Trending Hausa Novels

Anas Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Anas_Maleek_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 5 of 25

*____________________*
Page 9&10

Gani suka yi wani ƙaton mutum, ya fito daga cikin lungun, bayansa goye da kwari da baka. Tafiya yake amma ƙasar wajen, sai amsa amon takunsa take, yadda kasan wani basarake haka yake tafiya.

Bai tsaya a ko'ina ba sai, akan mushen zakin nan, hannu yasa ya finciko mashinsa daga cikin zakin, sannan ya juyo ya nufo inda su Anas suke a tsaye.

Yana zuwa wajensu, kai tsaye ya nufi inda jaririn nan yake kuka, sunkuyawa yayi ya ɗauke shi, yana rarrashinsa. Sannan ya kalli Anas yace "menene ya kawo ku wannan baƙin dajin?"

Shiru suka yi suna kallonsa, babu wanda ya iya buɗe baki a cikinsu ya bashi amsa, har lokacin jaririn yana hannunsa yana ta aikin rarrashinsa amma ya ƙi yin shiru.

Tafiya ya fara yi yace "ku biyo ni a baya" cikin hanzari kuwa suka rufa masa baya, tuni Safna ta manta da ƙishirwa da yunwar da take ji yayin da ta ga zakin nan, sai yanzu ne ta ji ta dawo jin matsananciyar ƙishirwa.

Tafiya yake a hankali su ma sai faman bin sa suke yi, a baya su faɗa wannan surƙuƙi su fita su faɗa wancan. Da haka har suka ƙaraso, wajen wata bukka mai kyawun gaske.

Yayin da suka iso ƙofar bukkar sai ya dakatar da su, ya shiga ciki shi kaɗai, ba jimawa sai ga shi ya fito da tabarmar kaba (karauni) ya shimfiɗa musu yace su zauna.

Bayan sun zazzauna sai ya sake shiga cikin bukkar, sai ga shi ya fito da tulun ruwa me sanyin gaske a hannunsa, tsiyaya wa yayi ya bai wa jaririn Allah sarki bawan Allah sai da ya sha ruwan me yawan gaske, nan take barci yayi awon gaba da shi.

Sake tsiyayawa yayi ya miƙa wa Safna, da sauri ta karɓa ta rinƙa sha, har sai da cikinta ya kusa ƙullewa sannan ta miƙa masa ƙoƙon, ya sake tsiyayo ruwan ya miƙa wa Anas shi ma ya sha da yawa yayi gyatsa ya godewa Ubangiji.

Gani yayi duk hankalinsu ya dawo jikinsu, duban Anas yayi yace "menene ya kawo ku wannan dajin, kuna yara da ki?" Hawaye Anas ya fara zubarwa ita ma Safna ta shiga share hawayen.

Labarin irin ta'addancin da aka je ƙauyensu aka yi musu suka ba shi, har saka su a rumbu da Baffa yayi domin su tsira da rayuwarsu sai da suka ba shi.Da irin wahalar da suka sha a hanƴa kafin su iso nan duk sai da suka faɗa masa, ba su ɓoye masa kome ba har zuwa lokacin da wannan zakin ya ritsa su sai da suka faɗa masa.

"To a ina kuka samu wannan jaririn?" Safna ce ta faÉ—a masa yadda aka yi suka tsince shi yana ta kuka kuma babu uwarsa a kusa da alamu ita ma an kashe ta.

Hawaye maharbin ya shiga zubar wa, haƙiƙa ya tausayawa su Anas ba kaɗan ba, nan shi ma ya shiga ba su na shi labarin kamar haka.

