Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 25

*Page 41/42*

Alhaji Abubakar ya sunkuya ya ɗauke shi, ya sumbace shi a goshi, harararsa Amina ta yi ta ce "Wato ta ɗanka ka ke yi ko kula ni" da sauri ya juyo ya kalleta ya sakar mata wani lallausan murmushi ya ce "Kiyi haƙuri matata wallahi zumuɗine ya ke ɗibana kiyi haƙuri kin ji" ita ma yayi mata kiss a goshi, sannan ya samu waje gefen gadon da take zaune ya zauna. Ƙura mata ido yayi ya daɗe yana kallonta kafin ya ce "Yanzu dai da fatan babu inda yake yi ciwo" gigiza masa kai ta yi ta wani ɗan yatsina fuska ta ce "Ni babu inda yake yi min ciwo, na gaji ma da zaman asibitin nan ka je ka kira likita ya bani sallama." Murmushi Alhaji Abubakar yayi kafin ya ce "Haba ke kuwa Ƴar Aljanna me kike faɗa haka? ki bari ka sake warwarewa mana sai mu karɓi sallamar, kawar da kanta gefe ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Ni dai ka je ka kirawo min likita ya sallame ni, don na tsani zaman asibiti gaba ɗaya wallahi." Ba yadda ya iya tashi yayi ya nufi office ɗin likitan, a zaune ya same shi yana duba files, sallama yayi masa kafin ya samu wurin zama, bayan ya zauna ya dubi likita ya ce "Likita Madam ce wallahi ta damu a bata sallama wai ita ta matsu ta tafi gida" murmushi Likita yayi ya ce "Ko kwana fa bata yi ba ta ke cewa haka" ƴar dariya Alhaji abubakar yayi ya ce "Likita ka san halin Madam ɗin da rigima" numfasawa Likita yayi ya ce "Ok to bari na je ba duba ta idan babu matsala sai na baku sallamar. A zaune suka zo suka sameta riƙe da jaririnta yana kan cinƴarta tana ta sakar masa murmushi, zuwa Likita yayi ya ce "Haba Madam ki bari ki ƙara warwarewa mana sai na baku sallamar sannan kin gama warwarewa gaba ɗaya. Ɗan ɓata fuska ta yi ta kalli Alhaji Abubakar ta kawar da kai, da sauri ya kalli Likita ya ce "Kawai ka ba mu sallamar tun da ta matsa, sai ta sake warwarewa a gida" sai da Likita ya ƙara duba ta sosai, sannan ya rubuta mata takardar sallamar, tare da wasu ƴan magunguna.

Bayan sun dawo gida ƴan'uwa da abokan arziƙi suka yi ta zuwa suna yi musu barka, kowa idan ya zo sai ya yaba da kyawun jaririn. Abokan Alhaji Abubakar suka yi ta kawo masa kyaututtuka masu yawan gaske, Amina ma ta samu kyaututtuka daga wajen matan abokan mijinta, da ƙawayenta da kuma danginta. Da satin haihuwar ya zagayo aka raɗa wa yaron suna KAMALUDDEN amma ana kiransa da AMMAR saboda sunan mahaifin Amina aka saka masa. An sha shagali sosai har walima aka yi, an ci an sha sosai abokan Alhaji sun zo sun taya shi murnar samun ɗa namiji da yayi.
Bayan suna sosai suka mayar da hankalinsu wajen kula da tilon ɗansu na fari, lokacin kuma arziƙin Alhaji Abubakar ya ƙara bunƙasa, har company ya gina sosai ga manyan shaguna a cikin kasuwanin cikin Kano. Lokacin da Ammar ya cika shekara biyu da rabi, har an saka shi a makaranta irin ta ƙananun yaran nan, sosai yake samun kulawa daga hannun iyayensa ko kaɗan ba sa barin shi yayi kukan rashin wani abu da suka fi ƙarfinsa.

Wata rana da safiyar Juma'a, Amina ta tashi da wani irin matsanancin ciwon ciki, Alhaji Abubakar bai jira wani abu ba, ya ɗauke ta yayi asibiti da ita, anan Likita ya shaida masa tana ɗauke da wani sabon juna biyun, sosai Alhaji ya rinƙa murna kamar wannan ce haihuwarsa ta farko. Sosai Amina ta rinƙa samun kulawa daga wajen Alhaji Abubakar, duk da farko Amina ta nuna ƙin amincewarta akan cikin domin ba ta daɗe da yaye Ammar ba ta kuma samun wani juna biyun, ta nunawa Alhaji a zubar da cikin, fir ya ƙi amincewa kuma ya ce "Indai ta kuskura ta zubar da cikin nan sai ya ɗauki mummunan mataki akanta" ba yadda ta iya haka ta haƙura ta cigaba da rainon cikin, har ya cika wata tara. A safiyar wata Juma'a ne Amina ta tashi da naƙuda, babu ɓata lokaci aka kaita asibiti, likitoci ne suka taru akanta domin bata taimakon gaggawa, bayan an ɗauki tsawon mintina. Sai ga ɗaya daga cikin likitocin ya fito yana share zufa, tamkar wanda ya shafe awanni a cikin ɗaki mai zafin gaske, kallon Alhaji Abubakar yayi ya ga yadda duk ya bi ya fita daga hayyacinsa, kamar wanda aka yiwa alƙawarin barin duniya.
Shi ma Alhaji Abubakar idanu ya ƙurawa likita, bakinsa yana ta motsi alamun yana da magana a baki amma ya kasa furta ta.

