Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 20 of 28

Page 39&40

"Mommy takai minti talatin Asume, kafin Beebah tashigo falon tana sallama taga Mommy Akwance ƙasa ba Alamun numfashi, Ta tsala ihu tana kiran Bintu, dagudu Bintu tashigo ɗakin ganin Mommy asume tayi gudu taje frij ta ɗauko ruwa suka shafa mata afuska"

A hankali tasauke Ajiyar zuciya, tafara buÉ—e idanunta.

Ganin Beebah da Bintu tsaye akanta cirko cirko, tafara Addu'an Allah yasa basuga hotonba.

Tajuya tana dube duben inda hoton yake Amma bata ganiba, ta rikice tana neman hoton can taga hoton Agaban Bintu daidai ƙafarta, Bintu kuma bata lura da hoton ba burinsu suji me ya sumar da mom?

Mommy dataga Alaman basuga hoton ba tayi sauri ta kwanta rub da ciki akan hoton tana cewa wayyo cikina! Tafara ja da cikinta har ta iso wajen gado tatura hoton babu wanda yagani.

Bintu da Beebah suka rinƙayi mata sannu harta samu tayi bacci, Beebah ce takira Habeeb tace mishi "yaya mommy ba lafiya harta suma"

Habeeb yace meya sameta? Tace babu komai muma dai haka muka shigo muka ganta a sume, yace "ok" ina izuwa.

Habeeb yana zuwa yaga mommy akwance tana bacci yafara tambayan Bintu meya sameta?
Bintu cikin sanyin murya tace nima dai haka nazo naganta a sume! Amma naji tana cewa cikinta ne yake ciwo!
Yayi shiru yana kallonta yace "ok".

Habeeb yazauna awajen mommy harta tashi daga bacci, tana tashi tacewa "yaushe kadawo?"
Yace mommy ay tin ÆŠazu nadawo tace ok cikin sanyin murya tace inason kaje kasiyaminmagani yanzu yanzu basai kawani canza kaya ba!
Yace tom mommy, yatashi yafita mommy ta tsunkuya taɗau hoton a ƙarƙashin gado Kana tasa a frame ɗin ta ɓoye a rigarta tabi bayanshi.

Tana fita taganshi yana ƙoƙarin buɗe ɗakinshi, da sauri ta ƙarasa wajenshi tace kai Habeeb mezakayi kuma a ɗaki bayan kasan banida lafiya harda suma? Amaimakon kayi sauri kasiyomin magani?
Habeeb yayi mamakin yanda mommy takeson korashi amma be kawo komai aranshi ba!.

Yace mata mommy kuÉ—i zan É—auka sabida kuÉ—in hanuna yakare, Mommy tace kaje É—akina kacire acikin jaka, yace tom Mommy.

Saida Habeeb yabar gidan kafin Mommy tashiga ɗakin ta ajiye hoton yanda tagani ta gyara wajen kamar ba'a taɓa komai ba.
Harda fesa turare.

*_Ahmad_*
Tin bayan tafiyan Habeeb yashiga damuwa kamar da dama acikin abokananshi daga Habeeb sai Abdul ne kaɗai suke kwantar mishi da hankali saɓanin Bash dayake bashi giya yasha kuma yakawo mishi mata.

*_Bintu_*
Bintu kuwa da Abdul soyayya tayi nisa idan Abdul beji muryan Bintu ba To ranan akwai tashin hankali.
******************

"Bayan wata ɗaya da sati uku, wanda yayi daidai da kawo kayan lefen Bintu Daza'ayi ayau juma'a, gidansu Bintu ne yau ake shirye shiryen karɓar kaya, inda Mommy tayi namijim ƙoƙari wajen ganinta ƙayata abun,
Abinci musamman akayi daga gidan Abincin Mommy, yayinda aka dafa abubuwa masu daÉ—i da ban sha'awa aka zuba a take-away, drinks kuma ba'a magana mommy tayi ordernsu kamar ba gobe.

(Azuciyana nace wannanma ba ranar Auren ba)

An kawo kaya komai yayi daidai inda akayiwa Bintu kaya nagani nafaÉ—a, kowa yasa Albarka anyi mata fatan Alkhairi.

Abdul ne yabijirowa Bintu da maganar pre-wedding pics, Bintu taje sama ta sakko kasa tace bazatayi ba!
Hakan ya fusata Abdul har yayi fishi da ita kota kirashi baya É—aukan kira.

Abun yadami Bintu, tasamu Beebah tayi mata bayanin duk abinda yafaru, Beebah tace Abu me sauƙi basai kitura mishi text kice kin yadda zakiyi ba,
Idan yazo saimu tafi tare inyaso sai ayi dani.

Thats my sisterluv inji Bintu tabawa Beebah hannu suka tafa tace hakan kuwa za'ayi..

_✅ote, comment, and share pls_

✍️🗒️ *_jiddah S Mapi_*
[6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

_Dedicated to my love_

*WATTPAD*
Jiddahpretty

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.