Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 14 of 25
*Page 27/28*
Koda ya fito ya iske su a tsaye suna jiransa, murmushi yayi yace "kar ku ga na daɗe don Allah kuyi haƙuri akwai abin da ya tsare ni. "A'a babu komai kar ka damu" Aisar ya faɗa yana mai sakarwa Sa'id murmushi.Koda suka shiga gidan, sai ya nuna musu wani lungu me ɗauke da ɗakuna uku, sai kitchen da banɗaki, nuna musu yayi yace amma ɗakunan sun yi ƙura sai sun gyara. Murmushi Aisar yayi yace "kar ka damu babu komai wallahi zamu gyara."
Tashi Sa'id yayi ya fita don ya ba su damar gyara wajen sosai, zuwa yayi ya ga Ammi tana alwala, Husna kuma tana ta fama da hura wuta zata É—ora abinci, da mamaki ya kalleta yace "Husna har yanzu ba ki gama girki ba ne har magriba?"
Murmushi ta yi ta kalle shi tace "gani nayi mun yi baƙi shine naga abincin da na dafa ba zai ishe mu ba, shi yasa na sake ɗorawa domin ya isa, murmushin jin daɗi yayi yace "Allah ya saka miki da gidan Aljanna matata, kina son duk abinda nake so haka kuma kina ƙin duk abinda nake ƙi, kuma kullum burinki shine ki gan ni a cikin farin ciki.
Rufe fuskarta ta yi da hannayenta, alamun jin kunƴa ɗaukar buta yayi zai shiga banɗaki yace "ta ɗauko bokiti a kai wa baƙin ruwa su yi alwala domin lokacin sallar magriba yayi.
Da sauri kuwa ta tashi ta je ta kitchen ɗin su, ta ɗauko wani sabon bokitin Ƙarfe, ta kunna famfo ta tari ruwa, ta haɗa da butoci guda biyu, tare da kofi, ta ɗauka ta nufi wajen su Aisar don ta kai musu su yi alwala.
Tana shiga ta tarar da su Ummu nisreen tana shara, su Inna kuma suna fito da kayansu, suna shigar da su cikin É—akin.
Har ƙasa ta tsugunna ta gaishe da su, cike da kulawa suka amsa, fuska a sake sannan tace "ga ruwa nan kuyi alwala" bata jira me za su ce ba ta tashi ta nufi hanƴar fita, sai jero mata godiya su Iya suke yi amma ko kaɗan bata waigo ba balle ta amsa.
Inna ce ta dubi Iya tace "gaskiya ashe ba ƙarya ake yi wa mutanen kano ba, suna da karrama baƙo, sosai abin nan da suka yi mana ko wajen ƴan'uwanmu muka zo iyakar abin da za suyi mana kenan.
Iya ta ajiye ajiyar zuciya tace "ke dai bari, ai na gama tsinkewa da al'amarin Kanawa ashe da gaske ne da ake cewa mutane ne masu karrama baƙo, ki kalli irin karramawar da aka yi mana.
Aisar ne ya É—auki É—aya daga cikin butocin, ya É—ebi ruwan da Husna ta kawo musu, ya shiga cikin banÉ—aki, bayan ya fito ya É—aura alwala, don lokacin sai kiran sallah ka ke ji a masallatan da suke cikin unguwar.
Bayan ya gama alwalar ya nufi ƙofar gida, a hanƴar fita ya haɗu da Sa'id shi ma zai tafi masallacin, murmushi Sa'id yayi da ya ga Aisar yace "kai ma masallacin ka nufa kenan?" Aisar yace "E wallahi can na nufa, duk da ban san ma inda masallacin yake ba.
Murmishi Sa'id yayi yace "ka ji ka, ko babu ni idan ka fita ai zaka ga mutane suna tafiya masallacin" dariya suka saka gaba ɗaya sannan suka fice daga gidan, cikin sauri suke tafiya don har an fara tayar da iƙama.
Bayan an idar da sallar an yi addu'a an shafa, Aisar tare da Sa'id suka fito daga masallacin, suka nufo gida, da suka zo ƙofar gidan, sai Sa'id yace "Aisar ya tsaya za su yi magana" babu wata jayayya Aisar ya tsaya, nuna musu wani ɗan dakali yayi yace su je su zauna anan.
Bayan sun zauna Sa'ad ya dubi Aisar yace "haƙiƙa tun da nake ban taɓa haɗuwa da mutumin da ya shiga raina, nake kuma matuƙar jin tausayinsa fiye da kai ba, ya nuna Aisar sannan ya ci gaba da cewa.
"Batun neman inda zaka zauna ka daina, inda na sauke ku na ba ku shi ku zauna, har lokacin da Allah zai hore maka kai ma kayi naka.
