Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 25

*Page 37/38*

*Z* ama Ammar yayi yace "to bani goron sai na faɗa maka" murmushi Anas yayi yace "idan kuma albishir ɗin bai yi min daɗi ba fa?" "ai wannan albishir ɗin da zan yi maka ba'a taɓa yi maka irin shi ba" kallon shi Anas yayi yace "don Allah kayi sauri ka faɗa mini indai yayi min daɗi ni na san kyautar da zan yi maka".

Murmushi kawai Ammar yayi yace "Anas ka godewa Allah domin burinka yana gab da cika, Daddy na yace tare da kai zai nemo mana admission a makarantar horon sojoji ta Kaduna" a zabure Anas ya miƙe tsaye yana yi wa Ammar kallon tuhuma, zama yayi ya kalli Ammar ɗin yace "ta yaya Daddyn ka ya san ni da har zai samo min admission?".

Murmushi Ammar yayi yace "Anas kenan ai kullum idan na zauna da Daddy na babu labarin da nake ba shi face naka" da haka har ya san ka a baki amma bai taɓa ganinka ba, kuma nace kaine kake taimaka mini a makaranta, sosai kana da kirki.

Haka ne yasa duk lokacin da na yabe ka, sai Daddy ma ya yabe ka, kuma na ce masa burinmu ni da kai iri É—aya ne, ma'ana ni da kai duk sojoji muke son mu zama.

Da yace min zai nemo mini admission na shiga makarantar horon sojoji, sai na dage nace tare da kai za'a nemo mana, idan kuwa ba haka ba na fasa yin sojan gaba É—aya.

Dole Daddy ya haƙura zai nemo mana a tare ka ga sai mu wuce ko? har hawaye sai da Anas ya zubar don murna. Duban Ammar yayi yace "Ammar tashi ka raka ni na je na yiwa Daddynka godiya."

Da sauri Ammar ya dakatar da shi ya ce "Yanzu Daddy na baya gida, sai dai ka bari a ƙarshen satin nan yake zaman gida, da kaina zan zo na raka ka wajen shi ka yi masa godiyar, yanzu ni dai ka bani goron albishir ɗin da ka ce zaka ba ni." Murmushi Anas yayi yace "jira ni anan ina zuwa" sannan ya shige cikin gidan, kai tsaye ɗakinsa ya nufa, dube-dube yake ta yi ya rasa me zai ɗauko ya kawo wa Ammar ɗin, saboda ya matuƙar burge shi ba kadan ba.

Wani hoto ya ɗauko wanda shi da Ammar ɗin ne a jiki sun yi kyau sosai, kamar ƴaƴan Larabawa. Fitowa yayi ya samu Ammar ɗin a ƙofar gida yana jiransa, yana zuwa ya miƙa masa hoton yace "ungo wannan hoton da ban yi niyyar ba ka ba amma saboda wannan albishir ɗin da kayi mini na mallaka maka shi. Karɓar hoton Ammar yayi yana sakin wani murmushi, ya dubi Anas yace "a ina ka ɗauki hoton nan? don ni ban da shi ba gaskiya".
Murmushi Anas yayi yace "yanzu kai har ka manta wajen da muka yi hoton nan?" gyaɗa masa kai Ammar yayi "ka tuna lokacin da muka tafi yawon shaƙatawa a makaranta?" da sauri Ammar yace "wallahi na tuna, a wajen TIGA DAM ko?".
Dariya Anas ya saki yace "ashe ba ka manta ba, to a lokacin da aka ta yi mana hotunan nan, anan aka ɗauke mu. Inda na samo hoton kuwa wata rana na shiga office ɗin Principal ina share masa shi, babu kowa a ciki sai naga wannan hoton, ni kuwa da naga mune a jikin hoton kuma mun yi kyau sosai, sai na ɗauke shi na ɓoye shi a cikin jakata, da so nake sai mun girma in nuna maka shi na san zaka yi farinciki idan ka gan shi.
Dariya Ammar yayi yace "ai ba zan raba ka da wannan hoton
ba, yanzu ka je ka ajiye shi idan na samu lokaci zan zo ka raka ni mu kai shi a wanko mana wani su zama biyu kaga kenan ni É—aya kai É—aya kowa a cikinmu ya mallaka.

Bayan tafiyar Ammar Anas wuni yayi da farinciki, ya matsu Abban shi ya dawo ya shaida musu, ko kadan bai yi gangancin faÉ—awa su Inna ba don yana tsoron kada su riga shi faÉ—awa Abbansu. Bayan sallar Isha'i sai ga Aisar ya dawo daga kasuwa, dama yayi sallarsa kafin ya shigo ciki, yana shigowa abincin Rahila ta kawo masa zama yayi ya fara ci.

Yana cikin cin abincin Anas ya shigo, har ƙasa ya tsugunna ya gaisar da shi yayi masa sannu da zuwa, cike da kulawa ya amsa yana mai shafa kan Anas ɗin.

Bayan ya gama cin abincin, ya wanke hannunsa, sannan ya dubi Anas yace "ya karatun naku?" sunkuyar da kansa ƙasa yayi yace Alhamdulillah Abba, dama akwai albishir ɗin da nake son nayi maka.

Da sauri Aisar ya kalli Anas yayi murmushi yace "to ina jin ka Anas" kansa yana ƙasa ya fara magana dama ina so na faɗa maka Daddin Ammar yace zai samo min admissin a makarantar horar da sojoji ta Kaduna.

