Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 15 of 25

*Page 29/30*

Yana shiga ya tarar da su gaba É—ayansu a zaune a kan tabarma suna karyawa da shayi da bread, zama yayi yana tambayar su inda suka samu shayi, Iya ce ta bashi amsa da cewa "ai É—iyar albarkar can ce ta kawo mana, da sassafen nan, kai ma zauna a zuba maka."

Samun waje Aisar yayi ya zauna, Rahila ce ta zubo masa shayin, a wani a kofi sannan ya karɓa yana godiya, biredin iri me yanka-yankan nan ne, saboda haka karɓa yayi ya ɗebi guda uku yace sun ishe shi.
Nasreen na hango a gefe ita da Safna, sai faman shan shayin suke yi, ko irin surutun nan, da suke yi idan suna cin abinci yau babu shi, ban da santi babu abinda suke zubawa.

Sosai suka bai wa kowa dariya a wajen, Anas ma bai saba shan shayi da madara ba, yana jin daɗin shi sosai, amma shi ko kaɗan bai nuna yana santi ba, saboda kar ayi masa dariya, don ya tsani ya ga ana yi masa dariya to yanzu ransa zai ɓaci.

Bayan kowa ya gama breakfast ɗin, sai Aisar ya dube su cikin nutsuwa yace "Alhamdulillahi rabbil alamin, dukkan godiya ta tabbata ga Allah (S.W.A) tsira da amincinsa su ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu (S.A.W) kamar haka muka fito daga garinmu ana bin mu za'a kashe mu, cikin ikon Allah da ƙudurarsa ya kawo mana Sa'ad ya taimaka mana, sanadinsa yau ga mu dukanmu a cikin farin ciki.

Nan ya kwashe labarin yadda suka yi da Aisar da safiyan nan, ya faɗa musu bai rage musu komai ba, ya cigaba da cewa "ni yanzu babu isassun kuɗaɗe a wajena, amma zan fara da waɗanda nake da su, kafin na yiwa Mu'az waya, ya siyar min da dabbobina ya aiko mini da kuɗin sai na ƙara jari, ko ya kuka gani?

Rahila ce ta yi gyaran murya tace "ni ina da wasu kuɗi da na siyar da saniyar nan da babata ta bar min, to kuɗin suna nan ko biyar ban taɓa ba, saboda haka bari na je na ɗauko maka su, sai ka haɗa da na wajenka ka fara, Allah ya sanƴa albarka a cikin sana'ar.

Nan kowa ya amsa da amin, sannan Iya ma tayi masa addu'ar farawa lafiya, nan dai kowa yayi ta masa addu'a, nan suka zauna suna hira, sosai har lokacin fitar Sa'ad yayi. Da kansa ya shigo ya gaisar da su Inna, sannan yace "shi zai fita aiki, ban da aikin godiya babu abin da su Iya suke yi masa, shi ko sai cewa yake babu komai ai yiwa kaine.

A motarsa ya ɗauki Aisar suka nufi kasuwar Wambai, kai tsaye rumfar abokin Sa'ad malam Ɗahiru suka nufa, suna zuwa suka iske shi yana ƙirgar kuɗi sauri yayi ya ɓoye, sannan ya dubi Sa'ad rai a ɓace yace "haba Sa'adu ya zaka shigo mini rumfa kai tsaye baka tsaya nayi maka iso ba?"

Murmushi kawai Aisar yayi saboda ya riga ya san halin Malam ÆŠahiru akan kuÉ—i, ba shi da mutunci sai son kuÉ—i amma kuma ba zai iya siyan wani abun ya saka a cikinsa ba. Haka yasa yake tsoron Æ´aÆ´ansa, kada suyi masa sata, shi yasa idan zai yi irgar kuÉ—i sai ya shige can cikin rumfarsa ya hana kowa shiga.

To yau ma irgar kuÉ—in yake yi, su Aisar suka same shi, a zatonsa wani daga cikin yaransa ne, ya shigo shi yasa ya firgita sosai, da yaga su Sa'ad ne sai ya fasa faÉ—an da yayi shirin yi amma duk da haka sai da ya sauke wa Sa'ad wani faÉ—an.

Samun waje suka yi suka zauna akan wani benci, sai da ya gama irga kuÉ—insa tas, sannan ya saurari su Sa'ad yace me yake tafe da su, nan take Sa'ad yayi masa bayanin komai, take ya yarda malam ÆŠahiru akwai son customer, suna nan zaune ya kira wani yaronsa ya kawo wa su Sa'ad ruwa da abinci.

Sai da suka ci suka yi masa godiya sannan Sa'ad yayi masa bayanin duk abinda ya kawo su, nan take kuwa ya É—auko wasu gwanjuna masu yawan gaske ya bai wa Aisar.

Godiya Aisar yayi, sannan yace zai nemo masa wajen da zai rinƙa zama yana kasa kayan, ba sai ya fita yawo ba tun da bai san cikin garin sosai ba, bayan Aisar ya karɓi kayan gwanjon sai malam Ɗahiru ya haɗa shi da wani yaronsa ya nuna masa inda zai kasa kayan, kuma yace yaron ya tsaya ya rinƙa koya masa yadda ake siyarwa, kafin ya saba shi ma ya fara siyarwa da kansa.

