Complete Hausa Novels

A Gidanmu Take Complete Hausa Novel

Reading file: A_Gidanmu_Take_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 16 of 28

Page 31&32

"Ahmad yakasa juyawa, mommy tace Ahmad ta sanadin baƙin cikinka mahaifinka ya mutu, ka kashe 'yar mutane yarinya me hankali, sannan nima yanzu naje an gwadani ance inada hawan jini, kaga saura ni idan ka kasheni, saika kashe Fareedah ko? To baka isaba, kayi kaɗan bazaka kasheni ba! Ahmad idan ka kara taka gidannan Saina tsine maka! Kafice kabar anguwannan ma gaba ɗaya banson ganinka,
Ahmad ya durkusa akasa ya rike kafan mommy yana rokon gafara".

Mommy ta tureshi tashiga gida tana me taƙaicin Ahmad,
Haka Ahmad yatafi gida yana kuka kamar ranshi yafita,
Yana zuwa gida ya buÉ—e frij ya É—auko kwalban giya yafara sha kamar ba gobe.

*HABEEB*
Habeeb tin ranan daya bar gidan Ahmad yashiga bincike kullum yana hanyan gidan marayu yana tambayansu ko akwai wacce aka tsinta? Domin shi jikinshi yana bashi Fateemah bata mutu ba! Ko Mommy batasan yana bincike ba haka ze shirya yace ze tafi makaranta Amma yana fita ze tafi nemawa Ahmad Fateemah, karatunshi yaɓaci baya attending na class, yazama busy wajen nemawa abokinshi matarsa.
Duk da shima yanada nashi damuwan amma yana ganin damuwan Ahmad yafi nashi.

"Yau takama ranar juma'a babbar rana Habeeb ne yayi shiri yacewa mom ze koma makaranta mommy dasu Beebah suka haÉ—a mishi kayanshi, suka rakashi wajen motarshi yatafi"

Habeeb gidan Ahmad yanufa A Kaduna yana zuwa yatarar da Ahmad yana bacci Alamun yashawu, haka ya zauna yayi musu girki ya zuba a flask yashiga toilet yayi wanka yayi alwala, yana sallah Ahmad yatashi daga bacci, yace wow suprise Habeeb agidana yau kai naji daÉ—i, shima yatashi yashiga toilet yayi wanka yayi alwala yazo ya tada sallah, bayan sun idar da sallah ne Habeeb yakalli Ahmad yace "Ahmad kayi min alkawarin bazaka kara shan abu ba! amma nazo naganka a buge meyasa? Ahmad yayi shiru, Habeeb yace tambayarka fa nake?

"Ahmad yace Habeeb bazaka ganemin bane, haka yabashi labarin duk abinda yafaru, Habeeb shiru yayi dan Ahmad yamugun bashi tausayi, yaƙarasa dacewa Habeeb mommy ta tsane ni! Gara nayi ta shan giyar ina neman matan ko zanji sauki a raina.
Aa Ahmad karkace haka shan giya ko neman mata baya ragewa mutum baƙin ciki da damuwa karatun kur'ani shine idan kayi zaka samu sauki aranka."

*BINTU*
Bintu sunyi nisa a soyayyarsu da saurayin data haÉ—u dashi a IG a halin yanzu har maganan aure yafarayi mata, inda tace mishi yashigo gidansu asanshi tukunna. Yace mata insha Allah zai shigo ayi magana.

Beebah idan taga Bintu tana chat da mutumin sai taji ranta yana ɓaci tarasa meyasa
Gashi kuma Bintu kullum suna tare awaya.

Yau suna zaune afalo da mommy, Bintu tacewa Beebah zokiga hotunan my Abdul kinga yanda yayi kyau, Beebah tamatsa kusa da ita tana kallon hoton,

taja tsaki tace "kiga yanda yake dariya kamar É—an tsintuwa yasamu gidan masu kuÉ—i"...

Afirgice Mommy taÉ—ago kanta tana kallon Beebah.....

✍️🗒️ *jiddah S mapi*
[6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*A GIDANMU TAKE!!!*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Story/written by
*Jiddah S Mapi*

*dedicated to my Eeshart❤️*

*WATTPAD*
Jiddahpretty

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.