Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 25

*Page 13&14*

Murmushi Aisar yayi ya shafa kan Anas yace "Anas me yasa kake son zama soja?" Saboda na ɗauki fansar ran iyayena da mugayen ƴanta'addan can da suka kashe iyayena, kuma na kawo ƙarshen ta'addanci da zalunci a ƙasata.

Sosai Anas ya burge Aisar, saboda yana matuƙar son yaro marar tsoro saboda haka ya sha alwashin ko zai rasa kome na shi, sai ya taimakawa Anas ya cika burinshi na zama soja. Kallon Safna yayi yace "ke kuma ƴan'mata me kike son ki zama anan gaba?"

Kwantar da kai ta yi tace "ni burina na ga Innata sannan na faÉ—a mata abinda nake son zama, don Allah ka kai ni wajen Innata na ganta." Sosai ta bai wa Aisar tausayi, rarrashinta yayi yace "gobe da safe zai kaita wajen Innar ta ta."

Washe baki Safna ta yi tace "Nagode Abbana daga yau ka zama Abbana tunda Baffa ya mutu kai ne Abbana" Murmushin jin daɗi yayi ya dubi Safna yace "Da yau to ki rinƙa kirana da Abbanki."

Da sauri tace "to Abba" tana sakin wani murmushi da ya saka dimple ɗinta lotsawa. Haƙiƙa Safna yarinƴa ce don a shekaru ba ta fi shekara takwas ba, shi kuma Anas zai yi shekara goma sha huɗu shi yasa yake da wayo da kuma hankali.

Shi kansa Anas ya san Aisar ya faÉ—awa Safna zai kaita wajen Innarta ne, don kawai ya kwantar mata da hankali, amma shi yasan yanzu Innarsu ta daÉ—e da mutuwa.

Shiga cikin bukkar Aisar yayi, bai daɗe ba ya fito da wata jaka a hannunsa, kunce ƙullin jakar yayi gurasa ce da busashshen kifi a ciki. Ruwa ya ɗebo ya jiƙa gurasar da kifin, har suka yi laushi, sannan ya ɗauko ya zo ya hura wuta, ya sake gasa kifin da gurasar har suka yi ɗumi, damƙawa kowa gurasa uku kifin da ya kasance manya ya ba su bibiyu.

Ci suke yi suna nishaɗi abinsu, dama ba ƙaramin yunwa suke ji ba yanzu sun samu wanda zai taimaka musu a rayuwa, da santi ya ɗebi Safna bata san lokacin da ta dubi Anas ba tace "Yaya Anas dama na faɗa maka mu taimaka wa jaririn can, mu ma Allah zai kawo me taimaka mana, kuma ga shi mun samu da ba mu taimaka masa ba da yanzu mu ma Allah bai taimake mu ba.

Dariya Anas da Aisar suka saka, sannan Aisar ya dubi Safna yace "A'a Safna ko da ba ku taimake shi ba, Allah zai kawo wanda zai taimaka masa, kuma zai taimake ku saboda kuna buƙatar taimakon, ai Allah shi ba azzalumin bawansa ba ne."

Yana kai wa nan a zancensa, ya tashi ya shiga cikin bukkar. Bai daɗe a ciki ba, sai ga shi ya fito rungume da jaririn ya rufe shi da wata busashshiyar fatar Damisa, saboda zafin rana. Sannan ɗaya hannunsa riƙe da jakar farautansa, kallon su Anas yayi yace "ku taso mu tafi cikin gari, da sai gobe na so mu tafi saboda wannan jaririn nace mu tafi yau.

Tashi suka yi Anas yace "Abba kawo jakar na riƙe maka" a'a Anas ku ji da tafiyar ma da zamu yi don da ɗan nisa kafin mu isa ƙauyen namu. Saka su a gaba yayi shi kuma ya rinƙa bin su a baya, sai da suka fita daga surƙuƙiyar nan sannan suka faɗa wata babbar hanƴa.

Hanƴar tana da faɗi sosai ga shi cike take da yashi, amma a haka suke ta tafiya, idan ya ga sun gaji sai ya tsaya su huta sannan su cigaba da tafiya, sai doshin magariba suka isa wani ɗan ƙaramin ƙauye.

Murmushi Aisar ya saki ya dubi su Anas da Safna yace "kun ga ɗan ƙauyen namu ko?" dariya Anas yayi yace "Abba ai nan yafi ƙarfin a kira shi ƙauye."

Tafiya suke yi a cikin ƙauyen, har suka ƙaraso ƙofar wani gida, wanda aka zagaye shi da dangar kara daga gaban gidan kuma aka yi shi da bulon ƙasa, har da zaure da kuma ɗaki a cikin zauren.

Lokacin da suka shiga cikin gidan, babu kowa a tsakar gidan motsin mutum, suka ji a cikin banɗakin da yake tsakar gidan. Nuna musu wani itace yayi yace su zauna akai, shi kuma ya shiga cikin wani ɗaki ya ajiye kayan farautarsa ya fito ya zauna kusa da su ya ƙurawa fuskar jaririn da yake ta sharar barci abinsa idanu.

Ba daɗewa sai ga matar gidan ta fito daga banɗakin, sai faman yarfe ruwa take yi a jikinta, hankalinta bai kai inda su Anas suke ba. A hankali ta ɗago idanunta, ta sauke su akan su Anas da Safna sai kuma mijinta riƙe da jariri yana ta aikin kallonsa.

A hankali tace *"Abu Nisreen* lafiya na ga ka dawo, ba lokacin da ka saba dawo ba? Da sauri ya É—ago da kansa ya kalleta ya sakar mata wani murmushi mai taushi yace "haba *Ummu Nisreen* ga dalilin da yasa na dawo yanzu, ya faÉ—a yana nuna su Anas da Safna.