Tare da Sa'ad suka fito suka kira wani baro ya daukar musu kayan har rumfar da aka baiwa Aisar É—in ya zauna, bayan sun je Aisar ya ga akwai masu gwanjo da yawa a wajen, a ransa yake tunanin zai siyar kuwa, amma sai yayi shiru bai ce komai ba, bayan sun sauke kayan, sai suka kakkasa su a gefen hanÆ´a inda mutane suke wucewa.

Suna gama kasawa kuwa mutane suka kewaye su ana zaɓa, yaron ne me faɗar farashin kayan, shi kuwa Aisar yana kula da duk wanda ya ɗauka gudun kar gudar musu da kaya, ciniki suke yi sosai yamma tayi sannan suka haɗe kayansu suka nufi shagon Malam Ɗahiru, suna zuwa kuwa Aisar ya zauna a cikin rumfar ya lissafa kuɗinsa, bisa ga mamakinsa sai ya ga ya mayar da kuɗinsa, har da riba ma akai, wajen dubu huɗu da ɗari biyar kuma yana da sauran kayan ba su ƙare ba.

Kiran yaron da ya taimaka masa yayi ya sallame shi, Malam ÆŠahiru ya kalle shi yace "da fatan dai yanzu ka ga yadda ake yi? gobe ko kai kaÉ—ai ma zaka iya zuwa ko?" Shafa kai Aisar yayi yace "na gani Baba insha Allah gobe ko ni kaÉ—ai ne, zan iya kula da komi, ashe ma harkar babu wuya sosai.

Nan dai yayi wa Malam Ɗahiru sallama ya nufi gida, duk hanƴar da suka biyo shi da Sa'ad lokacin da za su zo Wambai ɗin, yana riƙe da ita a ransa bai manta ba, don haka shi ma nan ya rinƙa bi, har ya fito bakin titi ya tari napep yace Darmanawa zai kai shi, faɗa masa kuɗin yayi yace "su je babu matsala".
Lokacin da iso cikin Darmanawan Allah yasa suka fito dai-dai unguwar da Aisar ɗin suke, da suka kusanto layin nasu sai ya dakatar da me napep ɗin yayi yace zai ƙarasa a ƙafa.

Bayan ya sallami me napep ɗin sai ya nufo gidan, yana zuwa ya iske Nasreen da Safna da kuma Basma suna ta wasa a ƙofar gidan, suna ganin shi suka tashi da gudu suka tarye shi, har da Basma duk da bata san shi ba amma sabida ba ta da wuyar sabo nan ita ma ta zo ta rungume Aisar kamar dai yanda ta ga su Safna sunyi.

A tare suka shiga cikin gidan, ya fito da tsarabar da taho musu da ita ya damƙawa kowa nasa, har da Basma sai da ya baiwa. Da gudu kuwa ta je ta nunawa Ummanta, harararta tayi tace "wato Basma ba ki jin magana ko?" bana hanaki roƙo ba?
Marairaice murya ta yi tace " wallahi Umma ni ban roƙe shi ba, Abban Safna ne ya ganmu muna wasa shine da ya basu sweet ɗin nima ya bani.

Kallonta Husna tayi tace "shikenan amma kar na ƙara ganin kina roƙo, idan ki ka ga Abban su Safna ya dawo to kiyi sauri ki taho gida kin ji, kar ki kuskura ki je kema a baki sweet ɗin, idan kika faɗawa Abbanki zai siyo miki kin ji. Da murnarta tace "to Ummata kiyi haƙuri ba zan ƙara ba, na je na mayar musu da wannan sweet ɗin yanzu?"

Sai da ta baiwa Husna dariya tace "a'a ban ce ki mayar musu ba, amma kar ki ƙara zuwa a baki kin ji ko.

Aisar kuwa yana gama rabawa su Safna da Nasrin sweet ɗin, sai ya ɗauki bocket ya nufi famfo zai ɗebi ruwa domin ya watsawa jikinsa, da sauri Rahila ta karɓe bokitin da kanta ta tara masa ruwan, ta ɗauka ta kai masa banɗakin sannan ta fito tace ya shiga yayi wankan.
Kafin ya fito har an fara kiran sallar magariba, saboda haka ta É—auko buta ta zuba masa ruwan kafin ya fito, yana fitowa kuwa yayi maza ya É—aura alwalar ya shiga É—aki ya saka kayansa masu kyau, ya nufi masallaci.

Su Iya kuwa suna can ɓangaren Ammi sai hira suke faman sha, domin Ammi macece mai son jama'a kiran sallar da suka ji ne yasa suka tashi suka taho lungunsu domin su gabatar da sallah.

Aisar kuwa akan hanyarsa, zai fito ya haɗu da Sa'ad ya dawo daga kasuwa, yana ganin Aisar ya saki murmushi yace har ka dawo kenan, Aisar yace "wallahi na daɗe da dawo wa ma har nayi wanka yanzu masallaci zan je, idan na dawo zamu yi magana, shiga cikin gidan Sa'ad yayi shi ma ya ɗaura alwalar ya fito ya nufi masallacin, don har an kai raka'a ɗaya raka'a biyu ya samu, haka ma ya godewa Allah da ya nufe shi da zuwa masallacin don Sa'ad ba baya bane wajen ƙokarin ibada.......

To be continue..........
Comment and share

*_HUSSAIN YUSUF_*
07069475482[12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*

*NA*

*HUSSAINI YUSUF*

*_______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*______________________________*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.