Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 8 of 25
*Page 15&16*
Aisar ne ya zo ya kama hannun Anas yace "Anas ba mu tabbatar Innarku ba ce, har sai mun je mun gan ta. Wataƙila ma a irin ƴan garinku ne waɗanda su ma suka yo gudun hijirar, yanzu ka je ka yi wanka magriba ta kusa idan mun yi sallah sai mu je mu gano ta. Gaba ɗaya mutanen wajen sai da suka tausaya wa Anas da Safna, musamman ma Iya har hawaye sai da ta zubar ta rinƙa cewa "wallahi yanzu ƙasar nan babu adalci ko kaɗan, haka kawai kana zaune lafiya wasu su zo har cikin gidanka su hallaka ka amma gwamnati ta kasa ɗaukar mataki akai, wannan wanne irin rashin imani da tausayi ne?
Ummu Nisreen ce ta kama hannun Safna ta ja cikin banɗaki, ta yi mata wanka bayan ta gama yi mata ta fito sai Anas ma ya shiga, ba ƙaramin daɗi ya ji a jikinsa ba yayin da yake watsa ruwan zafin a jikinsa, saboda ko'ina na jikin nasa tsami yake yi masa.
Bayan ya fito daga bayin, sai ya É—auki buta ya É—aura alwala domin an fara kiraye-kirayen sallar magriba. Bayan Ummu Nisreen ta gama yiwa Safna wankan, sai ta jawo cikin É—akinta ta shafa mata mai ta yi mata kwalliya, sannan ta É—auko kayan Nisreen ta sanÆ´a mata a jiki, masha Allah shine abinda na faÉ—a yayin da naga Safna ta yi wani irin kyau duk da yarinÆ´a ce, amma idan ka kalleta sai ka sake kallinta saboda Safna ba baya ba ce wajen kyau da cikar halitta irin ta Æ´a mace.
Lokacin da Nisreen ta ga Safna sanƴe da kayanta, kuma ta yi kyau sosai kamar ɗiyar larabawa, sai ta cika da farinciki ta rinƙa jan Safna da zance tun ba ta kula ta har ta zo ta riƙa mayar mata, daɗi yasa Nisreen tace ta bar wa Safna kayanta da aka sa mata.
Bayan Anas ya gama É—aura alwalar, sai suka tafi masallaci tare da Abu Nisreen, ita ma Ummu Nisreen sai ta É—ebowa Iya ruwa tace ta yi alwala ita ma ta É—auki wata butar ta fara alwalar.
Su Nisreen da Safna kuwa sai faman wasansu suke yi, Nisreen sai faman zagaya gidan take yi ita da Safna tana nuna mata abubuwa.
Allah -Allah Anas yake yi a idar da sallah su je su gano matar da Iya ta faÉ—a, idan kuwa Innarsu ce bata mutu ba babu wanda zai kai su farinciki da ganinta.
Bayan an idar da sallar an shafa addu'a sai Abu Nisreen ya kamo hannun Anas suka fito daga masallacin, yayin da suka shigo cikin gidan su Iya Ummu Nisreen sun idar da ta su sallar, gaba É—ayansu suka É—unguma suka tafi gidan Iya, har da su Nisreen da Safna.
Sosai Safna take jinta a cikin farinciki ta samu ƙawa me mutunci, a cewarta wato *Nisreen* a hanƴa ma hannunsu yana sarƙe da na juna, cike da nishaɗi da walwala suke tafiya, duk inda Nisreen ta ga ƙawayenta sai ta kira sunansu ta nuna musu Safna tace kun ga sabuwar ƙawata haka ko wanda ta sani idan ta gan shi sai ta nuna masa Safna.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan Iya, take kuwa Anas ya ji gabansa ya tsananta faɗuwa sosai fargaban kada ya ga wata ba Innarsu ba yake yi cikin ran shi. Yayin da suka shiga cikin gidan gaba ɗayansu, Inna tana cikin banɗaki daga ciki take jiyo muryar Safna da Nisreen, domin ta daɗe da sanin Nisreen don a gidan take yini kullum.
Murje idanuwanta ta yi don ta tabbatar ba'a mafarki take jin muryar Safnar ta ba, sauri ta yi ta kammala abinda ya kaita banɗakin sannan ta nufo ƙofar fitowa. Idanunta sai ƙaiƙayi suke, sun matsu su yi tozali da ƴaƴanta abin alfaharinta, zuciyarta tana ta muradin sake ganinsu, yayin da ƙafafunta suka ƙagu a taka su domin su ga farincikin rayuwarta.
Lokacin da ta gama fitowa daga cikin bayin, ta hango su a zaune a ƙofar ɗaki kan tabarmar da Iya ta shimfiɗa musu, tana gama fitowa karaf! idanun Safna suka sauka a kanta ba ta tsaya wani jinkiri ba ta tafi da gudu tana kiran Innaaaa! da sauri Anas ya ɗago da kansa da yake a sunkuye tun shigowarsu cikin gidan.