Ta daÉ—e tana kallonsu, kafin ta mayar da hankalinta wajen jaririn da yake hannunsa tace "Abu Nisreen wannan jaririn fa ko shi ma tare ka same su" haka yace mata kwantar da hankalinki zan baki labarin komai, idan na samu nutsuwa.

Ni tunda na shigo ma ban ga Nisreen ba, ina ta tafi ta zo na samo mata Æ´ar'uwa murmushi Ummu Nisreen ta yi tace "Wallahi tun yamma ta tafi gidan Iya kuma har yanzu ba ta dawo ba."

Murmushi ya saki yace "Ai kin san Nisreen da Iya idan suka haɗu basa son rabuwa ko kaɗan, yanzu dai ki ɗumama wa waɗannan yaran ruwa su yi wanka, miƙa mata jaririn da yake hannun sa yayi yace "ungo wannan jaririn in anjima kaɗan zai farka insha Allah."

Har ƙasa ta durƙusa ta karɓi jaririn tare da ƙura masa idanu.
Shi kuwa Abu Nisreen, roba ya É—auka ya nufi rijiya domin ya ja ruwa ya watsawa jikinsa ko zai ji É—an daÉ—i a jikinsa.

Shiga da jaririn Ummu Nisreen ta yi cikin ɗaki ta ajiye shi, sannan ta fito ta ɗauki bokiti ta nufi rijiya za ta ɗebo ruwa, da sauri Anas ya tashi ya riƙe bokitin yace "Umma kawo na ɗebo miki ruwan" murmushi ta yi tace "ka bar shi kawai, zan ɗebo kai da gajiya a jikinka."

Ƙin sakin bokitin yayi, a bisa dole ta bar shi ya tafi rijiyar domin ya jawo kata ruwan, a zuciyarta kuwa addu'a take Allah yasa kada Abu Nisreen ya gani tace ita ta saka shi ransa ya ɓaci, ita kuwa ta tsani ta ga ran mijinta ya ɓaci.

Anas yana cikin jan ruwan, sai ga *Nisreen* ta shigo gidan da gudu tana kiran Umma! Umm... Shiru ta yi yayin da ta ga Safna a zaune kuma ta hango Anas yana jan ruwa, a bakin rijiya.

Bata daɗe da shigowa ba, sai ga Iya ta shigo gidan da alama tare suke da Nisreen ɗin. Idanun Iya ne ya kai Safna da take zaune, da Anas da ɗauko bokitin ruwa, dai-dai lokacin kuma Ummu Nisreen ta fito daga cikin ɗaki, hannunta riƙe da ashana.

Tana ganin Iya ta yi sauri ta ɗauko mata kujera ƴar tsugunne, ta kai mata ta zauna sannan ta dubeta tace "Rahila baƙi kuka yi ne?" murmushi ta yi tace wallahi iya Abu Nisreen ne ya zo da su daga wajen farautarsa, ni ma bai yi bayanin inda ya samo su ba.

"Ikon Allah ashe ya dawo?" "E, wallahi bai daÉ—e da dawo wa ba, wanka ma yake yi, shine yace na É—umama musu ruwa su ma suyi wanka, har da wani jariri ma yana É—akina yana barci.

Ita dai Iya riƙe baki kawai ta yi, Nisreen ce ta je wajen Safna ta kama hannunta tace "ke ma ƙawata ce?" gyaɗa mata kai Safna ta yi sannan ta sakar mata murmushi, ita ma Nisreen murmushin ta sakar mata, sannan ta kama hannunta tace "zo mu je ki ga kayana da Abbana ya siyo mini."

Miƙewa Safna ta yi ta bi Nisreen ɗin a baya, Ummu Nisreen da Iya sai dariya suke yi na shirmen da Nisreen take yi yana burge su.

Iya ce tace "Ummu Nisreen ta je ta É—auko mata jaririn ta gan shi, bayan ta tafi É—auko mata shi sai ta mayar da kallonta wajen Safna nan take ta ganta tana tsananin kama da matar da ta taimakawa jiya, kuma ta tuno matar ta bata labarin tana da Æ´aÆ´a yanzu haka bata san inda suke ba.

Dai-dai lokacin Ummu Nisreen ta fito daga É—aki hannunta rungume da jaririn, shi ma Abu Nisreen (Aisar) ya fito daga wankan da ya shiga.

Zuwa yayi gaban mahaifiyar ta shi ya tsugunna har ƙasa ya gaishe ta, kafin yayi wata magana Iya ta riga shi da cewa, Aisaru a ina ka samo waɗannan yaran?

Kafin ya bata amsa ta riga shi da cewa, abinda yasa na tambayeka jiya wata mata tazo garin nan, a firgice tace wai wasu ƴanta'adda ne suka kashe mata miji shine ita ma Allah ya bata nasarar kashe ɗaya a cikinsu ƴanta'addan da suka biyota sai Allah ya jefo ta nan garin, ni ce nan na taimaka mata bayan mun je gidan me gari yace "ta zauna a gidana. Tun jiya ta ƙi cin abinci sai faman kiran sunan ƴaƴanta take yi, kuma ina zaton duk yadda aka yi wannan ƴarta ce domin suna tsananin kama da juna, ta faɗa tana mai nuna Safna.

Anas ne ya zo da gudu ya riƙe ƙafafun Iya yana kuka yake cewa "Don Allah a ina kika ganta ta so mu je ki nuna mana ita Allah yasa Innarmu ce.

Hussaini Yusuf
Comment
Share
Fisabilillahi
[12/9, 4:33 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐*

Labari da Rubutawa
HUSSAINI YUSUF

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.