Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 20 of 25

*Page 39/40*

Har ƙofar gidan su Anas aka kawo shi, kuɗi ya ciro a cikin aljihunsa ya sallami me napep ɗin, ba tare da wata fargaba ba ya kutsa kansa cikin gidan su Anas ɗin. A ƙofa yayi karo da Basma zata fito, kallonta yayi ya ce; "Ke Anas yana nan kuwa?" Girgiza kai ta yi ta ce; "Yana nan breakfast yake yi, murmushi Ammar yayi ya ce; "Don Allah je ki kira mani shi zamu yi wata magana". Komawa cikin gidan ta yi, Anas kuwa yana zaune akan tabarma yana shan shayi, nan kuma ga su Aisar da su Inna gaba ɗayansu dai an haɗu ana karyawa. Basma ce ta shigo da sallamarta, tana zuwa ta ga Safna da Nasreen suna cin ƙosai, ba ta jira sun yi mata tayi ba, ta zura hannu ta fara cin ƙosan. Harararta! Nasreen ta yi ta ce; "Ke haka ake yi da shigowar ki, ba kiyi kowa magana ba, sai kawai ki fara ci mana abinci? Wallahi kika yi wasa ba ki isa ki ƙara ci ba."

Ko kallonta Basma ba ta yi ba ta cigaba da cin ƙosanta, gaba ɗaya ta manta da saƙon da aka aikota ta zage tana ta cin ƙosanta har da kora koko, sai da ta ji tayi nak sannan ta ɗago da kanta, tana wani kalle-kalle karaf! Idanunta suka sauka akan Anas.Nan take kuwa ta tuno da aiken da Ammar yayi mata, kallon Anas ta yi ta ce; "Yaya Anas abokin nan naka yana waje ya jiranka mantawa na yi ban faɗa maka ba." A fusace ya kalli Basma ya ce; "Yanzu dama ke aiko ki aka yi shine kika kasa faɗa mini har sai da ki ka ci kika ƙoshi ko? Yanzu yana can yana jirana sai ya ce nayi masa wulaƙanci alhalin ni ban san ma yana jirana ba." Mtsssss! ya ja wani dogon tsaki sannan ya ɗauki takalmansa ya fita waje, Ammar ya gani a zaune akan wani ɗan ƙaramin dakali, yana ta aikin zaman jiransa, sallama Anas yayi masa da sauri ya juyo ya kalli Anas sai ya saki wani murmushi. "Don Allah Ammar ka yi haƙuri, wallahi yarinyar da ka aiko sai yanzu ta faɗa mini kana jirana, amma wallahi kwata-kwata ban san da zuwanka ba. Ko da yake ba komai ai duk laifinka ne" da mamaki Ammar ya kalle shi ya ce; "Laifina kuma Anas bayan jiran da nayi maka? Laifinka mana me yasa da ka zo ba ka shigo daga ciki ba ka tsaya a ƙofa sai ka ce ka zo gidan ƴan yankan kai." Murmushi Ammar yayi ya ce; "Wallahi ni bana son shiga gidan da ba na mu ba, sai naji ni duka a ɗaɗɗaure, na kasa samun sukuni shi yasa wallahi, har zan shiga sai na haɗu da wannan ƙanwar taka Basma za ta fito shi yasa nace ta kirawo min kai sai ka shigar da ni. Amma yanzu tun da gashi ka fito ai kawai sai mu tattauna anan ba sai na shiga ba."

"Ohhh! kana nufin nan ba gidanku ba ne shi yasa baza ka sake ba idan ka shi ko?" Murmushi Ammar yayi ya ce; "No Anas ba haka nake nufi ba, kawai dai ba na jin daɗin shiga gidanne kawai" miƙewa tsaye Anas yayi ya dubi Ammar da yake zaune ya ce; "To bari ka ji ba zan taɓa tsayawa na saurare ka ba, indai ba za ka shiga cikin gidanmu ba." Yana gama faɗar haka ya juya ya nufi cikin gidan da sauri kuwa Ammar ya miƙe ya bi bayansa a tare suka shiga cikin gidan. A tare suka ƙarasa shiga ciki, kallon Anas Aisar yayi ya ce "Anas wannan kuma wanene?" Murmushi Anas yayi ya ce "Ammar kenan Abba ya zo ne ya raka ni mu je mu yiwa Daddinsa godiya" murmushi Aisar yayi ya ce "Masha Allah ai tare zamu je don nima nayi masa godiya, akan abin da yayi mana." Murmushin yaƙe Ammar yayi ya ce "A'a Abba ai ba sai ka je ba, tunda Anas za shi kawai ka yi zamanka. Dariya Aisar yayi ya ce "Ai dole ne na je na yiwa Daddinka godiya, domin abin da yayi mana kafin a samu wanda zai yi mana irin shi za'a daɗe sosai. Duk yadda su Anas suka so hana Aisar ya bi su, sai da ya kira Sa'ad suka tafi gidan su Ammar ɗin tare.