Sunana Aisar ni haifaffen garin Katsina ne, na dawo nan yankin Taraba ne sakamakon Æ´anta'addan da suka addabi yankinmu.
Lokacin ina yaro mu na zaune, ni da iyayena mu ka ji ƙarar harbin bindigu, nan take mahaifina ya ɗauke ni, a kafaɗarsa ya ja hannun mahaifiyata mu ka fice daga ƙauyen namu ta ɓoyayyiyar hanƴa, ba tare da ɗaya daga cikin ƴanta'addan ya gan mu ba.
Sai da muka share awa uku muna tafiya, sannan muka iso wata mararrabar hanÆ´a. Sauke ni mahaifina yayi daga kafaÉ—arsa, yace mahaifiyata ta É—auke ni.
Sunkuyawa ta yi ta ɗauke ni, cikin nutsuwa mahaifina ya dubi mahaifiyata ya nuna mata wata hanƴa da ta yi yamma. Yace "ta bi hanƴar akwai garuruwa da ƙauyuka sosai akan hanƴar" duk garin da ta je kada ta tsaya, da ta samu ruwa da abinci ta sha to ta ƙara gaba, domin a kowanne lokaci ƴanta'addan za su iya riskar ɗaya daga cikin garuruwan.

Sannan yace wa mahaifiyata ta bani tarbiyya dai-dai gwargwado. Sannan ya sake cewa ta saka ni a makarantar boko da islamiyya, kada ta barni na zama mutumin banza.
Ya ciro wani zobe daga hannunsa, ya miƙawa mahaifiyata yace "idan na girma ta ba ni shi a matsayin gadon da mahaifina ya bar mini."
Juyawa yayi zai tafi, mahaifiyata ta yi wuf, ta riƙe rigarsa ta saki wani kuka mai tsuma zuciya tace "Abban Aisar don Allah kar ka tafi ka bar ni!"
Hawaye Abbana ya goge, sannan ya dubi mahaifiyata yace "Binta dole ne na koma wajen mutanen can, domin na É—auki fansar ran iyayena" kuma na kare rayukan mutanen garinmu.
Bai tsaya sauraron abinda Ummata za ta faÉ—a ba, ya juya ya fara tafiya domin ya koma garin ya tari Æ´anta'addan.
Kama hannuna Ummata ta yi, muka fara tafiya, sai faman kuka Ummata take yi tana waigen Abbana.
Har suka daina hango juna, Ummata ba ta daina hangen Abbana ba.
Da kyar Ummata take iya ɗaga ƙafarta, tana tafiya ita kaɗai cikin yashi.
Sai da muka shafe sama da awa uku muna tafiya, sannan Ummata ta tsaya a gindin wata bishiya, ta sauke ni ta ba ni nono nan take kuwa na riƙe na fara sha.
Barci mai nauyi ne ya ɗauke ni, Ummata ta shimfiɗa mayafinta a ƙasa ta kwantar da ni a kai.
Ita ma ta kishingiɗa, take kuwa barci ɓarawo yayi gaba da ita, mun daɗe a gindin bishiyar muna barci, sai wajen doshin faɗuwar rana Ummata ta farka daga barcin, bakinta ɗauke da salati duban ta takai inda nake kwance, gani na tayi har lokacin ban farka ba, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu abinda ya same ni.
Ɗauka ta tayi ta goya ni a bayanta, sannan ta cigaba da tafiya, cikinta ban da ciwo babu abinda yake yi, ƙirjinta yana yi mata zafi, sakamakon tana ciwon ulcer kuma ga shi bata samu abinci ta ci ba tun safe.
Yayin da Ummata ta ga duhu yana ƙoƙarin mamaye sauran hasken ranar da ya rage, sai ta samu waje a gefen hanƴa ta zauna ba tare da ta kwance ni daga bayanta ba.
Jim kaÉ—an da zamanta, sai ta fara jiyo wani irin gurnani, marar daÉ—in sauraro, da sauri ta tashi ta shige cikin wani kogon dutse da yake gefen hanÆ´ar.

Hussaini Yusuf✍️
Comment and share
[12/9, 4:33 PM] ~HUSSAIN YUSUF~: *🫐🫐 ANAS MALEEK🫐🫐*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Labari/Rubutawa
HUSSAINI YUSUF

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.