Innarsu ya gani, ya murza idanunsa don ya tabbatar ba'a mafarki ya ganta ba, ai bai jira wani abu shi ma ya nufe ta da gudu ya rungume ta, gaba É—ayansu suka fashe da kukan farinciki. Anas yace "ashe Inna ba ki mutu ba? zamu sake ganinki, Safna ma tace "Inna me yasa kika ce mu gudu mu bar ki, kuma ina Baffamu yake a can kika baro shi?"
Tambayar Safna ta sake karyarwa Inna da Anas zuciya, suka sake fashewa da kuka, mai tsuma zuciya.
Su Abu Nisreen da Iya da Ummu Nisreen, sai faman zubar da hawaye suke yi, na tausayin su Inna da Æ´aÆ´anta, Allah sarki! Yanzu da Allah bai sake haÉ—a su, ko yaya za su yi da rayuwarsu? don tsakanin É—a da mahaifi sai Allah.
Har *Abu Nisreen* ya yunƙura zai je ya rarrashe su, da sauri Iya ta hana shi tace me yasa zaka je ka hana su kukan farincikin sake ganin juna da suka yi?
Dakatawa yayi ya zauna ya ƙurawa su Inna idanu, cike da tausayinsu. Dai-dai lokacin jaririn da su Safna suka tsinta ya farka daga barcin da ya shafe awanni yana yi, kukan shi ne ya dakatar da su Inna, da sauri suka ɗago kawunan su, suka kalli inda suka jiyo kukan jaririn da yake goye a bayan Ummu Nisreen.
Da sauri Iya ta karɓe shi daga hannun Ummu Nisreen, ta je ta ɗebo ruwa a wani ɗan ƙaramin kofi ta bai wa jaririn, kowa a wajen sai da yayi mamakin ruwan da jaririn ya sha.
Shigewa ɗaki Ummu Nisreen ta yi domin ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa musu, fitowa ta yi daga ɗakin Iya hannunta riƙe da wata ƙatuwar tabarma sabuwa dal.
Shimfiɗawa ta yi a ƙofar ɗakin Iya, Abu Nisreen yace "kowa ya zo ya zauna, gaba ɗayan su suka zo suka zauna akan tabarmar har Inna da su Anas da Safna sun zo sun zazzauna akan tabarmar.
Nisreen kuwa tun da ta ga ƙawarta Safna tana kuka, sai jikinta yayi sanƴi ta samu waje ɗaya ta zauna ta yi shiru tare da ƙurawa su Safnar idanu.
Bayan kowa ya zauna a kan tabarmar sai Abu Nisreen yayi gyaran murya, yayi wa Allah godiya tare da addu'a ga fiyyayen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) sannan suka yi addu'a suka shafa.
Anas ne ya fara bayar da labarin irin wahalar da suka sha, shi da Safna har tsintar jaririn da suka yi, da yanda Safna ta kafe akan dole sai sun É—auko, da lokacin da zaki ya ritsa su a dokar daji zai hallaka su, Allah ya kawo Abu Nisreen ya taimaka musu.
Sosai kowa ya ji tausayin su Anas, Iya har da zubar da ƙwalla sai da ta yi, haka Ummu Nisreen ma sai da ta zubar da hawaye na tausayin su Anas. Inna ma nan take ta shiga bayar da
nata labarin da irin wahalar da ta sha bayan ta cewa su Anas su tafi, su rabu da ita, bayan kowannen su ya gama alhinin da zai yi sai Abu Nisreen yace "ita Ummu Nisreen ta ruƙe jaririn ta raine shi tunda Allah bai sake bata haihuwa ba tun haihuwar Nisreen.
Ita kuma Inna ta zauna a gidan Iya sai a bata Safna da Nisreen, Nisreen ta zauna hannun Iya ita kuma Safna ta zauna a hannun Inna yayin da shi kuma Anas zai zauna a hannun Abu Nisreen, sai su rinƙa zuwa farauta da neman kuɗi tare. Nan take kuwa kowa ya amince da wannan kyakkyawar shawarar da Abu Nisreen ya kawo, miƙewa tsaye Abu Nisreen yayi yace "Ummu Nisreen ta tashi su tafi, domin an kusa yin kiran Isha'i, su kuma su Nisreen da Safna su zauna anan su kwana da safe za'a kawo musu kayan sakawar su."
Daga ƙofar gida suka ji ana bugun gidan kamar za'a karya ƙyauren da ke maƙale a ƙofar gidan da sauri Abu Nisreen ya fice domin ya gano lafiya ake buga masa gida haka.
To be continue..........
Comment and shareðŸ™
Hussaini YusufâœðŸ»
[12/9, 4:33 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ðŸ«ðŸ« ANAS MALEEKðŸ«ðŸ«*
Labari/Rubutawa
HUSSAINI YUSUF
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.