Cikin falon da ake ajiye baƙi Ammar ya kai su Aisar, shi kuma ya shiga cikin gidan, domin ya shaidawa Daddinsa baƙin da yayi. A falonsa ya zo ya iske shi yana ta faman danna laptop, zuwa yayi ya zauna kusa da shi, ya ce "Daddy ga Anas ɗin ya zo amma......." Kallonshi Daddy yayi ya ce "Amma me?" sunkuyar da kai yayi ya ce "Amma tare da Abban shi muka zo, wai shi ma zai yi maka godiya." Murmushi Daddy yayi ya ce "Masha Allah da bai zo ba ma sai nasa an kirawo min shi, tashi mu je kada su ce an bar su an ƙi kula su." Tashi yayi ya dubi Ammar ya ce "maza ka je ka cewa Lami tayi sauri ta kawo musu ɗan abin taɓawa" tafiya Ammar yayi domin ya faɗawa me aikinsu Lami saƙon Daddinsa. Shi kuma Daddy ya nufi ɗakin baƙin domin ya haɗu da su Aisar.

Da sallama ya shigo cikin falon, suna ganin shi suka miƙe tsaye suna mai barka da shigowa. Murmushi Daddy yayi ya ce "Ku zauna mana" zama suka yi, sannan shi ma Daddy ya zauna, dai-dai lokacin Ammar ya shigo shi da Lami hannunta ɗauke da plate da ruwan gora akai, ajiye wa tayi sannan ta tashi ta fita. Shiru ɗakin ya ɗauka na ɗan wani lokaci, Aisar ne yayi ƙarfin halin ce wa "Alhamdulillah Alhaji kamar ba ka san mu ba, mu ne iyayen Anas abokin ɗanka Ammar; mun zo ne domin mu yi maka godiya akan abin alkhairin da kayi mana, ka ce zaka samowa Anas aikin soja" murmushi Daddy yayi ya ce "Ai har na samo musu aikin ma, ƙarshen satin nan ma nake son su tafi domin a fara ba su horo" da gudu Ammar ya tashi ya je da gudu ya rungume Daddy yana ce wa "Nagode Daddyna Allah ya cika maka burinka kai ma, da sauri ya ce "Amin amin ɗana, gobe insha Allahu zaku fara shirin tafiya."
Kallonsu Daddy yayi ya ce "Wai ina Anas ɗin ni fa har yanzu ban gan shi ba, kafin Ammar yayi magana Anas ya riga shi ya ce "Ga ni nan Daddy" murmushi Daddy yayi ya ce "Taso mana ka zo kusa da ni ai kaima ka zama ɗana daga yau, cikin sanyin jiki Anas ya miƙe ya je ya zauna kusa da Daddy. Cike da jin daɗi Daddy yake kallonsa, yana sakin wani murmushi ji yake kamar Anas ɗin jininsa ne. Mayar da kallonsa wajen su Aisar yayi ya ce "Insha Allahu a satin nan su Anas za su tafi makarantar horon sojoji ta Kaduna, ba za su dawo ba har sai sun gama karɓar horo. Saukowa su Aisar suka yi daga kan kujerar da suke a zaune, suka dubi Daddy suka ce "Alhaji yadda ka faranta mana kai ma Allah Ubangiji ya faranta maka, Allah ya ji ƙan iyaye da kakanni, murmushi Daddy yayi ya ce "Kai haba don Allah ku tashi mana, da ni da ku ai mun zama ɗaya ta sanadiyyar yaranmu, yanzu abin da nake so da ku shine ku tashi ku je ku shirya domin a satin nan nake son su Ammar su wuce don su karɓi horo da wuri." Tashi tsaye suka yi "To Alhaji mu zamu wuce Allah ya saka da alkhairi" kallonsu Daddy yayi ya ce "To yanzu zaku wuce?" "E wallahi Alhaji zamu fita neman abinci ne" "To ku tsaya ina zuwa" shiga cikin gidan yayi bai daɗe ba, sai ga shi da kuɗi ɗauri biyu ya miƙawa Aisar ɗaya ya miƙawa Sa'ad ɗaya, sannan ya ce "Allah ya kiyaye ya bayar da sa'a" saboda jin daɗi su Aisar kasa yin magana suka yi, suka rasa da bakin da za su yiwa Daddy godiya, domin samun irinsu sai an tona. Murmushi Daddy yayi "Daga yau na ɗauki nauyin karatun Anas, insha Allahu har ya gama ba za'a nemi komai daga wurinku ba." Godiya suka yiwa Daddy sosai sannan suka yi masa sallama suka tafi, amma ba su tafi tare da Anas ba, domin Daddy ya ce "A bar shi tare da Ammar idan yamma ta yi sai ta taho."