Da sauri Aisar ya tashi daga kishinhiÉ—en da yake, ya kalli Anas ya ce; "Waye Ammar kuma waye Daddinsa da har zai biya maka kuÉ—i alhalin ni ban san shi ba." Murmushi Anas yayi ya ce; "Ai abokina ne a makaranta, kullum idan na kawo shi ku gaisa ba na samun ka a gida, sai dai na kawo shi wajen su Inna da Iya su gaisa sannan ya tafi. Amma ya ce; "In an jima zai zo ya raka ni wajen Daddynsa na yi masa godiya a bisa abin alkhairin da yayi mana, ka ga ai sai mu tafi tare ko."

Murmushi Aisar yayi ya ce; "Masha Allah yanzu kenan su Innarka sun san shi Ammar É—in? E mana Abba duk sun san shi mutumin kirki ne, duk faÉ—in makarantar nan shi kaÉ—ai ne abokina, su Safna ma duk sun san shi."

Girgiza kai Aisar yayi ya ce; "Allah ya kai mu goben sai mu je mu yiwa Daddinnasa godiya ko?" Murmushi Anas yayi ya ce; "Na gode Abbana Allah Ubangiji ya nuna mana goben lafiya" Amin summa amin Anas ayi maza aje a kwanta ka ji, Allah yayi maka albarka.

Bayan Anas ya tafi ɗakinsa ya kwanta, sai ga Abban Basma ya dawo daga wajen neman abincinsa, a ƙofar gida ya ajiye motarsa, sannan ya shigo cikin gidan. Bayan ya shiga wajen iyalinsa, jim kaɗan ya fito, ya nufi wajen Aisar, shi kaɗai ya tarar a wajen a kishingiɗe akan tabarma yana sauraron rediyo. Yana ganin Sa'ad ya tashi zaune yana sakin wani murmushi, ya nunawa Sa'ad tabarmar da yake kai a zaune ya ce; "Bismillah zauna mana" babu musu kuwa Sa'ad ya zauna kusa da Aisar ɗin suka fara hirarsu irin ta abokai, waɗanda suka yarda da junansu.

A cikin hirar tasu ne Aisar yake faɗawa Sa'ad mahaifin abokin Anas zai samo mishi admission a makarantar horon sojoji ta Kaduna, sosai Sa'ad yayi murna har da hawaye duk da ba shine ya haifi Anas ba, yana matuƙar so da ƙaunar yaron tamkar shine ya haife shi. Dubansa ya kai wajen Aisar ya ce; "A ina mahaifin abokin nasa yake gobe idan Allah ya kai mu sa mu je mu yi masa godiya?" Girgiza kai Aisar yayi ya ce; "Wallahi ban taɓa ganin shi ba, kai ni ban san ma yana da wani aboki ba sai yau ɗin nan na dawo daga kasuwa ya faɗa mini." Amma ya ce; "Wai abokin nasa zai zo gobe ya raka shi wajen mahaifin nasa yayi masa godiya, ka ga idan ya zo zai raka shi sai mu tafi tare ko ya ka gani?".

Washe gari da safe ta kama Asabar ɗin ƙarshen wata, saboda haka zaka samu duk kusan ma'aikata manya da ƙanana suna gida.

Mahaifin Ammar ne a zaune a wani ƙayataccen falonsa da yake hutawa a irin wannan lokacin, kallon wani wa'azi yake yi a tashar SUNNAH TV. Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa da nutsuwarsa akan wa'azin da wani shahararren malami yake gabatarwa, akan ta'addanci da illolinsa.

Kwatsam! Ya ga Ammar ya faɗo cikin falon a guje, yana zuwa bai zame ko'ina ba sai akan cinƴar Mahaifinsa. Kallon shi Mahaifin nasa yayi ya ce; "Haba Ammar sai yaushe za ka girma ne, ko so kake ka karya mini cinyoyina tun da sauran ƙwarina?" Murmushi Ammar yayi ya ce; "Wane ni Daddy ai ban isa na karya ka ba, idan kuwa har na karya ka to nima sai na karya kaina."

Dariya sosai Daddy yake yi barkwancin Ammar yana matuƙar burge shi, idan yana gida ba shi da abokin hira da ya wuce tilon ɗansa wato Ammar. Kallon Ammar Daddy yayi ya ga bakinsa yana motsi, da alamu dai akwai abin da yake son cewa, murmushi ya sakar wa Ammar ya ce; "Me kake son faɗa ne Ammar?"

Sosa kai yayi in ina ya fara magana "dam...dam.....dama, sai kuma yayi shiru ya sunkuyar da kansa ƙasa." "Ammar kenan sarkin kunya, ka buɗe murya ka faɗa min abin da yake cikin ranka, to kai yanzu Ammar idan ba ka faɗa min ba wa ka ke da shi da zaka faɗa masa? Maza ina sauraron ka."

Muryarsa har rawa ta rinƙa yi nan take ya fara magana "Dama Daddy Anas ne da na shaida masa, za ka nemo mana admission tare shine ya ce idan kana gida, na faɗa masa zai zo yayi maka godiya, murmushi Daddy yayi ya ce; "Akan wannan abun ne kake ta faman sunne min kai, kamar ka ga wata budurwarka?" to maza ka je ka shaida masa ina gida, dama ina son na ga wannan Anas ɗin da ka ke ta faman bani labarinshi.

Da gudu Ammar ya fita daga cikin falon, kai tsaye ƙofar gate ya nufa ya fita, yana zuwa bakin titi ya tari Napep sai unguwar Darmanawa domin ya shaidawa Anas yanzun nan ya zo ya ga Daddynsa yayi masa godiya....✍️

To be continue......📝📝📝
Comment and share

_*Hussain Yusuf*_
07069475482.
[12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*

*NA*
*HUSSAINI YUSUF*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

_Kuyi haƙurin rashin ji na da kuka yi kwana biyu, wata ƴar matsala ce amma insha Allahu yanzu komai ya dai-dai ta_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.