Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 17 of 25
*Page 33/34*
Bayan sun dawo gida, Anas da Nasreen da Basma sai faman murna suke yi, gani suke yi kamar su janƴo gobe saboda zumuɗi. Aisar yana dawo wa daga kasuwa Safna ba ta bar shi ya huta ba, ta shiga ba shi labarin makarantar da aka kaisu. Haka Nasreen ma Anas shi kuwa da ya zamana yafi su wayo, ko kaɗan bai nuna wa Aisar ya matsu gobe ta yi ba, har sai da Aisar ya tambaye shi sannan yayi masa bayanin komai har class ɗin da aka saka shi sai da ya faɗawa Aisar, ba ƙaramin daɗi Aisar ya ji a cikin ransa ba, kullum burinsa da fatansa shine ya cika wa Anas babban burinsa na zama soja.
Washe gari da sassafe su Anas suka tashi, da wuri Rahila ta ɗora musu tea, domin su yi breakfast da wuri kafin lokacin tafiya makarantar yayi. ƙarfe bakwai da rabi dai-dai, Sa'ad ya shigo lungun nasu, hannunsa riƙe da Basma ta sha uniform ɗinta, sun yi mata kyau sosai, ga school bag a bayanta, ban da kallonta babu abin da Anas yake yi, tunda ya zo gidan nan Basma take burge shi, kome tayi shi a wajen shi dai-dai ne, haka kawai ya ji yana ƙaunar yarinyar sosai a cikin ransa. Amma saboda Anas irin mutanen nan ne, marasa yawan magana, ba za ka taɓa fahimtar wani abu game da shi ba, bashi da surutu irin na sauran yara, ko da yaushe a nutse yake komai na shi yana aiwatar da shi ne cikin sanyi da nutsuwa, kana kallonsa zaka tabbatar a jininsa sanyi da nutsuwa suke.
Amma fa idan aka ɓata wa Anas rai, to mai rarrashin shi ya hakura sai yayi da gaske, domin idan yayi fushi yana daɗewa bai huce ba, amma kafin yayi fushin ne a wahala.
Kallonsu Anas Sa'ad yayi yace "wai ba ku gama breakfast din ba ne?" da sauri Nasreen tace "Mun gama" Aisar yace "Kuyi sauri ku shirya kun ga yana ta faman jiranku, kada ku makara a makarantar".
Anas tashi yayi ya shiga cikin wani É—aki, da alamu dai anan ne yake kwana, bai daÉ—e a ciki ba sai ga shi ya fito a cikin shirinsa na makaranta, kayan sun yi masa kyau sosai, su Safna ma ba su daÉ—e ba, Rahila ta gama shirya su, fitowa suka yi fuskokinsu dauke da murmushi na farinciki yau za'a shiga school.
Kama hannunsu Sa'ad yayi suka fita, kai tsaye motar shi ya bude musu suka shiga, Safna da Nasreen da Basma, a baya shi kuma Anas Sa'ad yace "ya shiga gaba."
Aisar yana tsaye yana ta sakin wani murmushi, yana ta aikin É—aga musu hannu har Sa'ad ya tashi motar ya tafi, Aisar bai daina murmushi ba, burinsa ya cika babu abin da zai ce da Sa'ad sai dai yayi ta masa addu'a, domin ya cika masa burinsa a ransa yake ji Anas zai cika burinshi ya zama babban soja a kasar nan.
Sai da ya daina hango motar sannan ya juya ya shiga gida, don ya shirya shi ma ya tafi neman abincin shi.
***** ******* *****
Yayin da suka shigo cikin makarantar, kai tsaye office É—in Headmaster suka wuce, suna shiga da murnarsa ya tare su yana musu barka da zuwa. Nuna masu kujera yayi yace su zauna, bayan sun gama zaunawa, sai ya dauki waya ya kira wani, two minute sai ga wasu matasan malamai sun shigo cikin office din, kallonsu Head master din yayi yace "Kabir ga sabon dalibi nan na kawo maka ka kai shi cikin ajinka, sunan shi Anas Abdulmalik." Murmushi malamin yayi yace "masha Allah sannan ya kalli Anas yace "Anas ta so mu tafi na gabatar da kai a ajin" tashi Anas yayi ya bi shi a baya, suka fita, sannan ya sake kallon daya malamin yace "kai kuma ga sababbin dalibai nan, murmushi malamin yayi ya kalli su Safna yace "yan'mata ya sunanku?"
