Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 28

Page 15&16

Da kyar Fareedah ta janye Fateemah zuwa gefen hanya ta kwantar da ita tace "ki zauna anan bara naje na kama mana Napep"

A haka ta kama musu Napep ta rike Fateemah suka shiga se gida.

Shi kuma Ahmad yana jan motarsa ya wuce carwash yace a wanke mishi ita,

Alh Kabeer kuwa da mariya suna zuwa gidan marayu yacewa mama yanason magana da ita,
Tace "ok ba komai ina jinka Alh"

Yace dama so nake na É—auke Fateemah na É—an wani lokaci idan ba matsala,
Mama tace ba komai Alh. Ay duk an zama É—aya,
Da haka suka tafi gida.
***************
Shakuwa me tsanani ta shiga tsakanin Fareedah da Fateemah,
Dan Fareedah sosai takeson Fateemah har cikin Ranta komai za'a siya mata zatace sai an siyawa Fateemah.

Shi kuma Ahmad a duniya babu abinda yatsani gani kamar Fateemah, kwata kwata Allah be haÉ—a jininsu da ita ba,
Ko abinci Fateemah ta dafa baya ci idan har ya san ita tadafa.

Yauma kamar kullum Fateemah ce take goge goge a falo,
tana kan goge TV ne taji ance mata "ke baki da hankali ne ko kin taɓa ganin inda ake goge TV da tsumma? Koda shike ba laifinki bane laifin iyayenki ne dasuka haifeki a titi, daga baya suka yadda ki"
Nasan da agaban iyayen ki kike, dakin iya goge TV. Wawiyar banza.

Tunda Fateemah take a rayuwarta ba'a taɓa faɗa mata maganan daya ɓata mata rai irin ta yau ba,
Ahmad ne farko yafara kiranta da shegiya.

A hankali ta É—ago kanta tace "kayi hakuri zan gyara insha Allah "
Ai kuwa yaja tsaki ya fita a É—akin yanaji kamar ya shaketa ta mutu kawai.

Wato yarinyannan duk abunda za'ayi mata bazatayi kuka ba, saide tayi tabada hakuri kamar marokiya, sai nayi maganinta ay.

Ita kuma Fateemah yana fita tasa kuka me cin rai,
Tana cikin kuka ne taji muryan Fareedah tana, Besty ina kike?

Ta share hawayenta tace "gani nan"

Fareedah ta rungumeta tace "meya sameki naga kamar kinyi kuka? tace "Aa babu komai kaina ke ciwo"
Ayya sorry kinsha magani?
Eh nasha,
Ok muje É—aki to ki kwanta.

Da daren ranan Fateemah takasa bacci, data rufe ido sai tana tuna maganganun Ahmad na É—azu.
_ba laifinki bane_
_Laifin iyayenki ne_
_Dasuka haifeki a titi_

Wato ni shegiyace? A titi aka haifeni? To ina iyayena suke!? Meyasa suka yadda ni?
Shine tambayoyin data kasa amsawa kanta,
Data kara tunawa seta fashe da kuka,
Jikinta yafara zafi, tana kokarin ta tsaida kukan amma ta kasa. Da haka har tafara tari, jikinta yafara rawa taja bargo ta lulluɓa jikinta amma har yanzu tana jin sanyi. Tana cikin wannan halinne Fareedah ta tashi zatayi fitsari,

Taga Fateemah acikin bargo jikinta yana rawa gashi fuskanta yayi ja,
A razane ta iso wajenta tana tambayanta meya faru

Fateemah ba bakin magana se ido kawai,
Ta fita da gudu taje É—akin mommy ta kirata,
A tare sukazo da mommy,
Mommy tana ganin halin da Fateemah take ciki tace akira mata Alhaji,
Ai kuwa Alh Kabeer yana zuwa yace aje akira Ahmad yazo su tafi Asibiti.

Fareedah ce taje kiranshi tana zuwa tayi knocking yace "yes waye? "
Tace Yaya Fareedah ce,
Yace me kikeso?
Tace "Daddy ne yace nakiraka"
Daddy kuma? Meya faru?
Nima ban sani ba!

Ok ina zuwa,
Ahmad yana zuwa Daddy yace "oya É—auke ta da wuri mu tafi Asibiti kar dare yayi sosai.

😳Daddy wani Asibiti?
Dama wani Asibiti muke zuwa? Inji Daddy

Daddy Ai yanzu dare yayi abari sai gobe mana da safe....
Kai Ahmad baka da hankali ne? Ko baka ganin halin da take ciki? Ko da Fareedah ce zakace abari sai gobe?

Yayi shiru dan besan me zecewa Daddy ba ganin yahau 90,

A haka badan yaso ba ya É—auketa yakaita mota,
Ji yake kamar ya shaketa tamutu ko ze huta

✍️🗒️ *jiddah S mapi*
[6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_story/written by_
Jiddah S mapi

_dedicated to my lovly sister_
@walidation

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.