Alama likita yayi masa da ya biyo shi office, bai tsaya wani ɓata lokaci ba, ya tashi da ɗan sassarfarsa ya bi bayan likitan, bayan likita ya zauna shi ma Alhaji Abubakar ɗin ya nemi waje ya zauna yana mai fuskantar likita tamkar ɗalibi a gaban malami. Wani gwauron numfashi likita ya ajiye, tamkar wanda ya daɗe bai shaƙi iska ba, ko kuma wanda aka shaƙewa wuya ya ɗan daɗe bai shaƙi iska ba. Cike da ƙwarin gwiwa ya shiga yi wa Alhaji bayani "Maganar gaskiya Alhaji matarka ba za ta iya haihuwa da kanta ba, har sai an yi mata aiki" wani matsiyacin kallo Alhaji ya jefi likita da shi, ya ƙura masa manyan idanunsa da suka firfito waje tamkar na mujiya. "Yanzu likita kana nufin sai kun yiwa Aminata ƴar Aljanna aiki sannan za ta iya haihuwa da kanta? ƙwarai da gaske kuwa Alhaji domin mun yi iyakar bakin ƙoƙarinmu amma ta kasa haihuwa." Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar ya ajiye, shiru office ɗin ya ɗauka na mintuna kamar maye ya ci shirwa, likita ne yayi ƙarfin halin ce wa "Alhaji lokaci fa yana tafiya amincewarka kawai muke buƙata, domin maganar gaskiya matarka tana mawuyacin hali" da sauri Alhaji Abubakar ya dubi likita ya ce "Na amince likita indai za ta haihu lafiya" wata farar takarda likita ya ajiye masa ya ce ya saka hannu, ba tare da wani ɓata lokaci ba Alhaji ABUBAKAR ya sanya hannu a farar takardar.

Nan take kuwa aka shiga da Amina cikin ɗakin tiyata, tun da aka shiga da ita gaban Alhaji ya rinƙa faɗuwa gani yake yi kamar baza'a fito da ita da rai ba, zuciyarsa raya masa take kamar ya rabu da matarsa, rabuwa ta har abada. Shaiɗan sai faman wasa yake yi masa da zuciyarsa wajen saƙa masa abubuwa marasa daɗi game da aikin da ake yi wa matarsa. Bayan kamar awanni biyu, sai ga likita ya fito daga ɗakin tiyatar yana ta faman share zufa, bai daɗe da fitowa ba sai ga nurses sun fito da Amina akan gado tamkar gawa cikin hanzari suka tura gadon zuwa wani ɗaki. Da gudu Alhaji Abubakar ya yunƙura zai bi bayansu, riƙe hannunshi likita yayi ya ce "Haba Alhaji ka tsaya na yi maka bayani mana za ka tafi ka barni a tsaye" sosa kai ya shiga yi tamkar wanda ba shi da gaskiya, muryar likita ce ta doki dodon kunnensa yana ce wa "Alhaji ka yi haƙuri ɗan bai zo da rai ba, sannan ita ma Aminar tana matuƙar shan wahala" yunƙura Alhaji Abubakar yayi ya nufi ɗakin da aka kwantar da Aminar, da sauri likita ya sake dakatar da shi a karo na biyu, ya ce "Haba Alhaji ka tsaya mana na je na sake dubata sannan sai na ba ka izinin ganinta. Ba yadda ya iya juyo wa yayi ya nemi kujera anan reception ya zauna ya zuba tagumi, gaba ɗaya kewar matarsa ta dame shi, so yake ya ganta ko sau ɗaya ne amma likita ya hana shi, shi da matarsa. Yana sunkuye da kansa tunani kala-kala sun cika masa zuciya, ya rasa yadda zai yi ya kasa controlling ɗin kansa akan abun da yake ji game da Amina kewarta ta dame shi sosai, yana cikin tunanin shi ya ɗago kansa karaf! idanunsa suka sauka akan ƴar aikinsu Lami tana ɗauke da Ammar a hannunta, ɗayan hannun kuma ɗauke da kula ta abinci......✍️

To be continue.....📝📝📝

*Hussaini Yusuf✍️*
[12/9, 4:37 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *ANAS MALEEK*

*NA*
*HUSSAINI YUSUF*

*______________________________*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu Ƴancinmu*
*______________________________*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.