wani ɗan ƙaramin ƙoƙo ta tsiyaya, bayan ta kamo ruwa ta zo ta ɗaura alwala ta koma cikin ɗakin ta tayar da Sallah.
Sai da ta rama duk sallolin da ake bin ta a ranar, sannan ta ɗora da Sallar nafila, a takaice dai sai misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare Ummata ta gama Sallar.
Lokacin ni kuma na farka daga dogon barcin da nake yi, zuwa tulun nan me ruwa ta yi ta tsiyayo ruwan ta zo ta bani, ba kaÉ—an ba na sha ruwan sannan ta bani nono na sha na koma barci.
Ita ma nan ta ɗare gadon karan da yake cikin ɗakin, tunani ne kala-kala ya cika mata rai, tunanin mijinta da iyayenta da sauran jama'ar garinsu ne, ya cika mata rai, hawaye ne ya rinƙa sintiri a kan fuskarta a haka har barci ɓarawo ya zo yayi gaba da ita.
Duk abin nan da Ummata take yi, yana kallonta ganin yadda ta zage tana ta Sallah ne ya burge shi sosai, bayan ta barci ya É—auke ta shi ma ya tashi ya É—aura alwalar ya tayar da Sallah. Bai idar da sallar ba har doshin asuba, sannan yayi sallama ya É—an kwanta ya runtsa kafin alfijir yayi.
Washe gari da safe ya É—auko gurasa da gasashshen nama, ya bai wa Ummata yace ta ci. Bayan ta gama ci, sai ya kalleta yace "yau zai koma garinsu don haka ta shirya sai su koma tare."
Ɗauko jakarsa yayi irin ta ƙwararrun mafarauta, ya rataya ta a kafaɗa yace Ummata ta biyo shi a baya. Tafiya suke sosai, tun da sassafe har rana ta take, saboda tausayin Ummata da yake yi yasa ya tsaya ta huta sannan suka cigaba da tafiya sai can wajen yamma suka fara hango wani ɗan ƙaramin ƙauye a tsakanin duwatsu.
Bayan sun ƙarasa ƙauyen ne, wani gida ya nufa da ita yayin da suka shiga gidan, sai wata tsohuwa ta taso da murnarta tare shi tana cewa "sannu da zuwa babana."
Sai da ta ɗago idanunta, karaf! ta sauke su akan Inna, tambayar shi ta yi inda ya samo wannan matar yayi bai ɓoye mata kome ba, game da labarin Ummata.
Wannan tsohuwar ta tausayawa Ummata ba kaÉ—an ba, tun daga ranar suka zama Æ´an'uwan juna da Ummata, kullum a wajen wannan tsohuwar nake wuni.
Sannu-sannu har Ummata ta samu labarin mutuwar Abbana a hannun ƴanta'addan nan, haƙiƙa ta yi kuka sosai, na rabuwa da Abbana da kyar tsohuwa da Mafaraucin nan suka rarrasheta tayi shiru.
Lokacin da tayi idda sai Habib wato mmafaraucin nan ya nuna yana son auren Ummata, da kyar dai ya samu ta amince zata aure shi.
Lokacin da ya auri Ummata sai ya mayar dani ɗansa, ya saka ni a makarantar boko a can wani gari nesa da ƙauyen da muke sosai, kafin na yi wayo kullum shi yake rakani har makarantar sannan idan an tashi da kansa zai zo ya ɗauke ni.
Kuma kullum da yamma da daddare ina zuwa makarantar allo da take cikin ƙauyen, idan kuwa aka yi hutu tare muke zuwa farauta, da haka har nima na koyi farautar.
Wata rana kwatsam! lokacin ina aji shida a primary, muka tashi da Abbana ciwon ciki ya turnuƙe shi, kafin mu yi wani yunƙuri rai yayi halinsa. Mun sha kuka sosai, musamman ma ni ba ƙaramin shaƙuwa muka yi da shi ba.
Tun daga ranar nima na ware rana, duk wata sau uku nake zuwa farauta, saboda na gaji Abbana. Sannu a hankali har na zama ni ne shugaban mafarautan ƙauyenmu, saboda kaf ƙauyen babu wanda ya kai ni iya farauta.
Shikenan na watsar da duk wani karatun boko sai na allon nake ɗan taɓawa, wani lokacin.
kunji taƙaitaccen labarina, don haka kuma zan taimaka muku iyakar ƙarfina.
Safna ce tayi murmushi tace "Abba labarinka wallahi akwai daɗi murmushi yayi ya shafa kanta, yace kina son labarai? gyaɗa masa ta yi yace "To karki damu kullum zan rinƙa baki labari Mai daɗi.
Anas ne ya katse musu zancen da cewa "Abbanmu zaka kai ni in zama babban soja?
[12/9, 4:33 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ðŸ«Â🫠ANAS MALEEKðŸ«ÂðŸ«Â*
Labari/Tsarawa
HUSSAINI YUSUF
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘Yancinmu*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.