Aisar ya rasa da bakin da zai gode wa Sa'id, saboda tsananin murna, ji yake kamar Sa'@d É—in É—an'uwansa ne na jini.
Nan dai suka zauna, suna ta hira har aka gama abinci, Sa'ad da kan shi ya je ya fito musu da abinci, tare suka ci, suka ɗan taɓa hira lokacin har an fara kiran sallar Isha.
Bayan an idar da sallar sai suka yi wa junansu sai da safe sannan kowa ya nufi ɓangarensa.
Yayin da Aisar ya shiga cikin gidan, sai ya iske su Iya har sun yi barci, a ɗakinsu da suka zaɓa, kai tsaye ɗakin matarsa Rahila ya nufa.
Yana shiga ya gan ta akan sallaya tana sallah, samun waje yayi ya zauna ya zuba tagumi.
Bayan ta idar da sallar, ta yi addu'ointa ta gama, sai ta juyo ta kalli inda yake, kan shi a sunkuye.
Cikin sanÆ´in murya tace "Abu Nisreen lafiya kuwa ka yi tagumi?" A hankali ya da kanshi ya dube ta yace "wallahi ina tunanin sana'ar da ya kamata na yi ne."
Murmushi ta yi tace "ka kwantar da hankalinka gobe idan Allah ya kai mu, sai ka tambayi me gidan nan, sai yayi maka bayanin sana'ar da ya kamata ka yi tun da shi mazaunin garin ne."
Sai da yayi tunani sosai, sannan yace "na amince da wannan shawarar ta ki matata insha Allahu zan jarraba na gani."
Daga nan suka yi addu'a suka kwanta, sosai suka samu farinciki a wannan daren, sun daÉ—e suna shan soyayya, sai wajen 2:30am suka samu barci ya É—auke su.
Washe gari da sassafe Aisar ya je ya gaishe da su Inna, sannan ya fita ya je ya gaisar da Ammi, sosai Ammi ta yaba da hankalin Aisar ta ji ya burge ta sosai.
Bayan ya gama gaida su, sai ga Sa'ad ya fito daga ɗaki, yana ganin Aisar ya saki murmushi tare da miƙa masa hannu suka yi musabaha.
Bayan sun gama gaisawa, Husna ma ta fito daga ɗakinta, ta tsugunna har ƙasa ta gaisar da Aisar, cike da kulawa ya amsa mata, sannan ya juyar a kallonsa kan Sa'ad, yace "ina son idan baza ka damu ba zamu yi magana."
Wani ɗan madaidaicin falo Sa'ad ya ja hannun Aisar suka shiga, kowanne ya samu kujera ya zauna, suna masu fuskantar juna, cikin nutsuwa Aisar ya dubi Sa'ad yace "abinda yasa na zaɓi na zauan a Kano shine saboda na ji labarin suna da sana'oi da yawa sannan kuma ga tarin albarka idan ka kasa zaka sayar. Shi yasa nace zan shawarce ka ka bani shawarar sana'ar da ya kamata na fara yi a yanzu, domin muna ɗora maka nauyi, jiya zuwa yau ɗin nan.
Murmushi Sa'ad ya saki yace "me yasa zaka faɗi haka? bayan ka san baƙunta ku ka yi, ka ga kuwa dole ne na ciyar da ku domin nauyin ku ya hau kaina, kuma Hausawa sun ce baƙonka Annabinka.Sannan batun sana'ar da yakamata ka fara, idan har kana da jari, to ka zo na kai ka wajen wani abokina, a Wambai yana sayar da kaya gwanjo, sai na haɗa ka da shi ka sara kaje ka shiga cikin kasuwa ka sayar, ita ma wannan sana'ar ta gwanjo, indai ka shigeta a sa'a to akwai albarka sosai a cikinta.
Nan take kuwa Aisar yace ya amince da wannan shawarar, ba su bar wajen ba sai da suka tsaya akan suna yin breakfast idan Sa'ad zai fita to tare za su fita ya kai shi wajen abokinsa domin ya fara jarraba sana'ar gwanjo.
Sosai Aisar ya rinƙa zubawa Sa'ad godiya, sannan ya sake cewa "yana son kuma ya kai su Anas makarantar boko da Islamiyya, Sa'ad yace "wannan kar ka damu insha Allahu ina da niyyar kai su, amma ka bari sai ranar monday sabida yanzu ka ga ƙarshen sati ne.
Sosai Aisar yayi murna nan take kuwa ya tashi ya nufi wajen Rahila (Ummu Nisreen) domin ya shada mata abin da suka tsara shi da Sa'ad mutumin kirki don haka suke kiransa...........
To be continue...........
Comment and share
_Hussain Yusuf_
[12/9, 4:36 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*
*NA*
*HUSSAIN YUSUF*
*______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*_____________________________*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.