_*WAYE DADDY*_
Asalin sunansa shine Abubakar, haifaffen jahar Kaduna ne a ƙaramar hukumar Rigasa. Ya gaji dukiya mai yawa a wajen mahaifinsa, kasuwanci ne ya kawo shi garin Kano. Har Allah ya haɗa shi da Aminatu ta je wani ƙaton Mall ɗin shi sayayya, anan ya ganta ya ji ta burge shi, bai tsaya wani ɓata lokaci ba ya tunkare ta, bai sha wahala sosai ba wajen shawo kanta. Ba su ɗauki wani lokaci ba manya suka shiga cikin maganar, aka daidaita sai ga Aminatu ta zama matar Alhaji Abubakar. Shekararsu biyar da yin aure sannan Allah ya albarkaci Amina da samun juna biyu, murna a wajen Alhaji Abubakar ba ta faɗuwa domin sai da yayi ta yiwa ma'aikatansa kyatuttuka saboda burinshi ya cika zai samu zuri'a tare da Aminatu, ƴar Aljanna, domin haka yake kiranta saboda tsananin biyayya da kuma kyautata masa da take yi. A ranar wata Juma'a da safe Amintu ta tashi da matsanancin ciwon mara, tun tana jurewa har ta gagara, tana cikin kitchen tana haɗa musu breakfast Alhaji Abubakar yana zaune a falo ya jiyo ihunta! Ba tare da tsayawa ɓata lokaci ba, yayi cikin kitchen ɗin a guje, a kwance ya tarar da ita jini yana bin ƙafafunta. Da taimakon wata ƴar aikinsu suka canja mata kaya, sannan suka saka ta a mota sai Asibiti, da sauri likitoci suka hau kanta don ceto rayuwarta. Sai da suka ɗauki dogon lokaci sannan babban likitan ya fito, ya ce "Alhaji ya biyo shi office" da sauri Alhaji Abubakar ya bi shi, domin ya matsu ya ji halin da matarshi take ciki, bayan likitan ya zauna sai ya dubi Alhaji Abubakar ya ce "Ka daina damuwa haka Alhaji, ba wata matsala ce babba ba haihuwa ce ta zowa matarka amma ta zubar da jini da yawa, don haka muna buƙatar jini yanzu cikin gaggawa" da sauri Alhaji Abubakar ya ce "Likita me kake jira ba gani ba a ɗauka a jikina mana" murmushi likita yayi ya ce "Ai sai mun gwada idan yayi dai-dai da nata sai mu ɗauka." An gwada jinin Alhaji cikin ikon Allah yayi dai-dai dana matarsa Aminatu, aka saka mata, jinin yana ƙarewa wata naƙudar ta sake zuwar mata. Bata daɗe tana yi ba ta haifo santalelen jaririnta, mai kama da ita sak, Alhaji Abubakar saboda tsananin murna rasa inda zai saka kansa yayi, bayan an kaita ɗakin hutu ya je ya ganta ga jaririn a gefenta cikin tawul yana ta barci abinsa. Cike da zumuɗi Alhaji Abubakar ya sunkuya ya ɗauke shi ya sumbace shi a goshi......

To be continue......📝📝📝

_*Hussaini Yusuf*_
[12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*
*NA*

*HUSSAINI YUSUF*

*______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*______________________________*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.