Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 25

*________________________________*
Page 5&6

Yayin da Anas ya ga Inna a kwance, a gaban gawar Baffa, sai ɗimauce zuciyarsa ta shiga bugawa da ƙarfin gaske. ƙoƙarin kwance Safna yake a bayan Inna, amma kwata-kwata ya kasa, domin ɗaurin da Inna ta yi mata ba na wasa ba ne, da ƙyar da siɗin goshi ya samu ya kwance ta, ganin har yanzu Inna ba ta tashi ba yasa shi fashewa da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro sannan ya sa ka zuciya rauni.
Tuno lokacin da Safna ta suma yayi, yadda ya ga ana watsa mata ruwan randa me sanyin gaske ta farfaɗo, yana gama wannan tunanin, bai tsaya wata shawara da zuciyar shi ba ya nufi wani ruwan sama da ya taru a gefen hanƴa.Da hannunsa ya ɗebo ruwan, kafin ya ƙaraso wajen Inna tasa ma rabin ruwan duk ya tsiyaye yana zuwa ya watsa mata a fuska, gani yayi bata motsa ba, ya sake komawa domin ɗebo wani ruwan, Safna ma biyo shi ta yi, don ta taya shi ɗebo ruwan su watsa wa Innarsu ta farka su tafi. Duk wannan abinda Anas yake yi sai faman kuka yake Mai sautin gaske, babban abinda ya fi ɗaga masa hankali shine ganin gawar Baffansu a kwance akan hanƴa a wulaƙance.

Suna sake É—ebo ruwan, suka watsa wa Inna take ta farfaÉ—o daga suman da ta yi, tana ajiye ajiyar zuciya.

Tashi zaune ta yi, ta rungume gawar Baffa ta fashe da kuka, su Anas ma sai suka fashe da kuka babu mai rarrashin wani a cikinsu.

Sun shafe lokaci mai tsawo a haka, sannan Inna ta yi ƙarfin halin daina kukan ta dubi Anas.

"Anas maza ka tashi, ka ja hannun ƙanwarka ku gudu daga wannan garin."

ƙin tashi Anas yayi, shiru yayi yana kallon Inna "ba zaka tashi mu tafi ba ko so kake duk mu hallaka gaba ɗayanmu?" Inna ta daka masa wata razananniyar tsawa.

Shi dai Anas a iya shekarun da yayi da mahaifiyarsa, ba ta taɓa ɗaukan wani madoki ta dake shi ba, ballantana ta yi masa wata tsawa.

Amma yau ga shi da kanta take korarsa, akan ya tafi ya barta bai san halin da zata shiga ba idan ya tafi, sai dai ba shi da zaɓi, muddin yana son ya rayu to dole ne ya ja hannun ƙanwarsa su bar wajen. Harbi suka jiyo can nesa, daga inda suke, firgita Inna ta yi tace "Anas ka ja hannun Safna ku tafi, ni ta wa ta ƙare, ina yi maka nasiha ka rungumi ƙanwarka, ko kaɗan kada ka bari ta zubar da hawayen maraici.

Jin harbin yana ƙara kusanto su, "Anas maza ka ja hannun Safna ku tafi insha Allahu babu abinda zai same ku" ina yi muku fatan alkhairi, juyawa Anas ya kama hannun Safna yana ta faman rusa kuka, ita ma Safnar ban da kuka babu abinda take yi. Tafiya suke yi, suna waigen mahaifiyar ta su, suna ta faman kuka, da ƙarfi Inna ta kira sunan Anas waigo wa suka yi a tare shi da Safna, "komai tsawon lokaci karka bar ɗayansu a raye, ka kashe su duka. domin ka ɗauki fansar ran iyayenka da jama'ar garinku."

Da ƙarfi Anas yace "insha Allahu Inna duk sai na kashe su, ba zan bar ɗayansu a raye ba." Sannan ya ja hannun Safna, suka tafi da gudun gaske, suna cikin gudun suka ga jariri a gefen hanƴa yana ta faman tsala uban kuka, ga rana me zafin gaske sai gasa shi take yi.

Har sun wuce shi da gudu, Safna tace "Yaya Anas mu koma mu ɗauki wancan jaririn da ganin shi, an kashe iyayen shi, mu taimaka masa wataƙila ta sanadiyyar sa mu ma Allah ya taimaka mana."

Mamakin kaifin basira da hangen nesa irin na Safna, Anas yake yi, don shi ko kaɗan bai ji zuciyar shi ta raya masa ɗaukar jaririn ba, amma sai ga shi ƙanwarsa wacce ya shige ta a shekaru sosai ta yi wannan tunanin mai matuƙar amfani. Amma duk da haka sai ya dubeta cikin nutsuwa yace "yanzu Safna idan muka ɗauki jariri, me muke da shi wanda zamu ba shi?" mu ma kanmu ba mu sani ba ko zamu rayu, don haka kawai ki zo mu tafi, ki rabu da shi Allah zai kawo wanda zai taimaka masa.

Yana faÉ—ar haka ya kaÉ—a kai ya wuce gaba, yana mai yafito Safna da hannu alamun ta biyo shi, tafiya yake amma bai ji alamun ana bin shi a baya ba, waigowa yayi can nesa ya hango Safna ta ruga da gudu ta nufi inda suka ga wannan jaririn da babu uwarsa. Ai bai tsaya wata-wata ba, ya bi bayanta da gudu.

Kafin ya riske ta har ta ƙarasa inda jaririn yake, ta ɗauko shi ta juyo. Anas yana zuwa inda take ya karɓi jaririn sannan yace "ta biyo shi da gudu su bar yankin garin nasu gaba ɗaya domin su tsira da rayuwarsu.

Inna kuwa har yanzu tana kwance akan gawar Baffa tana ta faman rusa kuka mai tsuma zuciya, takun mutane ta ji alamun suna kusanto inda take, shiru ta yi ta daina kukan da take yi. ta rufe idanunta tare da ɗauke numfashinta, alamun ta mutu, suna zuwa suka ga gawar Baffa Inna tana kwance akansa, duk jikinsu ya ɓaci da jini.

Bushewa da dariya suka yi, sannan ɗayan yace "oga dubi wasu ma'aurata saboda tsabar soyayya a lahirar ma ba za'a rabu ba. Shi ma ogan dariya ya saka sannan yace "rabu da jahilai ai a haka zamu ƙarar da su babu ruwan mu da wata soyayyar miji da mata domin mu bamu san ta ba." kisa kawai muka sani, sannan suka sake bushewa da dariya, suka taka ƙafar Baffa suka wuce, taɓa jikin Baffa Inna ta yi ta ji wata sharɓeɓiyar wuƙa mai kaifin gaske.

Bata tsaya wata shawara da zuciyarta ba, ta zaro wuƙar ta riƙeta a hannunta na dama sannan ta ɗauki takobin Baffa a hannunta na hagu, ta bi bayan ƴanta'addan cikin wani irin gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya.

HUSSAIN YUSUF✍️
Comment
Share fisabilillahi
[12/9, 4:32 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐*

Labari/Rubutawa
HUSSAINI YUSUF

Whatsapp number
07069475482.

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.