Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 28

Page 19&20

"Yace taɓɗi ni ta manta lalle zataci ubanta, ai kuwa da gudu Fateemah taje taɗau malullin ɗakin tazo ta baɗeshi"
Tana buÉ—ewa taji mari tass, dan ubanki ni kika manta! Gidan ubanki ne? Dazaki rufeni kice kin manta yau sena nuna miki kuskurenki!

Ya rike hanunta da karfi yana janta Yabi ta kofan baya da ita ya buÉ—e motarshi yasata aciki, yafita da gudu acikin gidan,

"Yana gudu tanata bashi hakuri shi kuma hakurin datake bashi yana kara bashi haushi"

Dahaka har ya iso wani gida,
Tangameme me Ƙaton get yayi parking,
Yafita agidan da kanshi ya buÉ—e get É—in yashiga cikin gidan yace mata fita!
Tafara cewa dan Allah kayi hakuri wallahi mantawa nayi.

Yau zakisan kin manta ni!
Haka ya É—auke ta a motan Ya fita da ita

Yana É—aukan ta be ajeta ako ina ba se a wani bedroom wanda ya kayatu da abubuwan kyale kyale,
Haka tana gani yafara yayyaga kayan jikinta tana bashi hakuri amma ina.

Haka Ahmad yayiwa Fateemah fyaÉ—e (eh mana ai wannan fyaÉ—e ne),
Haka Ahmad ya É—auki Fateemah A sume yasata a mota ya kama hanya,
Saida yayi tafiya me nisa kadin ya tsaya ya buÉ—e motar yana daga ciki ya cillar da ita waje yaja motarsa ya tafi.
****************

"Bayan Ahmad yakoma gidane ya fara wani tinani me ze faÉ—awa Daddy idan ya tambiyeshi ina Fateemah, kai anya bazan koma in É—aukota ba! Kodai nabarta ne! *(Nace duk kai kaÉ—ai)*"

Haka yayi wanka ya kwanta yayi baccinshi,
Washe gari da safe Fareedah tazo É—akin dan takirawa Mommy Fateemah,
Tana zuwa tayi knocking,
yace waye? tace Fareedah ce yace mene ne? Tace mommy ce take kiran Fateemah!

Dumm yaji zuciyarshi ta buga,
Kije ina zuwa tace toh,

Yana zuwa É—akin mommy yace "inakwana mommy"
Tace lafiya ina Fateemahn?
Yace Fareedah fita ki bamu waje,
Fareedah tafita yasamu bakin gado ya zauna,
Yace Mommy wato yarinyannan ta rainani ne jiy ta kulleni a É—aki har dare wai ta manta ni,
Shine me? Inji mommy,
Yace shine itama nakaita inda za'a manta da ita!
kana hauka ne ko ka fara shaye shaye ne?
Yayi shiru,
Ina ka kaita?
Yace bayan gari,
Ji kake tass tass tass Mommy ta wanke shi da mari har sau uku,
kayi hauka ko?
Yayi shiru ba magana nake maka ba?
Shiru har yanzu,
Tashi ya tashi Tace muje,
Yashiga gaba suka fita! Suna fita yaga Fareedah a kwance lub abakin kofa kamar ba Rai,
Da gudu Mommy taje wajenta tana kiran sunanta amma shiru, mommy ta kwala ihu tana kiran sunanta, shi kuma Ahmad ya rikece yarasa me zeyi.

"Suna cikin haka Daddy ya sauko da sauri yana tambayan meyake faruwa? Mommy tace mishi Fareedah ce ta suma! Yace wa Ahmad kawo ruwa. Ahmad yatashi da gudu ya É—ebo ruwa aka Zuba mata a hankali tafara buÉ—e idonta tace ina Fateemah? Da alama taji duk maganganunsu, Ahmad yayi shiru Daddy yace wace Fateemah? Mommy tace Fateemah ce Ahmad yaje ya yadda ita!"

Daddy yace what are you saying Mariya? Mom tace katambiyeshi kaji mana wai ta kulleshi a É—aki shine yarama,
Daddy ya É—ago idonshi yana kallon Ahmad
Yace me nakeji,

Yayi shiru, Daddy yace tashi muje suka É—unguma duka suka shiga mota.

Ahmad yajasu suka tafi sunata tafiya sukaga wajen yayi nisa mommy tana ta Addu'a a ranta,

Har suka iso bayan gari kafin yatsaya, Daddy yace ananne?
Ahmad yace eh ok ina take yayi shiru,
Mommy kuwa tazuba ma wani dutse ido Taga kamar jini ne akai, tacewa Alhj kalli can, Daddy yana kallo yaga jini ne awajen!
Suna zuwa sukaga jini dayawa akan dutsen harya fara bushewa,
Daddy yace Wannan jininfa? Ahmad yayi shiru Daddy have ba tambayanka Nake ba?
Daddy Nina ban Sani ba!
Tass Daddy ya wankeshi da Mari.

Ina kakai 'yar mutane? Inji Mommy yayi shiru...
Ba tambayanka ake ba?

"Shikamma yarasa ya zeyi idan yayi magana su mareshi yayi shiru suyi ta tambayanshi ya rasa ya zaiyi"

"Suna cikin dubawa sukaga wani mutum yana zaune dagacan gefe, Daddy yaƙarasa wajen mutumin yace mishi, bawan Allah bakaga wata yarinya Acan Akwance ba?
Tsohon yacewa Daddy, eh ai É—azu wasu mutane sunzo sun É—auki wani gawa acan kuma a yadda nagani gawan kamar mace ne........."

Ai kafin yaƙarasa Daddy yafaɗi awajen, da gudu suka ƙaraso wajen suna tambayan tsohon meya faru? Yayi musu bayanin komai, kafin yakarasa zancanshi ai Fareedah ma tayi ƙasa, mutumin yarasa meyake faruwa. Mommy tadinga zabga ihu shikuma Ahmad atake jikinshi yafara rawa da ƙyar suka ɗaukesu zuwa Asibiti
**************

Tun daga wannan rana Alh Kabeer yazama bashi da lafiya harya kasance jikin yayi tsanani hawan jini yake daminshi,
Ɓangaren Fareedah ma bawani lafiyane da ita ba tazama shiru bata da yawan magana. Shikuma Ahmad yarasa meyake mishi daɗi Abu kamar wasa gashi yazama gaske, shima yazama shiru shiru dama gashi miskili.

Alh Kabeer jiki yayi tsanani yana jinya sosai, yau kam jikinma yafi na kullum an kaishi Asibiti rai yayi halinshi saide muce Allah yagafarta mishi da duk musulman da suka mutu "Ameen"

✍️🗒️ *jiddah S Mapi*
[6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_Story/written by_
Jiddah S MAPI

_dedicated to my daughter Afrah_

_✅ote me on wattpad Jiddahpretty_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.