Kafin su yi magana Nasreen ta riga su, tace "ni dai sunana Nasreen Aisar" Safna ma tace "ni kuma Safnat Abdul maleek" sannan ya kalli Basma yace "ke kuma fa ƴan'mata kin yi shiru" ranta a ɓace tace "Lailat Sa'ad" kallonta Sa'ad yayi yace "Basma me yake damunki ne?" kamar zata yi kuka tace "ba sune suka ƙi bari na na faɗa wa Malam sunana ba; ta faɗa tana nuna Safna da Nasreen, kowa a wajen sai da Basma ta ba shi dariya, sosai ta burge Malamin nasu, a ransa yake jin yarinyar zata yi kai sosai ko daga maganarta zaka gane hakan.
Tafiya da su malamin yayi, suna shiga class É—in gaba daya Æ´an class din suka mike a tare suka ce "good morning Uncle!" kallonsu yayi yace "Morning student, how are you?" hade baki suka yi a tare suka ce " We are fine Uncle" sai bayan kamar minti biyar sannan yace "sit down student" anan ma a tare suka ce "Thank you Uncle" sannan kowanen su ya zauna.
Yanayin yadda É—aliban suka gaisar da malaminsu ne burge su Safna, sai faman sakin murmushi suke yi, suna fatan su ma su iya wannan turancin da Æ´an ajin suka yiwa Malam.
Kallon sauran yan ajin malam yayi yace "Alhamdulillah mun samu ƙarin new commers, a cikin wannan class din namu, ina fata zaku karɓe su hannu bibbiyu ku ba su wajen zama?" A tare suka ce "insha Allahu Uncle" sannan ya kalli su Safna yace "yanzu za su faɗa muku sunayen su ɗaya bayan ɗaya domin yanzu sun zama abokanku kuma yan'uwanku.
Nuna Safna yayi yace "ƴan mata kalli ƴan aji ki fada musu sunanki" muryarta na rawa saboda bata saba magana a cikin mutane haka ba tace "Sunana Safnat Abdul Maleek" nan da nan kuwa ta ji malam yace "clap for her" nan da nan ajin ya ɗauki sautin raf! raf!! raf!!! haka ba ƙaramin yiwa Safna da su Nasreen dadi yayi ba. Sannan ya kalli Basma yace "ƴan'mata ke kuma fa yaya sunanki?" kallon yan ajin Basma ta yi tace "sunana Lailat Sa'ad" nan ita ma aka tafa mata, sannan Nasreen ita ma tace "sunana Nasreen Aisar" nan take ita ma class din suka yi mata tafin.
Sannan malam yace "monitor ya basu wajen zama" wani desk ya nuna musu wanda babu kowa akai, zuwa suka yi suka zauna, sannan malam ya juya board din ajin ya fara rubutu.
••••••••••••••••
Anas kuwa bayan sun shiga cikin ajin, sai malamin ya umarce shi da ya bayyanawa sauran daliban sunansa, amma da turanci zai faÉ—a, murmushi Anas yayi sannan ya kalli yan ajin da suke zaune yace "my name is Anas Abdul Maleek" tafi suka yi masa sannan malam ya nuna masa wata kujera yace "ya je ya zauna akai kafin, a samo masa na sa, tun da me ita baya nan.
Zuwa yayi ya zauna kusa da wani yaro, kallon shi yaron yayi ya sakarwa Anas murmushi yace "abokina mu gaisa mana" cikin sanyin jiki Anas ya mika masa hannun suka yi musabaha, sannan yaron ya sake cewa Anas"sunana Ammar da fatan za mu zama abokan juna" sai a sannan Anas ya saki murmushi yace "ba matsala Ammar tun da yanzu mun zama daya, tun da ka zama maƙwabcina, dole ne mu ƙulla zumunci. Hira ce sosai ta ɓarke tsakanin Anas da Ammar, idan ka gan su sai kayi zaton dama can sun san juna.
Su Nasreen ma an yi sababbin ƙawaye a makaranta, sosai Nasreen ta zage sai zuba musu surutu take yi, kamar dama can ta san su, Safna da Basma kuwa su ba su fiye yawan magana ba, sai ta kama su yi magana sannan kake jin bakinsu, sai dai kome Nasreen ta tambaye su, sai dai su bita da E ko a'a da haka dai har malam ya shigo, ya kira su Safna ya shigar da sunansu cikin register.
Ƙararrawar tashi aka buga, nan da nan kuwa naga ɗalibai ta ko'ina suna fitowa, Anas sai hangen su Safna yake, amma ko kaɗan bai hango su ba, kai tsaye sai ya tafi bakin gate ya tsaya, yana ta kallon masu wucewa ko zai ga su Safna a ciki amma bai gan su ba. Sai da kowa ya gama fita daga makarantar, amma bai ga ko alamun su Safna ba da sauri yayi cikin makarantar, yana kiransu, amma shiru babu su babu alamun su..........
To be continue........
Comment and share
_*Hussain Yusuf*_
07069475482.
[12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*
*NA*
*HUSSAINI YUSUF*
*______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ƴancinmu*
*______________________________*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.